Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*See yourself as a light and you will shine,there is no one without a past,Don't be a prisoner to your past,move on, Allah is your witness*
*2*
Haka rayuwar salma taci gaba da tafiya,acikin jamia,har zuwa lokacin data kammala aka turasu service.
Salma tafi kowa ƙosawa ayi posting ɗinsu,har addua take sunanta yafito a verge A, Allah kuma yataimaketa sunan nata yafito inda aka turata garin keffi,cikin jahar nasarawa domin gudanar da bautar ƙasarta acan.
Salma sam bataso aturata keffi ba,Abuja taso akaita inda idonta ze ƙara buɗewa ,sosai.
Zaune suke ita da wata Aminiyarta,me suna Firdausi,wacce aka fi sani da fee-fee,makwabciyarsu salma ce,yarinya me natsuwa da kamun kai,sam halinsu yasha bambam da salma Allah ne de kawai ya haɗa jininsu suke ƙawance tun daga yarinta,makarantarsu ɗaya,ko hutu akayi tare suke tafiya,sede ɓangaran da kowa ke karanta da bam,ita firdausi,business admin take karanta,yayin da salma take karantar medical doctor.
Hira suke game da tafiyarsu bautar ƙasa,inda dukansu gari ɗaya aka turasu cikin hukuncin Allah,wato keffin ɗan yamusa.
"mtssuu,nide fee-fee gaskiya keffin nan bataminba,wlh,nibanma taɓa jin,sunan garinba inbanda da aka turamu can"salma ta faɗi cikin yanayin damuwa.
Dariya feefee tayi sannan tace.
"In banda abinki,Salma meye abun damuwa aciki mude ba iyakarmu in mundawo daga inda muke service ɗin mu koma kamp ba,nide yamin wlh dan inason dama indunga zuwa garin da ban saniba"feefee ta ƙarasa zancan cikin dariya.
Tsaki salma ta ƙarayi,sannan tace.
"Ni wlh Abuja naso aturani,idonka zefi buɗewa".
"To inbanda abinki,ay tsakanin keffin da Abuja ba nisa,ɗari biyar ne kuɗin mota,sannan garin keffin fa,ance garin ƴan boko ne sosai,kuma babban garine,dan yawancin maaikatan garin ma a Abuja suke ayki,akwai manyan masu kuɗi a garin sosai,dan har ɗan takarar gwamna garesu agarin,sunan shi wadada,kinga ko in ace ƙaramin garine bazaa sami hakanba".
Murmushi salma tayi tace.
"feefee,duk wannan bayanin a ina kika sameshi,naga kema kince bakisan garinba?"
"hhhh kede akwai sokuwa, kinmanta yaya nasiru acan yayi service ɗinshi?ay duk shine yabani labari,kinsan ko ba halinshi bane ƙarya bare ince ita yamin"
Farin ciki ne ya mamaye zuciyar salma sabida ta gamsu da bayanan feefee,dan tasan yayan feefee nasiru ba maƙaryaci bane.
Da wannan hirar da sukayi da feefee ne salma ta samu ƙwarin guiwar,tunkarar garin na keffi.
Shiri iyayanta suka mata sosai,gamida dayi mata nasihar taji tsoron Allah,takama mutuncin kanta,salma harda kuka na munafunci kamar ta yarda da shawarar iyayan nata.
Haka,suka kamo hanyar keffi ita da sauran ɗaliban da aka turasu garin.
Sanda suka shigo garin Abuja salma ji tayi kamar tace a sauketa a garin,dan haɗuwar garin,haka tanaji tana gani aka wuce garin batare da an tsaya ba.
Da la'asar suka isa, NYSC camp dake garin keffi.
Ranar lahadi ne dan haka masauki aka basu kamin gobe monday su gana da mahukuntansu.
Da kyar salma ta yarda ta kwanta,da dare yayi dan ita burinta,tafita ta zaga garin taga yadda yake.
Feefee ce ta hanata fita,amman ranta be soba,haka ta kwanta tana mita dan ba haka tasoba.
Washe gari da safe duk suka hallara a inda zaa faɗawa kowa inda zeje yayi aykinsa.
Babban Asibitin gomnati na garin aka tura Salma,me suna.F,M,C.
Tun daga bakin gate ɗin Asibitin salma ta fahimci asibitin babba ne duba da yawan jamaar dataga suna shige da fice aciki.
Haka taje tayi clearing komai aka nuna mata ɓangaran dazata dunga wakilta,inda babban likitan gurin bayanan yana ƙasar jamus,inda yaje wata seminer da aka haɗa ta manyan likitoci.
Muje zuwa.