Ƴar Bautar Ƙasa 17

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*MY BABY MANAL ALLAH YABAKI LAFIYA,DON ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR'ANI,AMEEN😭*


*17*


Koda ta ƙaraso gurin motar tsayawa tayi tana rufe idonta,

Najeeb buɗe ɗayan ɓangaran yayi amman bece mata ta shiga ba.

Jiki asanyaye ta shiga cikin motar ta zauna,ta maida murfin ta rufe.

Rusunar da kanta tayi sannan tace.

"doctor an wuni lafiya?ya bayan rabuwa?"

Shuru yayi be kulata ba,ƙarshema se yayi adjusting ɗin kujerar ya kwanta,ya lumshe idonsa,

Salma duk ta takura,dan ita yanzu cika mata ido yakeyi,gawata uwar kunyarshi da take ji datake hanata sukuni.

"Doctor dan Allah kayi magana mana"salma ta faɗi cikin wani salo wanda ita kanta batasan tayiba.

Da sauri doctor ya buɗe idonsa yana kallonta sabida salon yadda tayi maganar ya shigeshi.

"in nayi maganar me kikeso nace"cewar doctor cikin muryar da ke nuna kulawa.

shagwaɓe fuska salma tayi sannan tace.

"Haba doctor yanzu abinda zakace ɗinma nizan faɗa maka?"

Idonshi ya ɗan lumshe yana kallonta,sannan yace.

"To ayni ban iya surutubane shiyasa nace ki faɗamin abinda zance"

Turo baki gaba tayi sannan tace.

"to kace komai mana"

"to nace komai"doctor ya faɗi yana haska fuskarta datasha kwalliya da wayarshi.

"Wannan kwalliyar wakika yiwa?"

Zaro ido salma tayi sannan cikin inda inda tace..

"ba wanda nayiwa kawai de nayine"

Tissue ya miƙa mata yace.

"to amshi ki goge tunda bawanda kikayiwa"

"in nashiga gida zan goge"salma tabashi amsa.

Shuru yayi yana binta da ido,ya rasa yanayin dayake tsintar kanshi in salma tana magana.

Hannu ya miƙa sit ɗin baya ya ɗauko ledar kayanta data manta.

miƙa mata yayi ta amsa taɗan buɗe dan ganin abinda ke ciki,ay tana buɗewa taci karo da fant ɗinta nagidan yari wanda farine azabar datti ta maidashi ash,ay salma bata tsaya wata wataba tabuɗe motar riƙe da ledar ta kwasa da gudu zuwa cikin gida.

Ba ƙaramin dariya gudun nata yaba doctor ba,da ƙyar yaja motar yabaro ƙofar gidan,yakama hanyar,kano sabida mahaifinshi yadawo yana gari.

Salma ko bata dena guduba seda ta dangana da gadonta.

Dariya da kunyane suka dirar mata lokaci guda,haka taita darawa ita kaɗai aɗaki.

Miƙewa tayi takai wandon da doguwar rigar data fito dasu daga gidan yarin,taje tasaka a shara sannan taje ta buɗe ledar ragowar kayan daya siya matane aciki,se sabon takalmin daya saimata ranar dazasu zo kaduna ta manta dashi a motar shi.se rafer ta kuɗi kimanin dubu hamsin,se waya ƙirar samsung galaxy s7edge.silver colour.

Ɗaukar kayan tayi gaba ɗaya taje ta nunawa ummanta da sahabi,sosai siyayyar tabasu mamaki.

bama kamar ummanta dan cewa tayi.

"salamatu kode sonki yakeyine,wannan bawan Allahn,inde ba so ba ay hidimar tayi yawa"

"wlh umma ba sona yakeyiba,kawai de halinshine kyauta koda besan mutumba"


Fatan alkhairi sukayi gameda hakan sannan salma taba sahabi kuɗin tace yaƙara ƙarfin jarinshi yakoma kasuwa da saida kayan miyan.

Da ƙyar sahabi ya amshi kuɗin,shima seda ummansu tasa baki,godiya yayiwa salmar sosai.

Daga haka ta kwashe sauran kayan tawuce ɗakinta,farincikine fal zuciyarta,dan ita babu abinda yafi burgeta a tsarabar kamar wayar daya siya mata.

Koda taje saka charge ganinta tayi acike wato anmata chargen ta,harda sim card aciki na mtn.

Game tayi taɗan duba abinda baa rasaba ta ajiye wayar tayi sallar ishai sannan taje tayiwa ummanta seda safe,tadawo ɗakinta ta kwanta,ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.

Shiko doctor be isa kano ba se shaɗaya na dare,kowa yayi bacci dsn haka shima ɗakinshi ya buɗe ya kwanta bayan yayi wanka yayi sallah.

koda ya kwanta sam baccin ya gudu,tunanin salma da muryarta kawai yakeyi,ganin ba sarki se Allah ne yasa ya jawo wayarshi yafara kiran layin daya samata a wayar,seda yakira har so uku bata ɗagaba,da kamar ya haƙura sekuma yasake kira,ayko kamar jira yana kira ta ɗauka,tayi sallamah cikin muryarta ta bacci.

Shuru doctor yayi yana sauraron saukar numfashinta.itace ta katse shi da cewa.

"doctor ko kayi bacci ne?"

"waya ce miki shine ya kiraki"cewar doctor.

murmushi salma tayi sannan tace,

"sabida sanin danayi shikaɗai ze iya kirana ta layin da shine ya siya kuma ban ba kowa"

"hmmm to sannunki,da gudu,watarana inkina irin wannan gudun sekin fasa baki"

Dariya salma tayi batace komaiba.

shima shuru yayi beceba

"doctor naga abin arziƙi nagode Allah ya ƙara buɗi"

hakade yadunga sata magana shide sede yayi shuru,salma bata fargaba sejin saukar numfashin shi takeyi alamar yayi bacci,dariya tayi takashe wayar itama ta kwanta.



Post a Comment (0)