KAI KU TAYA SHI MANA

KAI KU TAYA SHI MANA

Wani dattijo ne yayi niyyar Noman gyada da damina, Ranar da aka yi ruwa mai yawa sai ya je Gona, ya na fara huda sai kawai ya ji ance kai Ku taya shi mana!!! 
Kawai sai yaga an hude gonar baki daya, washegari ya zo da nufin yayi shuka, yana sarawa zai fara shuka sai ya ji an ce kai Ku taya shi mana!!! 
Sai ya ga an shuke gona duka. Haka dai duk lokacin da yazo aiki a gona sai ya ji ance kai Ku taya shi mana. 
Har sai da Gyada ta isa roro ya zo ya fara aiki sai ya ji an ce kai ku taya shi mana. 
Nan take aka gama aikin roron Gyada. 
Sai ya dan dauki daya ya ci. 
Kawai sai ya ji an ce kai ku taya shi mana. Nan da nan suka cinye Gyada. 
Ashe aljanu ne.

Kai ku tayani mana!!!! ---->
Amman banda dariya😄😄😄😄😄😄


 
Post a Comment (0)