TANA AZUMI SAI MIJIN TA YA SUMBACE TA

*_TANA AZUMI SAI MIJINTA YA SUMBACETA?_*
  

                             *Tambaya*
Malam macece tayi kitso alhalin tana azumi sai mijinta yaga kitson ya basa sha'awa saiya sumbacesa ita kuma take sha'awa tazo mata harta jika pant dinta

                                     *Amsa*
To yar uwa da farko dai anyi wasa da azumi kwarai da gaske kuma ba daidai bane kina azumi ki bari mijinki ya sumbaceki ta yadda har zaki fitar da wani abu dazai bata miki azumi' wannan akwai ganganci a ciki.

Amma shi azumin nafila dama mai shi yanada yan'cin ya karyashi koya cigaba Annabi S.A.W ya fada cikin hadisi sahihi mai azumin nafila shine sarkin kansa idan yaga dama ya karya manzon Allah s.a.w. ya bada wannan damar.

Malamai suna cewa fitar maziyyi idan har maziyyine ya fita karamar sha'awa kenan zance mafi inganci baya karya azumi amma idan maniyyi ne ya fita to azumi ya karye shikenan idan na nafila ne bakida lada idan kuma farilla ne akwai kaffara akansu bisa kaulin malamai amma wasu malaman sukace sai anyi jama'i kaffara take wajabta idan nafilane shikenan idan kuma na farillah ne saiki rama guda daya wannan shine zance mafi inganci.

Allah shine mafi sani.

18/04/2017

Amsawa:- Dr. Abdallah Gadon Kaya
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)