Mairo 44

... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*44*

Yi tayi kamar bata jishi ba ta cigaba da shafa shi,
Hannun ta ya fisgo da karfi ya yarfar ya tashi tsaye yace "nace miki am not in the mood bakida hankaline?"
Da sauri ta Kalleshi tsantsar É“acin rai ta gani a tare dashi "Yarima mi yake damunka waya É“ata maka rai?"
Sama yayi da kansa "Zil miya kawo ki nan?"
"wannan wace irin magana ce ai kasan banada gurin zuwa sai nan wai wane irin É“acin rai ne ya rufe maka ido haka Yarima Kaga yadda ka koma kuwa?"
Fuskarsa ya shafa yana yak'unar hanci "u are right Ni kaina nasan na chanja na daɗe banga ɓacin rai irin wannan ba ban taɓa sanin inason Maryam ba sai yau kuma kota halin yaya sai na aure ta koda sama da k'asa zasu haɗe"
cikin rashin fahimta tace "ban gane ba Yarima wata kake so ne?"
Murmushi yayi "yes wata kyakkyawar yarinya ce mai k'ananan shekaru kuma yar k'auyen"
Kai ta girgiza "kasan da ni kake faÉ—awa wannan maganar ko dai wani abun kasha?"
tana kare maganar ya wanke mata fuska da mari biu ya nuna ta da yatsa "karki kuskuren faÉ—a min kalmar da zata daÉ—amin É“acin rai É“ace ki bani guri"
yanayin fuskanta naga ya chanja cikin É“acin rai tace "babu inda zanje kawai ka fada min aure zaka yi ko me?"
gira ya É—aga mata "yes aure zanyi tsoronki nake jine"
"tho ni kuma kayi yaya dani?"
"ai nasha faɗa miki Zil bazan taɓa iya aure ki ba maybe bazaki yarda ba har sai kinga matata a cikin gidan nan"
kwalla ne suka cika mata ido cikin muryar tausayi tace "amman ka É“ata min rayuwa Yarima ka raba ni da karatuna kasa na watsarda samarina"
murmusawa yayi ya taso yazo daf da ita ya É—ora hannayensa saman kafaÉ—arta yace "kina da matsala Zil mi yasa kike É—ora min wayannan laifukan koda yaushe ni ban lalata miki rayuwa ba kuÉ—ine suka ja hanalinki kikaga zaki iya kum gwargwado na kyautata miki tunda na baki mota na kai ki makka na mallaka miki gida na cia miki account É—in ki and what else do you need?"
Hannunsa ta rika hawaye nabin fuskanta tace "duk abunda ka zana yanzu ba sune a gabana ba aurenka nake so shine cikar burina"
Kai ya girgiza ya janye hannunsa "am so sorry Zil dear bazan iya yi miki wannan ba"
Cikin É—aga murya tace "ba a haifi matar da zaka aura ba Yarima ba ayika dan ko wace mace ba sai ni kuskure ne kasa son wata a ciki zuciyar ka matukar ina raye"
Fashewa yayi da wata mahaukaciyar dariya yasa kafarsa ya kaÉ—e mata kafafu ta faÉ—i da karfi sai da kashinta ya amsa (yayi kara) sannan ya sake kai mata wani mugun shuri ba shiri ta saki ihu ya nuna ta da yatsa yace "ba'a faÉ—a min irin wannan maganar be careful next time É“ace min da gani"
da sauri tayi baya² ta shige É—aki da kuka,
shi kuma ya zauna saman kujera yana cikama bakinsa iska
bai bar parlor ba sai kusan 3 dare bayan y gama sake² ya nufi bedroom,
zaune ya tararda Zil babu abunda take sai kuka tana rike da kunkurota kamar mai shirin haihuwa, yana kallonta yaja tsaki ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito
yana cikin saka kayan bachi yace "baci zanyi malama ko kiyi shiru koki fita kije gidan ubanki" ba shiri ta hade bakinta ta matse haka rage hasken wutar É—akin yayi kwanciyarsa ya barta zaune.

*WASHE GARI..........*
8:34am Qasin ya shigo part É—in Momi bai iya yin sallama ba saboda bugun gaban daya sami kansa dashi har ya isa dining room,
Nura da Usman suna zaune suna karyawa Momi kuma ta tisa abincin a gaba tana kallon wani guri
Mairo ce ta Kalleshi tace "yaya ina kwana?" da murmushi ya amsa mata "lafiya kalau Maryam an tashi lafiya?"
Kaita É—aga mishi ta na dariya nan suma suka shiga gaida shi bayan ya amsa ya kalli Momi yace "Momi an tashi lafiya?"
ba tare data É—ago ba ta amsa mishi "lafiya kalau"
cikin sanyi jiki yace "dan Allah Momi kiyi hak'uri wallahi banyi-"
kasa k'arasa maganar yayi sakamakon É—agowar da tayi ta É—aga mishi hannu "karka kuskura fitar da kalma ko É—aya daga bakin ka matuk'ar ni zaka furtawa ita kawai ka fita kabar parlor nan"
Nan da nan yanayinsa ya kara chanjawa bugun zuciyarsa ya karu kamar ya fasa kuka yace "dan Allah Momi karkiya fushi dani dan adam ne ni ajizi wallahi banyi hakan dan na É“ata miki rai ba dan Allah ki gafarce ni"
Momi fuska a É—aure tace "bana fushi da kai tun har na iya amsa s
gaisuwarka kawai dai ka É“ace min da gani nace"
tsayar da cin abinci Usman yayi ya kalli ta yace "Momi lafiya?"
"babu ruwan ka kuma karka kuskura sa min baki a magana kaima inka kare ka tashi ka fice"
k'asa yayi da kansa shida Nura suna mamakin abunda yasa ran Momi ya É“ace haka,

tsaye Qasin yayi yana kallonta kamar ba dashi take maganar ba sai son yake yayi magana kuma ya kasa
ganin haka yasa Momi ta tashi ta bar mishi parlor,
Jinginawa yayi da ginin dake gurin ya dafe kai yana cizon baki ya daÉ—e a haka sannan shima ya juya ya fice,
Nura da Usman ma suna ganin ya fita suka tashi suma suka fice aka bar Mairo ita kaÉ—ai sai cin abincin ta take tana yan wake²,

    baifi 5 minutes da fitar su ba Siraj ya shigo fuskarsa babu yabo ba fallasa sallamar ma ciki² yayi ta Mairo ta amsa masa ta kaÉ—a kai "taf lallai ma kai wannan yaron sai yanzu kaga damar tashi har kowa ya gama breakfast? Kayi olo ma dan abincin ya k'are"
Murmushi ya É—an yi "aini ba abinci zan ci ba"
gyara zama tayi "saboda me?"
shiru ya É—anyi sannan yace "a zumi nakeyi"
taɓe baki tayi "thom kun zama ɗaya kai da Momi kenan"
"itama a zumin take ne?" ya tambaya saida ta girgiza kai sannan ta bashi amsa "a a bata dai ci abinci ba"
"miyasa?"
"Nima ban sani ba kila bata da lafiya dan tun jiya kuka take ko bachi bata yi ba"
da a sauri ya nufi upstairs jikinshi na rawa ya tura k'ofar É—akin Momi,
da sallama ya shiga ta amsa masa da muryar kuka "wa'alaikassalam"
kusa da ita ya zauna yana faÉ—in" Momi kuka kike yi ne?"
bata iya ce masa a'a tunda yaga hawaye a idonta kawai sai kawarda fuska,
Hannun ta ya rik'a "dan Allah Momi kibar kukan nan Maryam tace tun jiya take kukan nan"
hannu tasa ta share hawayen tana faÉ—in "dole inyi kuka Siraj jiya Qasin a gaban Hajiya ya aibanta Yarima É—an ta kwara É—aya É—an da tafi kowa sonsa ban taba ganin bacin ranta ba irin na na jiya wani abu bai taa haÉ—a ni da itaba sai jiya kuma nasan zata rika É—aukar na hana ma É—anta Maryam da nasan rikonta haka zai zamar min daban É—auko ta ba tun farko"
Ajiyar zuciya Siraj ya sauke yace "har gobe Momi bazan basa faÉ—a miki ba Yarima bai dace da Maryam ba dan ba mutumin kwarai bane taya za a É—auki karamar yarinya kamar Maryam a aura masa kada ki sake É“ata ranki akan wannan hukuncen da kika yi dan ni banga wata matsala ba"
Momi tace "akwai matsala Siraj dan yanzu ganin suke na hana Yarima auren Maryam na aura mata wani"
tashi yayi tsaye ya kalleta yace "Momi kina son Yarima sosai da badan wani abuba da nace kinfi sonshi sama da mu da muke yayanki"
Lumshe ido tayi ta sauke ajiyat zuciya shi kuma yasa hannayensa aljihu ya fice,

''' *** *** *** '''
duk inda yabi gaishe shi ake cikin girmamawa har ya isa parlor Hajiya zaune ya tararda ita tana cin apple wata baiwa na matsa mata kafafu Hajiya na ganinshi ta janye kafafun nata tayi mata alama data ta fice cikin sauri ta tashi ta gaida Yarima ta fice,
Karasowa yayi kusa da ita ya zauna ya É—auki apple É—in ya kai baki ganin bai yi mata magana ba yasa ta kalleshi yadda taga fuskarsa a É—aure tasan akwai wata a kasa saida ta É—anyi gyaran murya sannan tace "É“acin ran jiya ne ko kuma na yau dn nasan Mai martaba yayi maka magana?"
ba tare da ya kalleta ba yace "saboda mi Mai martaba zaisa min baki a neman aure?"
"saboda bata dace da kaiba haba Yusuf koda basu wulakanta kaba ai kaima kasan bai dace ka auri wannan yarinyar ba ga yayan manyan mutane masu aji masu kyau wasu m har sun nuna suna sonka amman ka kai kank gunda za a wulakanta ka karama da ba ayi auren ba dan Mai martaba ya nuna baya so kamar yadda nima bana goyon baya"
kallonta yayi yana murmushi yace "nima zuciya tace take so ba ni ba kuma aure sai anyi shi no matter what dan haka kuso abunda É—an ku yake so kawai"
fuskantar a haÉ—e ta kalleshi "saboda baka da zuciya ko shiyasa har yanzun kake son ta ina mamaki ka Yusuf kwata² ka chanja wai mi ka gani a jikin yarinyar nan ne.....?"
kamin ya bata amsa wayarsa tayi ringing ciro ta yayi ya danna picking ya kara a kunne,
banji mi akace masa ba murmushi kawai naga yayi yace "good job an samoshi kenan.........bani minti biyar"
da kallo Hajiya ta bishi har ya tashi tsaye sannan tace "waya kira ka a waya mi kake kokarin aikatawa?"
kallonta yayi fuskarsa É—auke da far'ah ya rika hannunta yace "babu komai Ummi na É—an ki ba zai aikata wani mummunan abu ba just trust him okey?"
bai jira cewarta ba ya sakarma hannun nata kiss ya fice yana murmushi.


*_©KHADEEJA CANDY_*
Post a Comment (0)