MAIRO 05

♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*5*

tana tafe saman hanya tana cin apple ɗin tana ɗariya.
koda ta iso gida taci kusan guda 4 ɗayan ma da giɗa ta haɗashi ta ci a kofar gida ta tsaya ta karasa na biyar ɗin sannan ta shiga tana watsar hak'ora

Gwaggo na zaune k'ark'ashi ecce durumi taɓa jan carbi Mairo ta shigo
"fuwan (gafaran) kudai masu gida"
murmushi Gwaggo tayi jin yau abunda Mairo ta shigo dashi sabanin sallamar data saba.
kusa da ita Mairo ta zauna ta eje mata turen giɗar gabanta ta zuba mata ido.
Gwaggo saida ta kai karshen carbin ta shafa sannan ta kalli Mairo da fuskar damuwa tace "yanzu Mairo tun fitar da kikayi giɗa ɗaya kika siyar?"
ɗariya tayi ta ɗauki apple takai bakinta tace "ɗayar ma cinta nayi ba siyarwa ba"
kai Gwaggo ta girgiza "yayi miki kyau yanzu ai saiki ce na baki na sawa asusu ko na siyen wani abu"
fashewa tayi da dariya harda buga k'afa ta ɗauki apple ɗaya ta mikawa Gwaggo "Gwaggo karbi ki ci goribar bunni"
banza Gwaggo tayi mata ta kara hade fuska.
nan Mairo ta ciro  kuɗin dake lak'ame a k'ugunta ta ajewa Gwaggo
"nidai ga kuɗinki nan har ma sun ninka na giɗar"
buɗe baki Gwaggo tayi tayo waje da ido "Mairo ina kika samu wannan kuɗin mai yawa haka?"
"wani ɗan bunni ne ya bani harda wannan goribar shine ya bani kuma fa kuɗin da yawa ne nice na ɗebo kaɗan"
kallon tsoro Gwaggo tayi mata "ina kika haɗu dashi Mairo"
kwantayi tayi saman k'afafunta ta soma bata labari tun farkon fitarta.
      
Mairo na kaiwa karshe Gwaggo ta ɗora hanu bisa kai tana salati
"Hasbunallahu wa ni imal wakil innalillahi wa inna ilaihi raji'un Mairo mi ya kaike mi yasa bakisan ciyon kanki ba Mairo mun shiga uku da wannan 'ya mai ya kaiki shiga can?"

Tashi Mairo tayi zaune tana kallon Gwoggo gabanta soma faduwa.
“minene hala Gwaggo?”
“Mairo kinyi gamo miya kaiki Mairo”
baki Mairo ta saki “gamon me Gwaggo?”
kamin Gwaggo tayi magana sukaji sallamar Halilu da sauri Mairo ta shige cikin Gwaggo tana fad'in “Gwaggo karki fad'a masa”
koda ya karaso Mairo yake kallon ganin yadda ta ahige cikin Gwaggo dan yasan ruwa baya tsami banza gashi kuma Gwaggo na kuka.
“Lafiya Gwaggo miya faru kike kuka?”
da sauri Mairo tace “bata da lafiya ne shine take kuka”
risinawa yayi yana fad'in “Subhanallah mi yake damunki?”
Mairo tace “ciyon kai ne da ciki yake damunta ko Gwaggo?”
Kai Gwaggo ta girgiza Alamar 'ah ah' nan cikin Mairo ya duri ruwa hannu tasa ta toshe bakin Gwaggo tana fadin “dan Allah Gwaggo karki fada masa dan Allah”
tsawa Halilu ya katsa mata “jaye mata hannunki kona miki duka yanzu”
da sauri ta janye hannun idonta cike da hawaye.
hannu Gwaggo ya rike yana fadin “dan Allah Gwaggo ki fada min abunda ya faru”
cikin kuka ta soma fada masa abunda ya faru.
raku6ewa Mairo tayi gefe tana hawaye.

Halilu ya juyo yana harararta yace "ashe haukarki Mairo har takai kiyi wannan kasadar?"
Gwaggo tace "ni tsoro ma nake ji in basu shige mata ba"
Halilu yace "wane irin shige mata Gwaggo aini bako ta aljanu nake ba ya mutanen nan nake yan yankan kai ko yan iska tunda zamani yanzu ya chaja babu babba babu yaro inma aljanune ai da sauki"
sai a lokacin wannan tunanin ya zowa Gwaggo kallon Halilu tayi tace "kana da gaskiya Halilu tunda kaga harda goribar burni ya bata wata kila akwai abu a ciki"
Kallon apple ɗin dake saman ture Halilu ya kalla "ragowarce nan?"
"eh itace taci guda shida tace koma minene ai ta cinye shikenan"
da kuka ta karasa maganar.
Ayatul-kursiyu Halilu ya karanta sannan ya ɗauki sauran biu da suka rage ya jefar bayan gida ya juyo gurin ecce durumi ya kallo ya hau Mairo da duka.

ihu take tayi ko ina ana jinta babu wanda take kira sai Gwaggo tana faɗin kasheta zaiyi.
wannan karon kan Gwaggo ba tayi unkurin hanashi ba dan itama ta tsorata da lamarin Mairo
mak'ota ne suka shigo suka caceta koshi daker dan mugun rik'o Halilu yayi mata saida bulalar ta kwanta mata a jiki.
kowa tambayar yake dalilin dokan da akayi mata Halilu dai baice komai ba ya fice Gwaggo ce take cewa kuɗin tallah ta zubar kuma an sata aiki taki tayi
wasu dai basu yarda ba dan sunsan yadda Gwaggo take son Mairo duk abunda zaisa ayi mata wannan dukan ta kyale batayi magana ba ba karami bane.
haka suka fice kowa da abunda yake faɗa,

                 '''*   *   *'''
kuka kan Mairo ta shashi har ta gaji tun tana iya ɗaga murya har ta koma kiran baba.
tausayinta ne ya kama Gwaggo tana cikin ɗaki ta fito ta nufi ta tadata zaune tana kaɗe mata jiki "dan Allah Mairo ki rika jin magana ki gyara halinki ki daina wannan halin"
kai Mairo ta ɗaga mata tana shisshekar kuka kamar zuciyarta zata fito idonta sunyi mugun ja.
hannunta Gwaggo ta rik'a suka shiga banɗaki wannanka tayi mata sannan suka fito,
Mairo na shiga ɗaki ko kaya bata saba ta faɗa saman gado ta soma wahalallen bachi

_8:15pm..._
gwaggo ta tashe ta taci abinci.
da ciyon kai ta tashi saboda kukan da tasha gashi kuma tayi bachi hannunta Gwaggo ta riko suka fito.
saida ta wanke mata ido sannan ta nufo tabarma.
Halilu dai kallonsu kawai yake yan mamakin irin son da Gwaggo take yiwa Mairo
saida ta zauna sannan ta zaunar da ita saman cinanunta (cinyoyi) ta shiga bata abincin da hannunta.
kai Halilu ya girgaza yace "Gwaggo kinga irin wannan sagartar da kike nuna mata shi yasa take kara lalacewa tana rashin jin maganar nan"
tsaki Gwaggo taja ta watsa masa harara sai yanzu take jin haushin dukan da yayima Mairo.
bai sake ce mata komai ba harta kare bata abinci ta bata ruwa kamar wata jaririya ta zaunar da ita saman  tabarma tana k'ok'arin tashi Mairo ta rik'o hannunta tace "Gwaggo kin daina sona ko?"
dawowa tayi ta zauna tana shafa fuskarta tace "ina sonki Mairo inban so kiba wazan so  halinki ne bana so koshi kuma na rashin jin nan da kikene ina sonki Mairo"
saida ta kalli Halilu dake kallonta sannan ta sake kallon Gwaggo tace "tho miyasa kika bari Halilu ya dakeni ɗazin?"
"saboda abunda kikayi baki kyauta ba kuma inason ya zamo miki dalilin da zaisa bazaki sake irin abunda kikayi ba ko makamancinshi"
jikinta ta shiga nunawa Gwaggo da ko ina kwancin bulalane "amman Gwaggo ai kwarai dakeni dubi jikina kuma inata kiranki ki ceceni kika kyaleni"
"na daina Mairo daga yau babu wadda zai sake dukanki bazan bari ba kiyi hak'uri kinji"
kai ta ɗaga mata tana hawaye.
Gwaggo tace “amman fa ki rika jin magana kinji?”
“na daina daga yau bazan sake ba Gwaggo har na mutu”
tashi Halilu yayi ya nufi kofa yana faɗin “indai dukane tho yanxu kika fara shanshi har sai ranar da kikayi hankali” kukan shagwaɓa ta shigayi “Gwaggo ce ya kyaleni bana sonsa”
“a a ki daina cewa baki son sa amman dai dukakan bazan bari ya sake miki shi ba”
kai Mairo ta ɗaga mata tana share hawaye.

© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)