DAUKE ABIN CUTARWA DAGA KAN HANYA

*_DAUKE ABIN CUTARWA DAGA KAN HANYA_*

Yana cikin hakkin zama akan hanya dauke abin cutarwa daga kan hanya yin hakan yana cikin imani.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Imani yana da reshe guda saba'in da wani abu,mafi falalar reshe shine fadar:ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، mafi kankantarsa shine dauke abin cutarwa akan hanya,kunya wani yankine daga cikin imani)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

Dauke abin cutarwa daga kan hanya Sadakane kuma hanyace ta kai mutum zuwa aljanna.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Kowace gaba ta dan Adam an dora mata aikin Sadaka a kowane yini,......kuma dauke abin cutarwa daga kan hanya sadakane)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Wani mutum yana tafiya akan hanya sai yaga wata kaya da take cutar da mutane sai ya sareta sai Allah ya godewa Aikisa sai ya gafarta masa......)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Annabi SAW yana cewa;
*(Wani mutum da bai taba aikata wani alkhairi ko sau daya ba sai wata itaciyar kaya mai cutar da mutane,sai Allah ya godewa aikinsa ya sanyasa a aljanna)*
@رواه ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ

  Allah ne mafi sani

Allah bamu ikon sauke wannan hakki

Rubutawar: ✍
*_Malam Mustapha Musa Abu Aisha {Hafizahullah}._*

Post a Comment (0)