GUZIRIN JUMA'A

🌼 *GUZURIN JUMA'A* 🌼

*Al-AllΓ’mah Ibn Qayyim Aljauzy* yana cewa:

🌼 *Salatin* da bawa zai yiwa *Manzon Allah* (S.a.w), yabo ne gareSHI, tare da fatan Allah yaΖ™ara Ι—aukaka ambaton SA, yaΖ™ara maSA girma da Ι—aukaka.

🌼 Sakamako yana daga nau'in irin aikin da mutum yagabatar. Duk wanda ya yabi *Annabi (s.a.w)* sai Allah yasaka masa da irin aikin da yagabatar ta yadda za a yabeshi kuma a Ζ™ara masa Ι—aukaka da girma."

🌼 *Ya Allah ! Salati da AmincinKA sukara tabbata ga BawanKA kuma ManzonKA , Shi da IyalanSA da SahabbanSA bΓ’ki Ι—ayansu, da duk waΙ—anda suka biyosu da kyautatawa har izuwa ranar sakamako*🌼

*Idris M Rismawy*
Post a Comment (0)