ƘAWAR MATAR KA

🧕🏻 *ƘAWAR MATARKA ITACE ABAR TSORO, BA MATARKA BA*🧕🏻

🧕🏻 Kada ka riƙa jin tsoron matarka, domin ba itace abar tsoron ba, kuma kada kariƙa kawar da kanka akan waɗanda matarka ke ƙawance da su, saboda zuciyar mace tana da rauni domin nan da nan za'a iya sauya mata tunani da rayuwa sai dai wacce Allah yatsare.

 🧕🏻Ka san ƙawarta wacce suke tare tazo gidanta ko ita taje gidanta kuwa ? to ai itace abar tsoron, saboda bakasan kirkinta ko rashin kirkinta ba, Kuma ya kamata kanutsu karika sanya idanuwa akan ƙawayen da matarka ke da su, don gudun kar aje arikita maka gida.

🧕🏻Saboda bakasan me take karanta mata ba, wata ƙila matarka mutuniyar kirki ce, tana yimaka ladabi da biyayya amma sai kaga ta haɗu da muguwar ƙawa wacce zata sauya mata rayuwa. Kar ka nuna ai ba ruwanka domin aƙarshe kaine ruwan zai shafa, za kasha nadama mara amfani, Allah yakyauta.

🧕🏻Acikin ƙawaye akwai na kirki akwai ɓata gari, kiyi amfani da hankalinki wajan tantancewa. Musulunci ya yi mana umarnin duba abokai nagari, kai ma haƙƙinka ne kariƙa lura da ƙawayen matarka ko abokan ƴaƴanka, domin gudun abinda ka iya zuwa yadawo.

Allah yakyauta kuma yaƙara tabbatar da zaman lafiya atsakanin ma'auratanmu.

✍🏻 *Idris M Rismawy*
Post a Comment (0)