Ƴar Bautar Ƙasa 11

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*11*


Gaba ɗaya yagama rikicewa yarasa abinda ke damunshi.

Waige waige yashiga yi yana neman wayarshi amman dayake a ruɗe yake sam yagaza,ganinta,se zuwa can Allah yakai idonshi kanta.

Da,sauri ya ɗauka ya dubo wata number yakira ba jimawa naji yace.

"Hello barrister,kana gidane?"

Dagacan ɓangaren yace.

"eh ina gida,amman kasan ayni ba gwauro bane kamarka,ina fatan de bacewa zakayi zaka zoba?"

Se alokacin doctor yafahimci ashe darene ba safiya ba.

"Da safe in Allah yakaimu inaso mu haɗu"doctor ya faɗi cikin damuwa.

"ok baka da damuwa Allah yakaimu safiyar"

Daga haka kowa ya ajiye wayar.

Doctor safa da marwa yashiga yi,zuface kawai take keto masa.

"Me ya haɗa salma da hodar iblis,adaren daya ganta?meya hanata yin magana a kotu domin ayi bincike?"wani tambayoyin su doctor ya kwana yiwa kansa har garin Allah ya waye.

Da safe da wuri ya shirya ya wuce office ɗin Barrister,be zoba seda ya jirashi na tsawon awa biyu.

Koda barrister yaga yanayin doctor yasan yana cikin damuwa sosai,danga idonshi ya nuna beyi bacci bama jiya.

"bokan turai me yake faruwane?"barrister ya tambaya.

"Barrister komai ma yafaru,wallahi narasa natsuwa tun jiya dana kalli news da aka nuna gidan yarin kuje"

Wata dariya ce ta ƙwacewa barrister inda yace

"kaiko in banda shirme irinnaka ina ruwanka da gidan yarin?"

"Bazaka gane bane barrister,shekaru biyu da suka wuce lokacin ina ayki a keffi akwai wata ƴar bautar ƙasa da aka turo office ɗina daga A,B,U zaria,to yarinya irin wainda suka fiye son kuɗi ɗinnanne,dan sometimes inna ajiye kuɗi tana ɗauka,so biyu ina ganinta da wani Alhaji wanda ni zuciyata bata amince dashiba,ƙarshen ganina da ita,wani darene munje conference a Abuja,naganta tare da mutumin zasu shiga cikin,hilton transcop hotel,to abun mamaki,bayan sati ɗaya dayin hakan sega report daga Hukumar NYSC zuwa office ɗina wai tayi hatsari ta ƙone maana de ta mutu,tsawon wannan lokacin da aka ɗauka ina mafarki da ita tana miƙomin hannu da niyyar incirota daga wani kogi data faɗa,toni tunanina se yabani,maybe ana mata hukuncine game da satar datasha yimin dan haka sekawai nayi sadaka sannan nace na yafe mata,ti kwatsam jiya segashi naganta acikin gidan yarin wai shekaru biyu kenan da aka kamata da hodar iblis,kuma babu irin azabar da baa gana mataba amman taƙi yin magana,kuma koda aka nunota jiyan still kukan takeyi,barrister kaji abinda ya ɗaga hankalina"cewar doctor fuskarshi na nuna tsananin damuwar dayake ciki.

doguwar ajiyar zuciya Barrister ya yi,sannan yace.

"Gaskiya abokina wannan zancan adubane,zeyi wuya idan ba sato jakar tayiba tunda tanayin satar"

"wlh barrister nima tunani na kenan,wata ƙila gurin shegiyar satar tane taje ta satowa kanta masifa"

Shuru barrister yayi kana daga bisani yace.

"ka kwantar da hankalinka,insha Allahu se angano gaskiya,karkadamu yanzu kataso muje gidan yarin mu nemi ganinta,wataƙila mu tayimana bayani"

"To Allah yasa,amman mu biya ta office nayi signing semu wuce kuje ɗin"

Daga haka Asibitin da doctor yake ayki suka je yayi signing sannan suka fice zuwa gidan yarin kuje.

Koda suka isa basu sha wata wahalaba gurin samun izinin ganinta,sabida barrister babban lauyane kuma fitacce.

Gurin da aka tanada domin ganawa da masu laifin aka kaisu,sannan akaje aka taho da Salma ƙafa da hannunta ɗaure cikin sarƙa,koda akace tazo tanada baƙi ba ƙaramin mamaki tayiba dan tunda aka kawota kare bezo yace yan nemanta ba.

Koda aka kawota gaban su doctor,agigice yake kallonta,sabida gabaɗaya,duk wannan kyan da kyan surar duk babu,takoma kamar tsohuwa sabida wahala

Sanda salma ta ɗago idonta taga doctor,wani kukane ya kubce mata,zubewa tayi agabanshi tana faɗin.

"Don Allah kayafemin,kagafartamin,wlh nasan hakkinkune yakamani shiyasa aka kawoni nan,kagafartamin,don Allah"ta ƙaras maganar cikin matsanancin kuka,ta ruƙo ƙafarshi.

Runtse ido doctor yayi yanjin kukan salma na taɓa zuciyar shi.

Hannuns yasa ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujera,sannan,yasa hand carchiep yana share mata hawaye,riƙe hannun salma tayi wasu hawayen nabin fuskarta tace.

"shekaru biyu kenan ina irin wannan kukan,babu wanda,yataɓa gogemin hawayen sekai,Allah yasa kayafemin ne?"

Kai doctor ya ɗaga mata.

Shiko barrister,abun nasu tv yazamar masa,danshi bema taɓa ganin masoya irin suba.

Gajiya yayi,da kallon nasu ya dakatar dasu,suka fara abinda ya kawosu.

Muje zuwa

Surbajo for life.


1 Comments

  1. A spa is a simple, calming, parlor-like destination where you enter for a day of rejuvenation. If you want to remove all the stresses, tensions and woes of your daily life, a spa is the place for you to be. A spa offers you a form of therapy, where you get to choose from a varied number of services, pleasing to your body’s wants and needs. These services laid before you seek to improve your physical and mental health as well as your beauty through personal care treatments like hair and body massages, facials and many more. Every spa treatment is a form of water treatment which involves using hot baths, saunas, steam rooms and even whirlpools. These treatments soothe your skin, and simmers you down to relax and enjoy the time at the moment. Although, in today’s advanced world, there have come up different types of spas such as day spas, destination spas, hotel/resort spas, they all narrow down to one main goal : Improving your wellness and helping you relax.
    Hi am Isha here from mumbai , 23 year old staying bangalore we provide body to body massage services in bangalore
    massage bangalore
    massage in bangalore
    body massage bangalore
    body massage in bangalore
    body to body massage in bangalore
    body to body massage bangalore
    massage parlour bangalore
    massage parlour in bangalore
    body massage parlour in bangalore
    body massage centers in bangalore
    body to body massage bangalore
    body to body massage in bangalore
    erotic body massage bangalore
    female body massage bangalore
    full body massage bangalore
    female massage in bangalore
    girls body massage in bangalore
    b to b massage in bangalore
    b to b massage bangalore

    ReplyDelete
Post a Comment