MAIRO 02

*♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*2*

gwaggo na k'ok'arin fita halilu na k'ok'arin  shigowa sukaci karo nan taci kwalarsa ta k'asara shigowa dashi tana masifa "ashe baka da hankali halilu dan kana magu zaka sa ecce ka bugawa Mairo bancin bugun da Almu yayi mata wai mi ta tare maka ne?"
kai ya girgiza "haba gwaggo wai miyasa duk tazo tayi miki k'arya saiki yarda ya za'aiyi na buga mata ecce fisabilillahi?"
"ai halinka na sani ba sonta kake ba zaka iya mata komai"
kallon mairo yayi da tayi shiru tana kallonsu kamar wata munafuka yace "ke dukanki nayi?"
kai ta daga ta turo baki tana matsar kwallah.
"eh gurin da Almu ya karyani ka buga min ecce"
gwaggo ta kara ciyo kwalarsa "mugu yanzu abunda kake ya kamata kenan a gaban idonka ka bari Almu yayi mata wannan illar wai miyasa baka son yarinyar nan ne halilu?"
"ohhh gwaggo haba haba wane irin illa Almu zaiyi mata rashin kunya fa tayiwa tsohuwar mutane shine ya dan zingureta fa"
gwaggo tace "tho ina ruwansa ya zingureta haihuwarta yayi kuma karya kake karyata yayi"
"haba gwaggo yarinyar da aka karya zata iya kawo kanta gida har ta iya faɗa miki an karya ta ai saidai a kawo miki ita"
saki kwalarsa gwaggo tayi ta nufi Mairo ta shiga duba k'afar.
aiko nan mairo ta k'ara marairaicewa tana "wayyoh k'afata" gwaggo ta duba bata ga alamun kariya a k'afarta ba ko alamun jimuwa babu barre karaya ta data gwaggo tayi tsaye "tashi kiyi tafiya na gani"
nan ta lak'e kafar "wayyo bazan iya takata ba gwaggo ta riga ta karye"
cikin dabara halilu ya cire takalminsa ya jefa mata iya karfinsa aiko da gudu ta faɗa ɗaki tana ihu.
matsowa yayi kusa da gwaggo ya ɗauki takamin yana faɗin "yanzu wadda aka karya zata iya wannan gudun?"

shiru gwaggo tayi halilu yace "gwaggo wata rana saita saki kunya matukar duk abunda tazo ta faɗa miki kina yarda dashi tho ko zaki ɓata da kowa"
tsaki gwaggo taja "mtsss tho sai mi dan na ɓata da kowa akanta so kake na zuba ido ina kallon ana cin amanarta? ko kai ka taɓa ta saina taɓa ka bare wani can"
halilu bai kara cewa komai ba banda kan da ya girgiza ya fice ya barta tana masifarta.
saida Mairo taji fitarsa sannan ta fito tana kukan munafurci.
nan gwaggo tayi cikinta ta masifa "Allah mairo in kina zuwa kina min karya saina ɓata miki rai kuma na ɓata dake na fita harkarki"
    kwantowa tayi jikinta tana kukan shgwaɓa "tho ai ba karya nake ba Almu ya dakeni kuma Halilu ya zaggamin bulala"
tureta gwaggo tayi "amman ai cemin kikayi shiya buga miki ecce Almu kuma ya karyaki"
turo baki tayi
"eh karya nake amman dai sun dakeni dukansu"
"tho miyasa kika min karya kuma halilu yace ai tsohuwa kikayiwa rashin kunya"
"tho gwaggo ai itace ta samin baki a magana kuma tace min masifaffiya"
"amman ai kinsan na hanaki rashin kunya da karya ko ni daga yau babu ruwana dake"
kuka ta shiga rerawa "na daina gwaggo dan Allah kar kiyi fushi dani ba zan kara ba"
gwaggo bata so kuka mairo ko kaɗan janyota tayi jikinta "shi kenan bazanyi fushi dake ba amman ki daina kinji ba kyau kuma bana so"
"na daina daga yau ni ko kallon mutane bazan sakeyi ba"
gwaggo tayi dariya tace "rufe da ido zaki rika yawo kenan?"
"eh bazan sake kallon mutane ba bare suce nayi musu rashin kunya"
gwaggo ta shafa kanta "a'a kawai ki rika jin magana kibar rashin kunya yayi basai kim rufe idoba"
dariya mairo tayi "ai wasa nake miki gwaggo ya za'ayi na rufe ido kina son na fada rijiyane ko rame?"
dundu gwaggo ta kaimata a baya tana dariya "oh baki daina karyar ba kenan ko?"
"na daina Allah yanzu ko zanyi kaɗan zanyi"
gwaggo ta girgiza kai "a,a ki daina gaba ɗaya dai wai ina kika baro min tulu?"
"yana can kogi ni gaskiya gwaggo daga yau bazan kara zuwa ɗiban ruwa ba kullum ni nake zuwa kuma yar k'ank'anuwa dani shi halilu da yake k'ato bazai jeba sai ni shiyasa suke dukana sunga ni banida girma"
cike da shagwaɓa take maganar tana son yin kuka.
gwaggo ta shafa bayanta "shikenan bazaki sake zuwa ba halilu ne zai rik'a ɗebowa"
rumgumeta mairo tayi tana murna.

'''        * * *'''

_2:13pm..._
gwaggo ta kare dahuwar giɗar ta ta zuba a gwango.
ta kwalawa Mairo kira da sauri ta fito tana ɗaurin ɗankwali rabin fuskarta duk fodace da bata shafu ba.
"na'am gwaggo kin kare?"
saida ta kare lisafin sannan ta ɗago ta kalleta tace "ta ɗari biu da arba'ince"
ɓata fuska mairo tayi "gaskiya gwaggo saidai ace ta ɗari biu da talatin dai dan gaskiya zan ɗauki ɗaya"
gwaggo tace "ɗauki ko nawa kike so mairo waya isa ya hanaki?"
murmushi tayi ta duka ta ɗauki turen tana faɗin "yau duka zan siyar"
"tho Allah bada sa'ah amman dai hodarki bata shafu ba mairo"
turo baki tayi "nidai gwaggo bana son haka bani na shafa ba nidai haka zanje"
hannu gwaggo ta ɗaga mata "jeki jeki Allah bada sa'ah inda yanzu kuma ban faɗa miki ba ki hauni da masifa"
batace komai ba ta ɗora turen samsn kai ta nufi kofa.
gwaggo ido ta sakar mata a ranta tana _Allah ya shirya minke mairo ya tsare_

© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)