*_DUK WANI ABU DA YAKE DANGANTUWA GA AL-QUR'ANI YA KAN ZAMA MAI GIRMA._*
👉 Mala'ika Jibril shine ya saukar da Al-
Qur'ani, sai ya zama shugaban Mala'iku.
👉 Manzon Allah ﷺ shine wanda aka
saukar wa da Al-Qur'ani, sai ya zama
shugaban Annabawa da Manzanni.
👉 Wannan Al'umma an saukar mata Al-
Qur'ani, sai suka zama mafi alherin al'umma.
👉 Watan Ramadan shine watan da aka saukar da Al-Qur'ani, sai ya zama wata mai daraja da falala.
👉 A daren Lailatul Qadr aka saukar da Al-Qur'ani, sai ya zama shine mafi alherin dare.
👉 Haka nan duk wanda Al-Qur'ani ya shiga zuciyarsa zai zama mafi alherin mutane, saboda Manzon Allah ﷺ ya ce: "Mafi alherin ku shine wanda ya koyi al-qur'ani kuma ya koyar da shi".
Via Hikimomi da kalaman magabata.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.