Assalamu Alaikum Warahmatullah.
'Yan uwana 'yan social media! Kashedinku da yada posting din da baku san ingancinsa ba. Domin zaka iya yin taimakekeniya wajen yada 6arna da hannunka ba tare da ka ankare ba.
Sau dayawa sai wani mutum ya zauna ya qirqiri wani rubutu mai ma'ana, amma daga qarshe saboda tsabar son zuciya sai ya danganta rubutun da Manzon Allah (ο·Ί) domin ya jawo hankalin mutane zuwa ga rubutun. Wannan ba qaramin al'amari bane 'Yan uwa, domin duk wanda ya qirqiri qarya da gan-gan ya danganta ta da Annabi (ο·Ί), to ya tanadi makomarsa a wuta. Shin a hakan kuma muke qoqarin taimaka masu wajen aikata wannan mummunan aiki?
'Yan uwa mu hankalta, duk wani post da a qarshe zaku ga an rubuta ku turawa mutane guda kaza, ko groups kaza, tare da cewa zaku ga wani alkhairi idan kun yi hakan, ko wani abin sharri zai same ku idan baku yi ba. To ku guji karanta da tura irin waΔannan post din.
Haka kuma duk wani post da zaku ga an kawo hadisi amma ba a fadi littafin da aka samo hadisin ba, da waΔanda suka ruwaito shi, to mu yi taka tsan-tsan wajen tura irin waΔannan post din.
'Yan uwa a takaice, mu tashi mu yi karatu domin mu tsira daga irin waΔannan rudanin.
Sannan duk wani post da bamu tabbatar da ingancinsa ba, to mu bar shi a inda muka gan shi, kada mu yi share ko forward dinsa.
Allah Ya sa mudace.
.
Daga dalibinku:
*✍πΎAyyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
*14-01-1440Ah.*
*24-09-2018.*