Zahra muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Shafin nakine ke kaɗai,kawata takaina,Allah yaƙara ɗaukaki duniya da lahira yakareki daga sharrin duk wani me sharri,Ameen,MRS FAWWAZ Allah yabarmu tare#ana tare*
*18*
Koda asuba tayi doctor yafarka,yaga wayarshi yashe akan fulo dariya ce ta ƙwace masa,wato suna waya da salma ne bacci ya ɗaukeshi,sede wani abu daya bashi mamaki shine,rabonshi dayayi bacci me daɗi irin haka tun kamin salma ta ɓace,dan yaji daɗin baccin sosai.
Alwala yayi yatafi masallaci,bayan an idar da sallah,kai tsaye ɓangaren mahaifinshi yashiga sabida beganshi a masallacinba.
A falo ya tsaya yanata sallama amman shuru bawanda ya amsa,dan haka ya juya ze fita,hajiya kaltum yagani tsaye abakin ƙofar fitar tana mishi murmushi.
Haɗe fuska najeeb yayi sabida ya tsaneta ba kaɗanba,raɓawa yayi ze fice,seji yayi ta rungumoshi,tana mishi kukan kirsa.
"Haba najeeb meyasa baka da tausayine,shaawarka kullum ƙaruwa takeyi araina,don Allah kadaure ka kwanta dani ko so ɗayane"tana magana tana ƙoƙarin shafo ƙasan wandon shi.
Agigice najeeb yatureta daga jikinshi,rai aɓace yace.
"kaltum kifita harkata ni ba mazinaci bane,kuma ko da ni mazinacine bazan haɗa shimfiɗa da mahaifina ba,wawiya shasha kawai"
"Najeeb ni kake yiwa wannan ɗibar albarkar"
"anmiki ɗin uwatace ke dabazan miki ba,dabba kawai,wallahi nan gaba ma sena zagi uwarki inde baki fita harkata ba"
"na nawa kuma ay sede kar akuma yanzunma kazagi uwar tawa ay,sede kasani,wallahi matuƙar baka biyamin buƙataba,sekayi danasanin zuwanka duniya,kuma wallahi kaida aure sede kaga anayi,inko kayi,matar hotoce agurinka,dan babu wacce ta isa ka shigeta seni"
"Tur dake wallahi,sede kisani,ay bakece Allah ba,tunda ko hakane muzuba nida ke shegene ze fasa"yana gama faɗa mata haka ya hankaɗeta,ya fice daga falon ita kuma ta faɗi ƙasa.
A fusace yaje gurin me gadi yana tambayarshi ko abbanshi yafitane.
"Ranka ya daɗe cikin dare direba yakaishi airport wai yatafi wata ƙasa amman bansan sunanta ba"cewar me gadin.
da sauri yanufi ɓangarenshi,wanka yayi ya shirya,yaɗauki key ɗin motar shi ya fice daga gidan ya kama hanyar Abuja yana me danasanin zuwan shi.
Anata ɓangaren salma itama tashi tayi cike da nishaɗin wayar da sukayi da najeeb in ta tuno ranta se ya mata sanyi.
koda taji shuru be kirata ba ita seta gwada kiranshi.
Adaidai lokacin shi kuma najeeb ya iso kawo kaduna,jin wayarshi na ƙarane yasa yakalli inda wayar take.
*Up to now*shine sunan daya bayyana akan screen din wayar tashi.
Murmushi yayi,danshi kanshi sunan ya bashi dariya.
Katse wayar yayi,yakirata inda ya tsinkayo muryarta tana faɗin.
"doctor ina kwana,ya bacci"ta ƙarasa maganar cikin sigar zolaya.
Wani sanyi yaji yana ratsashi yayinda ya mance da duk wani ɓacin rai dake damunshi,kasa yayi da muryarshi kamar mejin bacci yace.
"Salmah kin fara rainani ko?"
Numfashin salma seda ya ɗauke yadawo,sabida yanayin da ta shiga sanda taji sunanta a bakin doctor wanda bata taɓa jin yakiraba,da kyar ta saisaita natsuwarta tace.
"nidin banza,har na isa na raina ka"
Maganar tamasa daɗi,dan haka gefen titi yasamu yayi parking sannan yace.
"to faɗamin,ya akayi kikasan nayi bacci?"
"numfashinka naji yasauya alamar kayi bacci kuma inata magana naji shuru,shine yasa nagane kayi baccine"ta faɗi cikin muryarta me daɗin saurare.
murmushi yayi sannan yace.
"kice laɓe kikemin kenan awayar,to asheko kinaso na laɓaɓaki"
Dariya salma tashigayi harda hawaye.
Doctor shuru yayi yana jin dariyar tata,dan yasan ba iya maganarshi bace tasata dariyar.
Zuwa can de tace.
"da kana karanta novels se ince acan kajiyo wannan kalmar,dan wlh da lokacin ina cikin wani group na novels na surbajo,to admin ɗin batason mutum yana online amman bazeyi magana agroup ba shine tasa dokar duk wand takama yana laɓe seta laɓaɓashi waje,"ta ƙarasa maganar tana dariya.
Murmushi yayi,dan ya fahimci salma har yanzu da akwai yarinta atattare da ita.
"To kika sani ko nima surbajonce ta koyamin?"
dariya salma tasake yi sannan tace.
"tab ayko bade surbajonmu ba,kaide kasan inda ka koyo kayanka"tayi maganar cikin shagwaɓa.
kawar da hirar yayi da cewa.
"to ƙanwar surbajo me kikaci yanzu da safennaɓ?"
"lah banci abinciba,gashi nande ina ƙarasa haɗawa"
"me kike haɗawa?"
"wainar shinkafane,da miyar taushe"
"zaki sammin naci nima?"
"hhh doctor kenan kaida kake Abuja taya zakaci wainar dake kaduna"
"jiya ba Abuja nawuce ba,na shiga kanone nagaida Abbana,yanzu haka ina kawo kaduna,sede in rowa zakimin?"
"babu rowa tsakanina dakai har abada,komai kakeso kawai kafaɗe shi kanka tsaye,ni kuma zanbaka"
"to ki kawomun wainar junction ɗin bakin ruwa inna ƙaraso seki bani naci,ki tafi da kwanunkan"
"haba doctor yazaayi kaci abinci a titi,kabiyo ta gida mana kaci"
"inada uzurine salmah,ki kawomin inda nace"
"Amman de doctor..."
Katseta yayi dacewa.
"Salmah"cikin wata siga data tilasta mata yin shuru,jin tayi shurune yasa yace.
"zaki kawomun ɗin?"
"Eh zan kawo maka"
"to kiyi sauri"
daga haka sukayi sallama ya ajiye wayar,jinshi yake kamar wani sabon ango tada motar yayi yaci gaba da tafiya.
Be jimaba ya isa bakin ruwan,parking yayi daidai tahir plaza,yana jiranta.
Ita ko suna gama wayar gurin ummanta taje ta sanar da ita komai,dan haka umman fitowa tayi ta amshi suyar wainar,ita kuma salma,ta ɗebo kuloli tazuba wainar da miyar datasha naman kan rago da manshanu,a basket tazuba harda plate da cokali,sannan taje ta sauya kaya taɗan shafa hoda ta ɗauki,abincin ta fice,drope ɗin napep ta ɗauka,dan haka bata jimaba ta iso bakin ruwan.
kiranshi tayi awaya ya faɗamata inda yayi parking,dan haka ƙarasawa tayi gurin,tana zuwa ko ta hango motarshi a gurin,ƙarasawa tayi.
Tunda ta nufoshi yake binta da kallo,ba abinda yafi ɗaukar hankalinshi se yanayin tafiyarta,ga kayan data saka fited gown ce wacce tafitar da shape ɗinta da kyau,se siririn mayafi data rufa akanta zuwa kafaɗarta,tayi masa kyau sosai,sede sanda idonshi ya sauka akan wasu maza da suka zuba mata ido se yaji duk ranshi ya ɓaci.
kamin ta iso,ya buɗe motar yafito,yakoma gidan baya,dan haka tana isowa itama ƙofar bayan ya buɗe mata.
shiga tayi da sallamarta tazauna,sannan ta ajiye kayan abincin aƙasan kujerun sabida motar jeep ce to akwai space.
"wayace ki sako wannan mayafin?"
"wlh sauri nakeyine shiyasa nasakosho kuma napep na hawo tundaga gida zuwa nan ɗin"salma ta faɗi kamar me shirin yin kuka.
"zubamin abincin,Allah ma de yasa yayi daɗi kar inci,in haɗu da bacteria"
murmushi salma tayi ta zuba mishi abincin ta miƙa masa plate ɗin gabanshi,amman se yaƙi ɗauka,binshi tayi da ido,tace.
"doctor lafiya kuwa?"
yamutsa fuska yayi sannan yace.
"Hannuna ba awanke yakeba,kuma ni ban iycin waina da cokali ba,so ayki yasameki dan haka kibani da hannunki"
murmushi salma tayi sannan tace
"to ayga ruwa seka wanke hannun"
"nufinki infitar da hannuna waje ina wankewa,ayko bazan iyaba,in bazaki bani bane to na haƙura da abincin"
kunya duk ta gama kam salma haka ta ɗauke plate ɗin ta matsa kusa dashi,tafara bashi abincin abaki,bako kunya yadunga wangale baki yana amsa,har tagama bashi,koda yazo cin naman ba ƙaramin daru sukaib,dan miƙa mushi cokalin tayi yaci dashi,sam yaƙi ams haka tadunga bashi har yagama ci,zat jiye hannunta,yayi sauri yariƙe,wai dole se ya tsotse hannun sabida,ya ƙarasa ladanshi🤣tanaji tana gani ya suɗe hannun tas,sannan yasha ruwa,ya goge bakinshi da tissue.
me makon taga ya sallameta setaga ya jawo kayan abincin yazuba wani sannan yasa hannun nashi dayace ba wankakke bane ya ɗebo abincin yanufo bakinta dashi,ƙuri tayi da ido tana kallon ikon Allah
"zaki amsane ko sena ɗura miki?"
da sauri ta buɗe baki yasakamata wainar,haka yadunga bata har seda tace ta ƙoshi ya ƙyaleta.
wanke hannunshi yayi awajen dayace baze wankeba,ita kuma ta haɗa kwanukan acikin basket ɗin,duk atakure take ta ƙosa ta fice daga motar.
"kinsn ko kabeer yanzu in yaganki baze ganekiba dan haka bari inmana hoto tare sabida innaje na nunamasa yadda prisoner ɗinshi ta kile" dariya salma tayi da sauri ta yunƙura zata sauka a motar,jawota yayo da ƙarfi ta faɗo jikinshi,ɗago da kanta tayi tana kallonshi,shima ita yake kallo,ahaka yaɗaukesu hoton,ganin hasken camera ne yasa salma ɓoye fuskarta ƙirjinshi,shima sake ɗaukarsu yayi ahaka sannan yasaketa.
turo baki salma tayi gaba sannan ta ɗauki kwanunkanta seda taji ƙafarta aƙasa sannan ta waiga tace.
"wannn ay cin zaline,mutum yagama maka bin kirki kuma kaci zalinshi"tana kaiwa ƙarshe tayi saurin ficewa a motar,
Dariya abun yaba doctor sosai.
buɗe motar yayi shima yafice,yaje inda take,dariya take masa shima dariyar yayi sannn ya ɗaukar mata drop din napep,seda tashiga tazauna,sannan yasa hannu yaja hancinta yace.
"to mara kunya ki gaidamin da ummana d Abbana,da sahabi"yana gam magana ya ajiye mata kuɗi akan cinya ya juya ya nufu motar shi Ya tada ita ya kama hanya,yana jinshi cikin matsanancin farin ciki.
muje zuwa
surbajo for life