WANI ABU YA FITO MIN BAYAN ƊAUKEWAR JININ HAILA, YAYA MATSAYIN IBADA TA?

*_WANI ABU YA FITO MUN BAYAN DAUKEWAN JININ HAILA, YA MATSAYIN IBADANA?_*

                             *Tambaya:*
Assalamu Alaikum warahmatullah Malam Allah ya taimaka nayi wankan daukewar haila bayan naga alamar discharge babu jini sai dai karni karni kadan bayan awanni na kuma dubawa sai naga wani discharge din da yafi na farkon haske sai na kuma sake wankan to Malam yaya ibaduna san nan na taba ji ance shi discharge din da yake fita bayan Al'ada yana kanshin hudar dabino wanda yake ni ban san kanshin ba abunda yasa nayi wankan shine sabi da azumi kar na wayi gari ba tare da na dauki azumi ba Malam sai na sake wani wankan da kuma azumin da nake yi bayan wankan Allah ya saka da Alkhairi ya taimaka na gode.

                                     *Amsa:*
To, wannan nau'in ruwan da kika ga yana fito miki shi ake cema AI-SUFRAH ko AL-KUDRAH, shi ne yake zo ma mace kamar ruwan Siminti (Cement) ko ruwan ciwo wani lokaci ma gauraye da baki-baki. To, irin wannan ruwan yana da hukunci dayan biyu ne:

1. Idan kin gashi ne a lokacin da kike Haila ko a karshen Haila amma hade da Hailar to, hukuncin shi hukuncin jinin Haila ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Nana Aisha (RA).

2. Idan kin gan shi ne a cikin tsarki lokacin da baki Haila to, hukuncinsa, hukuncin tsarki ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Ummu Adiyyah (RA),  zakicigaba da Sallah, Azumi da sauran aiyukan na Ibada, duk abinda aka hana mai Haila bai shafe ki ba, sai dai duk lokacin da zaki yi Sallah sai kin yi tsarki kin sake Alwala har zuwa lokacin da wannan ruwan ya daina zuwa. Allah ya bamu ikon ganewa da gyarawa.

08/06/2017

Amsawa:- Mal. Ibrahim Jushi, Zamfara.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)