BUSHIYA

BUSHIYA....

*Ku karanta da kyau, kuma a natse... 

Bushiya ba ta iya kusantar 'yan uwanta.. domin kayoyin da suka mamaye jikinsu sun zamo masu tamkar wata kariya ce, ba wai kariya ga barin makiyansu kawai ba, a'a har da 'yan uwa da abokan arziki... 

A lokacin sanyi da hunturu, idan sanyi ya yi tsananin, iska ta yawaita, dole take sanya bushiyaye su kusanci juna, saboda neman dumi, amma fa dole su jure wa zafin sukar kayoyi.. Idan sun dan sha dumin juna kuma, sai su kara ja da baya da juna, ba za su kara kusantar juna ba sai idan tsananin sanyi ya kara riskar su.. A haka suke kwana suke tashi, wani lokaci su kusanci juna, wani lokaci kuma su yi nesa da juna.. domin idan suka ce za su dinga zama a manne da juna, to kuwa dole su yi hakuri da zama cikin miki da rauni masu haifar da radadi mai tsanani.. Idan kuma suka dauki matakin rabuwa da juna gaba daya, to kuwa mutuwa ce za ta dauke su duka, daya bayan daya...

Mu ma mutane haka dangantakar mu take da juna, babu wanda ba shi da kayoyin da suka zagaye shi, amma kuma ba za mu taba samun dumin juna ba sai mun yi hakuri gami da juriyar sukar kaya, da radadinta.. 

* Duk wanda yake neman abokin da ba shi da aibi, to kuwa shi kadai zai mutu.. 

* Duk wanda yake neman matar da babu naqasa a tare da ita, ko mijin da babu naqasa a tare da shi, to kuwa zai rayu gwauro, ko gwauruwa... 

* Duk wanda yake neman dan uwan da babu matsala a tare da shi, to kuwa zai mutu bai kammala bincike ba.. 

* Duk wanda yake neman dan uwa makusanci kamili, to kuwa zai yi ta yayyanke zumuncinsa.. 

Saboda haka dole ne mu yi hakuri, mu kuma jure wa sukar da za ta zo mana daga junanmu, domin rayuwarmu ta sami daidaito.. 

Ba komai ne za ka fassara ba, ba kuma komai ne za ka yi masa bin kwakkwafi ba, mutanen da suka dage sai sun gano asalin "diamond", a karshe sun gano cewa bai wuce gawwayi ba... 

Kada ka matsa sai ka bi diddigi mutane, kamata ya yi ka wadatu da alhairin da suke bayyana maka a zahiri, ka bar abin da yake cikin zuciya ga Ubangijin bayi...

«Tarjamar daga Larabci... »
Post a Comment (0)