Ƴar Bautar Ƙasa 19

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*Don Allah masuyin editing na yar bautar kasa kudena kubarmin shi ayadda nayi editing din kayana,pls🙏*

*19*

Ya isa Abuja lafiya itama ta isa gida lafiya.

Asibiti yafara zuwa ya sallami marasa lafiya sannan yanufi gidanshi.

Yana isa gida ba jimawa kabeer yazo gidan,da murna suka tarbi juna.

Zama sukai suna hirar rayuwar duniya,danshi kabeer bemasan doctor yayi tafiya har ya kwana ba.

Kamar wanda aka tsikara doctor yaje ya ɗauko wayarshi ya nuno hotunansu ya miƙawa kabeer yace.

"ka gane ta jikin hoton nan kuwa?"

Kabeer ko mamakine danƙare a fuskarshi dan besan doctor yanada budurwar da sukayi shaƙuwa kamar haka ba,

Murmushi kabeer yayi sannan yace.

"haba abokina no wonder kace ba son salma kakeyiba,ashe already anjima da cinye zuciyar taka,kana da gaskiya me mace kamar wannan ba abinda zeyi da salma,gaskiya tayi ba ƙarya,wannan tashiga taroce,kamin lokacin auren tun yanzu naɗauki nauyin events guda uku dazaayi lokacin bikin"

Dariya doctor yakeyi sosai sannan yace.

"daɗina dakai wani sain kai gabi ne,dama seda na faɗamata bazaka gane taba inka ganta,to wannan ta jikin hoton salma ce"

Ido kabeer yaware sosai gamida zooming din hoton,da idonta yagane salma ce,wani ihu kabeer ya saki yana dariya yafara nuna najeeb da hannu yace.

"kana shaaninka mutumina,kagama pretending ɗin kadawo kan hanya kenan,yanzu ka amince kana sonta,tunda gashi harda su runguma ana selfie"kabeer ya faɗi yana kyalkyala dariya.

"ni kaifi ɗayane,bana sauya maganata,sabida gaskiya itace nagartar namiji,wlh kabeer bana son salma bana sonta,kuma bazan taɓa sonta ba,ni tausayinta kawai nakeji,taya zan so salma mahaukaci ne ni?wlh bana sonta,ko hoto dakaga na ɗaukemu,zata gudune nikuma na kamota shine tafaɗo jikina,kuma badan komai naɗaukaba sedan nazo na nuna maka"najeeb yayi maganar ranshi aɓace.

Kabeer dena dariyar yayi ya tsaya yana nazari akan aminin nashi,tabbss aminin nasa yanada matsala,wato ya fahimci sam najeeb bemasan meye soba bare yasan yanayinsa,tabbas yasan najeeb aduniya babu wanda ze gwada masa son salma,to amman matsalar yaƙi yarda da so ɗinma bare ya amince sonta yake,tabbas amininsa yana cikin tsaka me wuya matuƙar Allah be buɗe masa idonsa ya fahimci son salma yakeyiba,sabida duk ranar daya rasata ze shiga tashin hankali,wanda baze masa kyaiba.

ɗagowa kabeer yayi asanyaye yace.

"calm down abokina se yanzu nagano matsalarka,zantaya da addua kuma zanci gaba da tunasar dakai abinda baka amince dashiba,insha Allahu komai zezo da sauƙi"

Dariya najeeb yayi sannan yace.

"kanka akeji"

Daga haka hira suka shigayi.


Tun daga wannan lokacin,azahirin gaskiya duk wanda yaga salma da najeeb yasan masoyane,amman agurinsu su kuma ba haka bane.

Salma nason najeeb kamar ranta,shikuma anashi ɓangaren,tausayinta yakeyi,wanda ita bata gane hakanba ɗauka takeyi sonta yakeyi,shiyasa ko saurayi tayi bata kulashi.

Duk ƙarshen sati najeeb,na hanyar kaduna zuwa gurin salma,har su kansu iyayen salma sun ɗauka najeeb sonta yakeyi.


Se su kwana su yini suna waya da juna ko gajiya basayi,koda feefee ta tambayi salma tsakaninsu,kai tsaye salma ta shaida mata soyayya sukeyi.

ganin irin sintirin da najeeb yakeyine duk sati daga Abuja zuwa kadunane yasa mahaifin salma tuntuɓarta yaji tsakaninsu,dan haka yasa aka kiramasa ita.

"Salamatu,meke tsakaninki da najeebullah ne?"cewar mahaifinta .

Ƙasa salma tayi da kanta alamun jin kunya da ƙyar tace.

"Baba sona yakeyi"

Murmushi yayi sannan yace.

"kekuma bakya sonsa ko?"

cike da kunya tace.

"nima ina sonshi"

"to Alhamdulillahi,nayi farinciki,to amman salma kinsan baze yiwu muzuba muku ido ba dan haka inyazo wannan satin nida kaina zanmasa magana yaturo magabatansa atsaida magana,hirar ta isa haka atiti kuje gidanku ku cigaba".

daga haka ya Sallameta.

Ranar salma har zuba ruwa tayi a ƙasa tasha dan murna,koda suna waya da najeeb seda ya fuskanci tana cike da farinciki ,danhaka yace mata.

"hala tasamune kike ta farinciki haka?"

dariya tayi sannan tace.

"kaide bari wlh ay dawa tayi nama ne"

Dariya yayi sannan yace

"Ah tunda hakane,shafamin nawa tun yanzu,kar kamin inzo yaƙare"

dariya salma tayi tace.

"Sha kuruminka,babu me taɓawa se kazo,kaine ma zaka fara taɓawa"

"Har kinsa naƙosa satin yazo nazo"

Haka de sukai ta hirar su irin ta masoya a zahiri.


Wannan satin shi da kabeer suka zo.

murna gurin salma baa magana,nan tashiga ɗawainiya dasu,har tausayi taba kabeer,sabida ya fuskanci ba ƙaramin so takewa najeeb ba.

seda sukayi sallah azahar sannan mahaifin salma ya buƙaci ganawa dasu,

Zaune suke atsakar gidan su salma suda mahaifin nata inda mahaifin salma yafara da cew.

"Najeebullahi kimanin shekara ɗaya kenan kana tare da salma,batare da ka turo magabatanka an tsaida maganaba,shiyasa nacewa salma ta turomin kai dan nayi maka magana,soyayyar awaje taisa haka,gwanda amuku aure inyaso sekuyi agidan auranku,dan haka katuro magabatanka,atsaida magana,dama kiran danamaka kenan"

Tunda Abban yafara magana zufa take ketowa kabeer,yayinda shiko gogan kanshine yaɗau charge,dan haka beyi ƙasa aguiwaba yace.

"baba ni duk wannan bayanin naka banganeshiba,ita salmar ce tace soyayyace tsakanina da ita?"

murmushi baban yayi sannan yace.

"ita tashaidamin kuma dama idanuwana sunjima da gani,danhaka katuro magabatanka kawai ayi magana"


Ran najeeb gaba ɗaya yagama ɓaci inbanda salma ta ɗaukeshi mutumin banza ubanme zeyi da ita.

"baba nifa bason salma nakeyiba,taya zatace sonta nakeyi,kwatankwacin wannan maganar babu ita atsakaninmu"najeeb yafaɗi ranshi aɓace.


"baka sonta meyasa kake,zuwa gurinta duk sati,kuma kake ɗawainiya damu da ita gaba ɗaya,kaga najeebullahi karka maidani sakarai wanda besan abunda yakeyiba,yazaka ɗauki tsawon lokaci kana huremata kunne taki sauraran kowa alhalin kaibada aure kake sontaba,sannan yanzu kazo kana faɗamin ba sonta kake yiba"

Afusace najeeb yace.

"ya isa haka baba kar kayi yunƙurin cimin mutunci akan abinda bedace da aci mutuncina dominsa ba,ni mahaukacin inane zanso salma har inyi shaawar ajiyeta amatsayin mata agareni uwar ƴaƴana,?baba kode kamantane,?salma shekarunta biyu agidan yari adalilin sata,bayan wacce tajima tanayimin kamin Allah yatoni asirinta,bafa iya sata salma ta iyaba salma taƙware a harka da maza kalakala,ni ganau ne ba jiyau ba,kuma shikenan dan tsabar sonkai irin naka seka ce ni nafito na aureta,in gaskiya kake yi ka nemo me irin halinta ka aurawa sahabi mana".

Tunda najeeb yafara magana mahaifin salma ke zubar da hawaye,yayin da kabeer se hana najeeb yin maganar yakeyi amman yaƙi denawa,kuma tunda yafara magana akan kunnen salma taji komai.

kuka takeyi numfashinta na sarƙewa,daƙyar tajanyo akwatin kayanta ta ɗauko wata jaka,cike da kuɗi kimanin miliyan ɗaya ɗori,ta ɗauko jakar tafito dagudu zuwa tsakar gidan,kuka take kamar ranta ze fita ta ajiye jakar akan cinyar najeeb tace cikin kuka.


"ƙarya kake najeeb kana sona wlh karya kakeyi,inde sabida satar danayimakace to ga kuɗinkanan karka kuma kirana da ɓarauniya,najeeb nimesonkace,karka lalata farincikina,ka saurari zuciyarka najeeb ni takeso kar ka...."numfashintane ya ɗauke ta kife agurin.

A gigice najeeb yayi kanta da sauri babanta yadakatar dashi da cewa.

"inka kuskura kataɓamin ƴa,wallahi se ka raina kanka,kuma yanzu base anjimaba ka ɓacemin da gani,wanda besan darajar manyaba"

Najeeb hankalinshi nakan salma,wacce jini yake fitowa ta bakinta,duk yagigice ya rasa abinda kemasa daɗi,kabeer ne yayi yunƙurin bada haƙuri amman ina be sauraresuba dole kabeer yaja najeeb daƙyar suka nufi hanyar fita,har sunkai ƙofar gidan Abbah yabiyosu,yabasu jakar kuɗinsu,dakyar kabeer ya amsa suka nufi mota,najeeb se tirjewa yake baze tafiba,dakyar kabeer yasashi amota,suna tsaye aka fito da salma akasata a napep,aka wuce da ita asibiti rai a hannun Allah.

Najeeb hawaƴene kebin fuskarshi wanda besan dalilinsuba,ahaka kabeer yaja motar suka ɗau hanyar Abuja.



    *INTERMISSION*



Surbajo for life.



Post a Comment (0)