*👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
*Bissimillahirrahmanirrahim*
Da sunan Allah Zan fara Da sunan shi zan gama insha Allahu.
Kada wani ko wata ya juyamin labarina ta kowacce siga in hakan tafaru nabar mutum da rabbil alamin.
Inkinji wani abu dayayi dede da rayuwarki arashi ne dan labarina ƙirƙirarrene.
*1*
Salma ƴa ce ga malam hadi me walda da faci,suna zaune a garin kaduna cikin wata unguwa da ake kira hayin rigasa.
Malam hadi mutum ne me taƙawa da tsoron Allah duk da talaucinshi kullum cikin yiwa Allah godiya yake,dan wata rana ko,abinda zasu ci gagararsu yake.
Matarshi ɗaya da ƴaƴa biyu,Rakiya shine sunan matar tashi,wacce ƴaƴan ke kira da Umma,se Sahabi wanda shine babban ɗansa,sannan Salma,wacce tazama ƴar auta sabida daga ita Allah be ƙara basu haihuwa ba.
Salma ƴar kimanin shekara Goma sha shida,ta kammala makarantar secondry da ƙyar sabida iyayanta ba masu ƙarfi bane,amman suna da zuciyar neman nakansu,tun tasowar Salma yarinyace da ta ɗauki ɗabi'ar ƙarya tasa a ranta,tana da rawar kai ga tsiwa da rashin kunya,bata da buri daya wuce ace gata a jami'a tana karatu uwa uba kuma ace ta zama ƳAR BAUTAR ƘASA,wannan shine fata da burin Salma
Da kyar tasamu tayi registration ɗin jam,kuma Allah ya taimaketa taci,tasamu Admission a Zaria,wato A,B,U,in kuka ga yadda kan Salma ke rawa zaku ɗauka har tashiga ma ta gama.
Duk wata kadara da iyayanta suka mallaka ita suka siyar,suka biya mata kuɗin registration,murna gurin Salma baa magana.
Tun shigar Salma jamia idonta ta ƙara buɗewa ta fahimci ba ƙaramin cutarwa bace data kasance ƴar talakawa,sam kalarta ba kalar talauci bace,sabida haɗuwa da tayi da ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi.
Salma duk wani abu da ake kira kyan sura ba abinda Allah be bata ba,tana da kyau na bugawa a jarida sede wani ikon Allah duk da wannan kyau na,salma sam bata da farin jinin samari,dan ko saurayi bata dashi,wanda ita anata ganin talaucin data taso acikine yasa samarin basa kulata,hakanne yaƙara haddasa tsanar talauci a zuciyar Salma duk wani abu daze daidaitata da ƴaƴan masu kuɗi shi takeso kuma takeyi,matsalarta ɗaya bata da irin suturarsu,wannan shi ke kawo mata cikas a rayuwar datasa kanta aciki.
Abu dayakai abu Salma har sata tafarayi,kana sake da kayanka tuni zata gyara musu zama,in shaddace se takai a rina mata taci gaba da sawa ba me cewa tashice,inkuma atamfa ko materials ne se takai acanja mata ɗinki,yadda duk ƙwaƙwar mutum yasha Ƙarya yace tashi ce.
Satar takalmi da jaka kuwa ta jima dayin,degree a wannan fannin sede idan bata ganiba,shigar ta ce tasa ɗalibai ƴan uwanta ke ɗauka ƴar masu kuɗi ce.
Muje zuwa.
Surbajon kuce.