MAIRO 08

♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*8*

da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba ɗan kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa,

shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)
tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya,

yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su.

can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k'ofar gidan mu ko naa muku hegen duka”
maganar take tana wani ɗageɗage da marmaɗen ido.
          duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba
yarinya ɗaya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faɗin “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kanki”
kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faɗawa wannan maganar  zaki ko ci ubanki yanzu”
ɗankwalinta ta cire ta k'ulle kuɗin giɗar dake hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a k'ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faɗa da juna,

kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k'arfi ba ɗaya ba gashi  daman can  Mairo ba wani k'arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.
ɗukan k'warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faɗin “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-”
Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.
nan Mairo ta faɗi ta fashe da kuka
da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito.

kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik'e da ɗankwalinta a hannu kanta kuma duk k'asa ta shiga gida,
da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.
da sauri ta ɗago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?”
kai ta girgiza mata ta shiga faɗa mata abunda ya faru,
ɗankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taɓa mota kuma in banda fitina inake ina faɗa da wannan yariyar?”
turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka

“shigar mata kikayi ko Gwaggo?”

“a'a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaɗiba”

“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzu”

“barta da Allah kijin”
kai ta ɗaga “Gwaggo motar wace kofar gida?”

“yan birni ne suka zo ganin gida”

kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina suke”

“sun tafi ganin sauran dangi”
“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?”

“eh kema ai en'uwanki ne tun kima karama marabinsu da nan”
risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama.

Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba,

harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli  Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggo”
“yauwa sannu qasin kai kaɗai ka dawo?”
“eh ina gabansu ne suna hanya suma”
tabarmar dake shinfiɗe k'arkashin ecce ya nufa ana k'ok'arin zaunawa yayiwa Mairo magana
“ke baki eya gaida mutane ba?”
tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna.

“na eya ina wuni?”
“lafiya kalau ya sunaki?"
saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairo”
murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?”
daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ce”
“wane margayi?”
“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k'arama”
shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak'ora,

“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik'onta?”
sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.
“amin wa'alaikassalam alhaji harku dawo?”
“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangi”
momi ce ta amsa mata.
bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faɗin

“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo ɗai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati ɗaya kuyi ko biu”

ɗariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifa”

“yau ni wani haline dani daga faɗar gaskiya”
momi tace

“karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukuna”

taɓe baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karya”
dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.
duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?”

“ashe zaka iya gane ta ai ɗaukar ka manta”
cewar Gwaggo

murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganarta”
mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake magana”

momi tace “eh itace yar marainiya”
“Allah sarki Allah ya jikan mahaifa”
duk suka amsa da Amin.

sun ɗan juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.
gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaɗan sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba.

kuɗi Abbah ya ciro aljihunsa masu ɗan ɗama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurar”
“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?”
“babu komai jamila a daici da hak'uri”
godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.
suna shirin fita Mairo ta laqe kafaɗa ta bata fuska ita saita bisu.

Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasuje”
“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisu”
“kinason ki daina ganina?”
“a a ai dawowa zanyi”
Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?”
kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzu”
Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwa”
faɗa Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaɗi saiku ɗauke ta to baza taje ba”
juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba

aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.
Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima
duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita.

suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,
nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faɗa masa,

nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane  shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinya”
kara buɗe baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya,

Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa ko”

“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musu”

“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisu”

Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimu”
momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin.

Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halinta”

kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.
aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k'asa tasha da gudu ta nufi ɗaki ta shiga haɗa kayanta cikin bakko (ghana most go).


© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)