HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA

*_HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA_*

                               *Tambaya*
Assalamu alaikum.
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?

                                   *Amsa*
Wa'alaiku musaalam, To dan'uwa Allah Madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida aya mai lamba ta: (5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda.
Duba: Ahkamu-ahlizzimah 2\794

Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu.

Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci.

Allah ne mafi sani.

11/6/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Samir Salisu

_*سبحانك اللهم وبحمدك اشهد ان لااله الا انت استغفرك واتوب اليك*_

_Ku ci gaba da kasance da zauren As-sunnah_

_Domin shiga zauren zaka iya tura suna da adreshi ta wannan nambar_

WhatsApp👇👇
*08060967385*

Post a Comment (0)