*_HIKIMOMIN DA ZAKKA TA KUNSA!!_*
Zakka 'yar'uwar sallah ce a cikin Alqur'ani, a wurare da yawa Allah yana hada sallah da zakka, saboda sallah hakkin Allah ne, zakka kuma ta kunshi kyautatawa bayi, bawa yana samun kamala idan ya bada hakkin Allah da hakkin bayinsa, ga wasu daga cikin hikimomin da suka sa aka shar'anta ta:
1. Nuna godiya ga ni'imar Allah, saboda dukiya ni'ima ce daga cikin ni'imomi.
2. Tsarkake dukiya da kuma mai dukiyar, saboda zakka tana kare dukiya daga halaka, sannan tana koya mutum kyauta da karamci ta kuma kare shi daga rowa.
3. Taimakawa talakawa da toshe bukatunsu.
4. Samun kyakykyawar alaka tsakanin talaka da mai kudi, saboda duk lokacin da mai kudi yake bawa talaka zakka, ba za'a samu hassada a tsakaninsu ba.
5. Fitar da zakka yana sanya zuciya ta nutsu da maye gurbin da Allah yake yiwa wanda ya fitar da ita, duk wanda yake fitar da zakka Allah zai zuba masa alkairi a dukiyarsa, fiye da zatonsa.
6. Kankare zunubai, da samun daraja mai girma a wajan Allah.
7. Tabbatar da imani da kuma cika musulunci, saboda zakka tana cika addinin mutum, don duk wanda ba ya fitar da ita, dukiyarsa za ta zamar masa azaba ranar alkiyama.
*WADANNAN KADAN KENAN DAGA CIKIN MANUFOFI DA KUMA HIKIMOMIN DA ZAKKA TA KUNSA.*
18/1/2013
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
___________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.