YAUSHE ZAKIYI AURE???

*YAUSHE ZAKIYI AURE???* 



Me yasa wannan tambayar ita take zamana abu na farko tsakanin duk wasu manya da na kasa dasu da Allah bai kawoma mazaje ba? 

Har sai yaushe ne zaku fahimci tambaya ce da bata da amsa? Har sai yaushe zaku gane girman kalaman da ciwon su ga wanda kuke ma tambayar? Har sai yaushe zaku fahimci aure da mutuwa na cikin abubuwan da sanin lokacin su na wajen Allah? Saboda me ba zaku gane duk yanda kuke son suyi aure ba kukai da su ba? 

Me yasa kuke sa suna jin kamar jinkirin zuwan lokacin auren su laifin su ne? Kun saka damuwa a zukatan mahaifiyarsu da tambaya akan abinda bata san lokacin shi ba, ko yaushe kuka hadu wajen bikin Ya'ya baku da maganganu da suka wuce 

"Sauran na Aisha"

"Halima yaushe zamu zo mu sha nata bikin?'

"Wai ita kam Zainab sai yaushe ne?"

Dame zata ji? Ba saikun tuna mata 'Yar ta bata samu miji ba, ba saikun kara mata damuwa kan wadda take ciki ba. Ba sai kunsa damuwarta ta kara ma 'Yarta damuwa ba. Yaushe zaku gane su duka biyun cikin bugun zuciya suke duk lokacin da wani biki ya kusanto? 

Me kuke so suyi? Suyi rubutu su manna a kofar gidajen su? 'Yan matan suyi kwalliya suna bin layi? Kowanne tarkace ya taya su amsa? Sai kuma ya zamana da ku ake zagaye ana zagin su ko? Ai maman su lantana tana ganinta tana kule-kule, harda dan iskan yaron nan shima zuwa yake zance wajenta. 

Me ma ya faru da bakinka ya fadi alkhairi ko yai shiru? Waya baka tabbas zuciyarka ba zata tsaya ba lokacin da kake tsakiya da aikata abinda bai shafi rayuwarka ba? Waya baka tabbas akan dawwamar naka auren? Waya ce komai zaici gaba da dai-daita a wajenka da zaka dora ayar tambaya akan rayuwar wasu? 

Bazan tsawaita zance na ba wannan karin. Sai dai duk lokacin da naji

"Sa'anin ki yanzun fa harda masu yara uku. Me yake faruwa ne? Yaushe zakiyi auren ke?"

Dakyar zuciyata kan jure maida amsar da tawa tambayar. 

"Gwaggo, inna, anty, kaka, mama, sa'aninki da yawa sun jima a kaburburan su. Me yake faruwa ne? Ya akai ke shiru haka? Ya labarin taki tafiyar? Yaushe ne mutuwar taki?"

Yanda mutuwa bata da lokaci haka ma aure, yanda mutuwa ba gasa bace hakama lokacin aure, yanda burin kowa Aljanna haka burin duk wani marar aure abokin rayuwa nagari. Yanda ba'a rubuta ma kowa lokacin mutuwarshi a goshin shi ba, hakama wasu ba'a rubuta musu rabon aure a rayuwar su ba. 

Bazai rage ka da komai ba in kaja bakin kakai shiru, kowa rayuwa daya yake da ita. Dan Allah karka zamana sanadin kara kunci a zaman duniyar wasu. Allah ya datar damu. Amin thumma amin.


Post a Comment (0)