Mairo 47

*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*_JINJINAR BAN GIRMA A GAREKI RUFAIDA OMAR_*😘👍🏻

*NA YABA DA SOYAYYARKI MARYAM ABDULKADIR (MAMAN AFFAN)*😍

*WANNAN SHAFIN NAKI NE DR. ZULAIHAT ISA (AUNTY NA)*😘

*47*

"Assalamu alaikum Assalamu alaikum Assalamu alaikum"
Halilu ne yake sallamar tun daga kan Gwaggo har Mairo aka rasa mai amsa masa.
Mairo dai in banda harara babu abunda take masa.
"wa'alaikassalam" saida ya kusa k'arasowa sannan Gwaggo ta amsa masa can k'asan mak'oshinta.
jiki ba k'wari ya zauna saman tabarmar ganin marhabar da Mairo take masa da harara ga kuma yanayin yadda Gwaggo ta amsa masa sallamar duk sai yasashi jin ba daɗi.
haka ya danne abunda ke zuciyarsa ya kalli Mairo da far'ah
"Yan birni saukar yaushe ?"
"D'azu ɗazun nan Hajiya ta kawota har ma take tambayarka"
Gwaggo ce ta bashi amsar bayan ta nisa
murmushi yayi
"Ayyah aiko ban jidaɗin da suka wuce ban samu ganinsu ba dan naso ganin Siraj sosai"
"Ai ba dashi aka zo ba da Ya Qasin aka zo kuma basu daɗe ba suka wuce"
Wannan karon Mairo ce ta amsa masa.
"Amman dai lafiya suka kawoki yanzu ko anfasa karatun ne ?".
Gwaggo ta taɓe baki "Toh ban sani ba amman dai sun kawota ne wai kar a tauye maka hakki"
Murmushin jindaɗi yayi "Aiko Hajiya ta kyauta kuma tayi abunda ya dace. daman jiya Tsohon yake cewa ya kamata a dawo da ita gida abar maganar karatun nan."
"Toh gata nan an kawo sai ta maka maganin da zatayi maka haka kawai ka ɓata rayuwarka kana son ɓata mata nata rayuwar." kallon Gwaggo yayi fuskarsa na nuna ɓacin ran dake zuciyar "Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce haka.?"
Sake taɓe baki tayi a karo na biu "Eh mana toh in bashi ba miye na wani damuwa da a kawo ta alhalin ko ɗakin da zaka sakata baka ginaba gaka babu sana'ar yi barre aiki kai dai kamar ba namiji ba!"
a hankali ya sauke ajiyar zuciya "Gwaggo kada rashin aikina ya dame ki munyi magana da wani zanje neja zai nemin aiki kuma zai mayar dani makaranta yanzu haka ma na haɗa kuɗin mota nan da kwana biu zanje In'sha Allah"
cikin sanyayyiyar murya yake maganar cike da ladabi.
Gwaggo ta nisa "Toh Allah yasa ya kuma taimaka ai haka nake so jin"
Murmushin jindaɗi yayi ya amsa da 'amin' tare da tashi ya nufi k'ofar ɗakinsa.
daf da zai shiga Mairo ta tashi zaune ta kalleshi "Halilu zaka je dani ko ?"
juyowa yayi bakinsa ďauke da dariya
"A'a Mairo kinga nema zai kaini ba zama ba sai naga yadda abun zai kasance tukuna."
Gwaggo taja mata kunne "Wai mai yasa kike da shegen son yawo ne ?"
"Ni wallahi bana son zama a k'auyen nan."
cewar mairo tana wani yak'unar fuska kamar wacce taga wani abun k'azanta.
Murmushi. kawai halilu yayi ya shige ɗakinsa.
Gwaggo ma dariya tayi "Ai zama k'auye ya kamaki tun da nan kika tashi kuma nan kikayi aure. sai hak'uri"
ɓata fuska tayi ta sake komawa saman k'afafun Gwaggo kamar ta fasa kuka.

Washe gari k'iri k'iri Mairo tak'i ta ci dumame dak'er Gwaggo ta lallaɓata ta samu ta sha kunu da rana ma k'in cin abinci tayi haka ta wuni har dare wai ita ba zata ci tuwon dawa ba tuwon masara da Gwaggo ta tuk'a mata ma k'in cin tayi saida dare Halilu ya shigo mata da agashe mai tumatir da albasa.
da murna ta karɓa tayi zaman kirki taci tasha ruwa sannan ta kwanta.
Cikin kwana biu duk tabi ta chanja sai rama da take fama da ita na rashin cin abinci da kuma tunanin birni kullum cikin kuka. take da mafarkin ranar da Siraj zaizo yaje da ita,
Ranar wata laraba Gwaggo ta na zaune tsakar gida tana aiki Mairo ta fito daga cikin ɗaki ta zauna fuskarta a kunbure da a'lamar kuka tayi.
Kalllo ɗaya Gwaggo tayi mata ta ɗauke kai "Allah yayi miki saukin wannan halin rayuwa da kika saka kanki ciki Mairo wannan abu dame yayi kama daga zuwa birni shi kenan kin mayarda abu armun-azi'mun kin are kin yafe ke sai can ai toh k'ara da aka dawo dakw yanzu dan in kika kara jimawa k'ila koni bazaki so gani ba."
idonta ne suka k'ara cika da kwallah. da muryar kuka ta soma magana "Gwaggo nan fa babu daɗin zama kuma tunda na dawo babu halin na fita sai ace naje yawo Tsoho ya rik'a min faɗa ko k'awayene sun daina zuwa guna..."
Gwaggo ta rik'e baki "Oh ni yau kiji mani 'ya toh ba aurene dake yanzun ba yaya zamu saka miki ido kina yawo yanzu fa ba kamar da bane ke MATAR AURE ce yanzu"
fashewa tayi da kuka "har ga Allah ni bana son auren na dan kun mayardani k'ank'annu kuke min haka"
"Uhmmm. inma dan zuwanki birni ne yasa kike wannan abun gara tun wuri ki shafawa kanki lafiya ko babu komai dai kinga bason suke ki zauna a tare dasu ba."
cewar Gwaggo,
uffan Mairo bata sake cewa ba in banda kuka da ta shiga rusawa.
fitowa Halilu yayi daga cikin ɗakinsa ya nufo Gwaggo yana faɗin "Gwaggo ina ganin tafiya ta gobe ne in sha Allah"
wani irin faɗuwa gaban Mairo yayi zuciyar ta ta buga da k'arfi nan da nan hawayen dake mata zuba suka tsaya ta ɗaga kai tana kallon Halilu,
Gwaggo ta kalleshi "Gobe gobe Halilu ?"
"Eh kinsan nace miki ranar Alhamis za muje da naso ɗaga tafiyar toh wadanda zamuje tare ne suka k'i"
Gwaggo na dama garin dake gabanta tace "Shin wai yau wace ranace ni har Alhamis ɗin tazo ne ?"
Halilu yayi dariya "Eh mana Gwaggo gobe ne Alhamis fa ko kin manta yau Laraba kinsan shekanjiya ne matar Garba ha haihu yau kwana huɗu"
kai Gwaggo ta girgiza "Haka ne fa oh duniyar nan lokaci yana gudu dubi kaga haihuwar nan wai har an kwana huɗu Allah dai yasa mu cika da imani kwankinmu ne ke tafiya maganar nan yaushe muka yi ta amman wai har Alhamis ɗin tazo"
"Wallahi kuwa Gwaggo ai mai hankaline yasan wannan ga tsadar rayuwa saidai ace Alhamdulillahi"
yayi maganar yayin da yake k'ok'arin risinawa kusa da ita,
Gwaggo taja damun ta aje gefe ta sake kallon sa "Wai tafiyar nan dai babu wani abu ko nidai sai na rik'a ba daɗi karfa garin neman gira a rasa ido karka jefa kanka cikin wani halin daman dan neman abunyi, dama ace bakiyi nisa da muba ko nan kusa ai ka samu wani abun amman qce har neja"
Murmushi yayi "Babu komai Gwaggo sai alkhari kedai kiyi ta min addu'ah wannan abun da kikeji ba komai bane sai sabo in sha Allahu za ayi nasara."
Ajiyar zuciya ta sauke "Toh Allah yasa addu'ah ai kullum ciki yi muku ita nake Allah ya kaika lafiya ya tsare amman naso tafiyar nan ba yanzu ne da sai na karɓi a dashe na saina baka ka k'ara"
"Babu komai Gwaggo addu'ah kin ya fiye min komai inada yan kuɗin da zasu ishe ni kwana biu kuma kinga in naje ba zama zanyi ba aiki zamu rik'a yi"
"Toh Allah ya taimaka yasa ayi sa'ah ya tsare min kai ya raya ka ya cika maka burinka"
sosai ya jidaɗi addu'ah da Gwaggo tayi masa bayan ya amsa da 'amin' ya tashi tsaye yana faɗin "Bari na shiga gari na ɗanyi bankwana da wasu"
kai Gwaggo ta ɗaga masa "Toh aikan yafi Allah dai ya tsare."
tafiya ya somayi har yakai k'ofa Mairo ta kirashi
"Halilu..."
"Na'am"
juyowa yayi ya kalleta itama shi take kallo bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana. ganin hakan yasa shi tambaya ta "Minene Mairo ko wani abun kike son a siyo miki ne ?"
kai ta girgiza alamar a'a "Toh minene faɗi naji ?"
cika idonta sukayi da kwallah "Halilu dan Allah karkaje neja ɗin nan kaji ko kuma kaje dani"
"Saboda mi ?" Gwaggo ta tambaya "Nidai bana son yaje bana so kawai"
cikin muryar tausayi ta bata amsar, hawayen dake idonta suka soma gudana.
dawowa Halilu yayi ya risina daidai gun da take zauna ya kalleta cikin muryar lallashi ya soma magana "Kar dai ace tafiya tace ta saki kuka ai ba daɗewa zanyi ba zan dawo dole naje dake dan haka kibar k'ararda hawayenki kinji ?"
"A'a nidai bana so kawai kar kaje bana son kaje ka bari har wani lokacin"
wannan karon muryarta na rawa tayi maganar.
iskan dake bakinsa ya busar sai zuciyar ta soma masa ba daɗi "Haba Mairo karfafa min gwuiwa ya kamata kiyi fa kinga nan ina zauna babu wani abunda zanyi amman can zan samu aikin yi nayi kuɗi na gina miki gida mai a birni da zaki zauna na rika baki kwai da daɗi kina ci amman kinga inna zauna nan haka zamuyi ta zama babu wani cigaba yanzu fa dana dawo birni zamu koma ko baki so ?"
"Ina so. mana"
Murmushi yayi "Yauwa toh ki zake ranki ki rik'a min addu'ah kinji ki daina kuka ?"
share hawayen tayi ta ɗaga mishi kai "Toh na daina amman dai in kaje karka daɗe"
"Ai bazan daɗe ba zan dawo na ɗaukeki"
Gwaggo daga gun da take tayi dariya tace "Oh Mairo kodai ya saki a jaka ne ya tafi dake ?"
fashewa tayi da dariya "Haba Gwaggo sai kace wata yar tsuntsuwa sai dai in Tsoho za asaka aje dashi"
wannan karon har Halilu saidai yayi dariya.
Gwaggo tasha mur "Wai Mairo mi yasa kika raina Tsoho ne naga dai ba sa'an ki bane ai ?"
"Amman dai kakana ne ko sai abarni dashi shima ai haka yake min"
"Toh shi kenan aiko zamu saka k'afar waddo ɗaya dake"
kai kawai Halilu ya kaɗa ya tashi ya fice.



Post a Comment (0)