YA NEMI AURE CIKIN IDDA

*_YA NEMI AURE A CIKIN IDDA?_*

                                *Tambaya:*
Assalamu Alaikum, Malam tambaya ne nakeso a taimaka a amsa mun akan sha'anin aure. 

Malam mace ne tana zaune da mijinta sae ya kasance zaman sun babu dadi kullum a cikin matsaloli iri iri har ya kai ga takoma gidan iyayenta. Iyayenta sun matsa mata se da ta tilasta mijinta ya saketa, saboda suna da wani manufa akan idon ya saketa tsohon saurayinta se ya aureta. Bayan ta matsawa mijinta akan lalle ya saketa se mijin nata ya amince akan zai kawo mata takardan sakin. Mallam a ranan da sukayi zai kawo mata takardan sakin, kawai sae ta samu tsohon saurayinta akan ta naso da zaran tagama idda se ya aureta. Mallam menene hukuncin wannan auren idon tagama idda ya aureta?  
Nataba ji ance duk wanda ya nemi mace tana idda babu aure a tsakanin su har abada, Mallam don Allah ka taimaka mana da Karin bayani.

                                      *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, in mutum ya nemi mace tana idda ya aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara ta tabbatar da hakan, sai dai in an yi auran bayan ta gama idda auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema.                                                  
Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya aure ta cikin idda, ba in ya neme ta ba.                                                         
Allah ne mafi sani.

09/08/1437
16/05/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)