*♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*45*
Haka Momi ta share kwana da kwanaki bata kula Qasin iyakarta dashi gaisuwa babu hanyar da bai biba na ganin ta dawo normal amman abun yaci tura dole tasa ya hakura ya kyaleta,
Wata ranar Asabar Momi na zaune parlor tana tunane² Siraj ya shigo guri ya samu kusa da ita ya zauna kasan carpet cike da ladabi ya kalleta yace "Momi wai miyasa yasa ba zaki É—aga ma ya Qasin kafa ba Momi wadda fa kike abun nan danshi baima san kinayi ba dan me zaki rika fushi da É—anki akan É—an wata Momi"
Ajiyar zuciya Momi ta sauke irin nasu na manya sannan ta É—an gyara zamata tace "bana daga cikin iyayen da suke fushi da y'ay'ayensu dan fushi iyaye yana tare da fushi Allah ko kaÉ—an ni bana fushi da Qasin kawai dai inason nuna masa kuskuren daya aikata babbane gaba karya sake aikata shi kuma wani gefen ma bana ganin laifinsa laifin kaina nake gani dana É—auko Maryam riko har Yarima ya ganta ya nuna yana so kuma na hana shi ita wannan abun shine ya tsaya min a rai shiyasa yanxu na yanke shawarar ma yarda ita gurin Gwaggonta kusa da mijinta"
kallon rashin fahimta Siraj yayi mata "kina nufi ki ma yarda Maryam kauye kenan?"
"haka nake nufi kuma hakan shine kwanciyar hankali"
Amsar Da Momi ta bashi kenan a takaice
"amman Momi naga ai abunda na faru ya riga ya faru kuma kin riga kince yarinyar nan karatu zatayi mijinta yayi Na'am itama tana so Gwaggo ta amince dan me kuma yanzu zaki ce ki maida ta itama ai ba zata jidadi ba"
Motsa baki Momi tayi "ma yarda ita ya zama dole a gareni kodan suma na sama musu sukuni"
"ki sama musu sukuni su suwa?" Siraj ya tambaya
Momi saida ta nisa sannan tace "satin daya wuce Gwaggo ta kirani a wayar haruna tace mun wasu daga birni zunzo neman auren Maryam an faÉ—a musu tana da miji shine suka samu halilu sukace zasu bashi kuÉ—i mai yawa ya sake ta shi kuma ya k'i Aminta babu irin rarrashin da basu yi masa ba yak'i sun jera kwana da kwanaki suna zuwa har suka ce masa matukar bai rabu da itaba komai zai iya faruwa dashi"
keɓe baki Siraj yayi "ba kowa sai Yarima dan babu wadda zai aikata haka sai shi dan sheɗan kaɗa masa ganga yake yana rawa"
Momi tace "hakan yasa nake son maida ta kusa da mijin ta kar wani abun ya shiga kuma adawo ana ganin lafin juna"
"babu wani ganin laifi Momi kawai ki barta tayi karantunta shi kuma darasi yake son a koya masa"
kai Momi ta girgiza "a'a bana son wata fitina wacce na sha yanzu ta ishe ni kabar shi yayi duk abunda yake son aikatawa"
Da sauri ya kalleta fuskarsa da ayar tambaya "Momi wht are yhu tlkng abt abarshi ya kashe aure akan wani dalili na shi na banza?"
"abunda nayi ban kyauta masa ba Siraj na hana masa aurenta dan haka yanzu bazan hana shi rawar gaban hantsi ba na ganin ya kwatarwa zuciyarsa abunda take so"
wani kallo Siraj yayi mata kamar bai gane abunda ta faÉ—a ba can ya kawarsa kansa yana jinjina lamarin sannan ya sake kallonta yace "Momi yhu love Yarima a lot da ace ba ke kika haife ni ba da nace son da kike masa bana banza bane tunda banga wani abunda yake anfanarki dashi ba Amman ke kullum burinki ki faranta masa ko rantsuwa nayi ba zanyi kaffara ba kinfi mahaifiyarsa sonsa"
Sai a lokacin idanuwan Momi suka kawo kwallah magana ta soma yi cikin muryarsu ta manya "kai Da yayanka kun kasa fahimta ta akan Yarima da mahaifiyarsa Siraj yau inason faÉ—a maka wani abu da baka san da shiba dan ina ganin har yanzu baka wayi dangantakar dake tsakaninmu ba..."
lutse baki yayi ya tari numfashinta "na sani Momi bana nufin É“ata miki rai dan Allah karki zubar da hawayenki akan wannan maganar"
Momi ba tare da ta kalleshi ba tace "mu biyu kawai mahaifiyarmu ta haifa saida aka fara haihuwar Hajiya da shekara 6 sannan aka haife ni ina da shekara 15 mahaifiyarmu ta kwanta ciyon ajali a lokacin Hajiya tana gidan aure ni naje na kirata mukazo gaban gadon mahaifiyarmu muka zauna nan mahaifiyata ta rika hannuna tace nayi ma Hajiya biyayya na ɗauketa kamar uwa na guji ɓacin ranta duk kuma abunda zai sata farin ciki na tabbatar da na yi shi na sota kamar yadda nake son kaina sannan ta ɗauko hannun Hajiya ta ɗora saman hannuna tana faɗin ga kanwar ki nan ki riketa ki zamo mata uwa karkiyi mata abunda zai sata bakin ciki ki sota kamar yadda kike son kanki wannan itace wasiyar da mahaifiyarmu ta bar mana bayan rasuwarta Hajiya ta mayar dani gidan ta da zama wato gidan mahaifin Yarima tunda naje gidan bata taɓa koda hararata ba balle ta min tsawa bata taɓa ɓata min rai ba har ta aurardani ga mahaifinku lokaci ɗaya muka haihu da ita ita ta reni Qasin duk da irin son da take ma Yarima bai rufe mata ido ta nuna Qasin ba ɗanta bane karara take nunwa Yarima kiyayya ta karɓe abun hannunsa ta baiwa Qasin ko ta dake shi akan Qasin koda shine da gaskiyasa har kuka girma kuka kawo yanzu kuke ganin inayin abunda bai dace ba alhalin ni nasan abunda yake nan uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa bane koda mahaifiyarmu bata mana wannan wasiyar ba......"
da kuka ta karasa maganar ta lumshe ido alamar tunawa da bacin cikin baya
Lakas jikin Siraj yayi sanyi a hankali ya sunkuyarda kansa cike da tausayi
Sun daÉ—e a haka parlor yayi tsit kamar ba kowa Momi dai in bada sharar hawaye babu abunda take,
Ganin hakan yasa dole Qasin ya É—aga lalulen parlor ya shigo dan babu abunda ya tsana kamar zubar hawayen Momi.
*_©KHADEEJA CANDY_*