{{{{{{{ SHIN KO KASAN MUHIMMANCIN SULHU }}}}}}}
Wata rana ANNABI (S.A.W) yana Zaune Shi da Sahabbansa,
Sai Sahabban suka Ga ANNABI (S.A.W) yana Dariya.
Sai Sayyadina Umar (R.A) yace "Ya Rasulullah. Ya Muka Ga Kana dariya kai kadai"?
Sai ANNABI (S.A.W) Yace " Mala'ika Jibrilu Ne yazo Yake Bani Labarin wata shari'ah da Allah zaiyi Ranar alkiyama."
Sai suka ce bamu labarin muji Ya Rasulullah?
Sai ANNABI S.A.W yace "mutun ne Zai Kawo kara Gurin Allah" Yace ya Allah" Wannan dan uwan nawa ya zalunceni Kabi min hakkina?
Sai Allah yace da wanda ake karar akansa, Kaji Abinda dan uwanka yace?
Sai shi wanda ake karar yace ya Allah Lada na ya Kare.
Sai shi wanda ya Kawo karar yace "ya Allah ni ina da zunubi adiba a kara loda Masa.
ANNABI (S.A.W) da yazo nan sai ya sadda kansa Kasa, yana Daga fuskar shi, Sai kwalla ta cika idonsa.
ANNABI yace ranar da kowa yana son Waye zai dauki nauyinsa...
Sai Allah yace Wa wanda ya kawo karar "Daga kanka sama, Meka gani"?
Sai wanda ya Kawo karar Ya hangi Wasu gidaje na lu'u-lu'u Da zinari Na alfarma, Tunda yake duniya Bai Taba Ganin irin su Ba.
Sai yace "ya Allah wannan gidan Na Annabawa Ne? kona Shahidai, kona siddikai".?
Sai Allah yace " bana Annabawa bane bana Shahidai bane, Bana siddikai bane, Na sayarwa ne".
Sai mutumin yace "Ya Allah sama da Kasa Wake da kudin seyan wannan Gidan"?
Sai Allah yace masa " kai kana da kudin sayansu, zalincin Da dan uwanka nan yayi maka Kace ka yafe masa, Shine kudin Wannan gidan"..
Sai mutum yace "ya Allah na yafe masa".
Sai Allah yace "duk da dan uwanka bashi da komai, Ka kama hannunsa Ku Tafi aljannah yaci albarkacin sulhu.
Da ANNABI (S.A.W) Ya fadi haka, sai yace "Kuji tsoron Allah kuyi Sulhu a tsakanin Ku, domin Allah da kansa yanayin Sulhu tsakanin Masu imani Ranar alkiyama.
Yan' uwa Mubar gaba da Junan mu,
Allah ya jikan Mahaifanmu
Allah ya bamu Aljannah Domin Rahamarsa