Mairo 48

*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com


*48*

Tunda Halilu ya dawo, sallar A'suba ya shiga kintsa sauran kayansa.
daf da zai gama Gwaggo ta shigo masa da kari "Halilu ana nan nata shirin ?"
juyowa yayi bayan ya aje jakarsa gefe. "Eh wallahi har kin tashi Gwaggo ?"
"Eh tunda nayi sallah na shiga haÉ—a maka abun kari naji kace da wuri zaka wuce."
kunun data aje gaban shi ya buÉ—e ya shiga motsawa "Toh ai kara tafiyar safen Gwaggo tun kinga garin nesa ne kara muje da wuri"
Ajiyar zuciya kawai Gwaggo ta sauke ta tsora masa ido.
biu da ludayi yayi ya aje Gwaggo ta kalleshi "Ba dai ka k'oshi ba ?"
"Gwaggo bazan iya sha da yawa ba ki cikina a É—aure yake wannan ma dan kar naje babu komai a ciki nane"
Gwaggo ta tura masa dumame "Toh kaci tuwon mana ai bakaje da yunwa ba dai"
"Bazan iya ci ba Gwaggo inna ji yunwa zan siye wani abun ko a hanya ne"
"Toh Allah ya sauwake ko ni haka nake in zanyi tafiya bana iya cin abincin kirki"
kuÉ—i dake É—aure a gefen zaninta ta ciro ta mika masa "Ga wannan jiya na aro gun FaÉ—ime ka É—an k'ara"
kamar bazai k'arɓa sai kuma yasa hannun ya karba yana godiya "Allah ya saka da Alheri amman dama baki wahalar da kanki ba Gwaggo na faɗa miki inada yan kuɗin da zasu ishe ni." "Babu komai Halilu in banyi maka ba wa zaiyi maka Allah dai ya raya mani kai ya tsare ya baka abunda kake buk'ata."
"Amin Gwaggo Mairo bata tashi bane ?"
saida yayi tambayar kunya ta zo masa da sauri ya sunkuyarda kansa.
murmushi Gwaggo tayi "Bata tashi ba daman bana son ta tashi dan in taga tafiyar ka zata iya fasa min kuka"
shima murmushi yayi "Mairo manya ana girma na cin k'asa Allah dai ya shirya"
kamin Gwaggo tace Amin sukaji an buga gida.
da sauri ya tashi ya fita, bayan kamar minti É—aya ya dawo ya É—auki jakar yana faÉ—in "Ga abokan tafiyar nan sun zo zamu wuce..."
ganin idonta sun cika da kwallah yashi risinawa ya kalleta "Haba Gwaggo kar kimin haka mana dan Allah karkiyi kuka bafa rabuwa mukayi ba tafiyace kuma in sha Allahu zan dawo"
sam Gwaggo kasa hak'uri tayi saida kukan nata ya fito fili,
nan shima nashi idon suka cika da kwallah amman bai yarda ya bari ta gani ba kasancewar shi namiji. tsit É—akin yayi in banda shashekar kukan Gwaggo babu abunda kake ji.
saida hawayen suka É—an tsaya mata sannan ta kalleshi da jajayen ido "Allah ya tsare ka Halilu ya kaika lafiya"
dak'er ya iya amsawa da Amin ya tashi ya nufi k'ofa nan ma ya daÉ—e tsaye sannan ya fice.
. Sai takwas da yan mintuna Mairo ta tashi da murjar ido ta fito É—akin ta É—auki buta ta shiga banÉ—aki., bayan ta fito ta nemi guri ta zauna zata fara alwala.
Gwaggo ta kalleta "Yau Mairo anyi ranar sallah."
"Wallahi Gwaggo jikin ne yayi min nauyi kuma duhu dubun nan da nake gani saina É—auka ko safiya bata waye bane."
Gwaggo ta É—an kalli gajimare "Eh da yake yau an tashi da hadari kuma yayi bak'i sosai ina ganin ruwa ake a wani garin kusa."
taɓe baki kawai tayi ta cigaba da alwala bayan ta k'are ta shiga ɗaki ta saka Hijab ta shinfiɗa ɗan kwali ta soma Sallar, tana k'arewa, ta fito ɗakin da sauri ta shiga ɗakin Halilu.
fitowa tayi kinit kinit da fuska kamar ta fasa kuka ta nufo Gwaggo,
tun kamin ta k'araso Gwaggo ta tare ta "Toh karki fara mani kukan nan naki ni ban iyawa"
"Miyasa baki tashe niba da zai tafi kuma kika barshi ya tafi"
da rawar murya tayi maganar alamar tana son yin kuka.
"Shine a yace karna tashe ki na kyaleki baya son kukan nan naki" aiko kamar jira take Gwaggo ta kai aya ta fara sana'ar ta ta "Ni wallahi Gwaggo sai na miki kukan tunda kika ki tashi na" abunda ta dinga faÉ—a kenan tana murjar kafafunta akasa kamar wata k'aramar yarinya,

*BIRNI.........*
Koda Momi ta sauko downstairs ta nufo dining room ta tararda Siraj zaune yana haÉ—a ma kansa tea.
"Kai kaÉ—aine a dining ?"
juyowa yayi ya kalle ta "Eh sun wuce makaranta tun dazu wai suna da lakca k'arfe takwas good morning Momi"
"Morning too yau kayi saurin tashi tunda A'suba fa na ganka parlor nan nama É—auka ko aikin ne naku ya taso."
ta faÉ—a yayinda take k'ok'arin zaunawa.
dariya yayi "Haba Momi aiki tunda asuba ?"
"Eh mana in an kawo patient irin wannan lokacin kuma ace duty É—inka ne ai dole kaje ba É—aga k'afa dole a tashi da wuri"
shafa kanshi yayi "Taf ai kan ba amin haka ko patient ne wasu likitocin saji dashi sai goma ko sha É—aya nake shiga office."
"Hmm. kaidai Allah ya kawarda É“acin rana ai inta kama dole kayi toh yanzu wai miya tashi ka tun da safe. ?"
"Wani mummannan mafarki nayi..."
Momi ta tsayarda zuba madarar da take. "Mummannan mafarki kuma har kasa gabana yayi dakan uku uku ?"
dariya yayi "Kai Momi kin cika tsoro bafa akanki nayi ba akan Abbah ba akan kowa na gidan nan ba."
"Toh akan wa faÉ—a min gaskiya Siraj ?"
"Momi ai ance in anyi mafarkin daba na k'warai ba ba'afaÉ—a"
"Toh miya rage a kariga ka faÉ—a."
saida ya É—an cije baki sannan yace "Mafarkin nayi wai Maryam ta Auri wani mutum..."
Ajiyar zuciya Momi ta sauke ta lumshe ido,
bayan ta buÉ—e ta É—anja tsaki "Mtsss Siraj ka iya tada hankalin bawa ni Wallahi na É—auka ko wani abun ne"
"Wani abun ne mana Momi kai Allah dai ya tsare."
kallon mamaki Momi tayi mashi "Ya tsare. mi abunda Allah ya kaddaro ai babu mahani in Allah ya rubuta saita Auri wani ai sai ta Aura"
tea dake gabansa ya kurɓa "Eh haka ne amman dai kada Allah ya kaddaro ta Auri wani bayan..."
sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa.
kai Momi ta girgiza "Allah yayi muku saukin wannan rayuwa kun É—auki kiyayyah kun É—orawa Yariman nan na san ai danshi ne kake wannan abun"
hannayensa ya É—aga sama "A'a Momi karfa ki lakamin laifi kedai kika amfato sweet son É—in nan naki baki ji a baki na ba."
Momi ta soma shan tea tana faÉ—in "Ai ko baka faÉ—a ba na san haka kake nufi."
Murmushi yayi ya tashi tare da cup É—in tea ya É—auki jaridar dake gefensa ya fice.

''' *** *** *** '''
KishingiÉ—e yake tsakar parlorshi sanye da wando pencil da riga yellow, idoshi a lumshe yana tsutsar minti yana mayarda numfa a hankali,
"Yes enter..."
shine abunda ya furta bayan mai bugun k'ofar ya dade tsaye.
wani wassgegen mutum ne naga ya kunnu kai cikin É—aki da gamammiyar fuska kamar an masa mutuwa.
nesa dashi ya tsaya yace "Oga nazo maka da Albishir mai daÉ—i"
saida ya kusan minti uku da yin maganar sannan ya amsa masa har lokacin idon shi a lumshe suke. "Wane irin Albishir kazo dashi ?"
cike da isa yayi mashi tambayar shi ko jiki na rawa ya bashi amsa,
"Halilu ya mutu..... "
_Halilu ya mutu.! Halilu ya mutu..!! Halilu ya mutu...!!!_
haka maganar ta rik'a yima Yarima yawo a kwakwalwa sai a lokacin ya buÉ—e ido ya kalli Mutumin "Nace maka duk yadda zakayi kayi na ganin ka raba tsakanin su amman banyi da kai ka kashe shi ba."
da sauri ya bashi amsa "Oga ba kashe shi nayi ba accident ya samu a hanyarsa ta zuwa Neja neman aiki" wani tsire baki Yarima yayi "Ya a'kayi kasan ya samu accident ?"
"Oga idun mu yana kansa fa tunda ka bamu aikin nan ko ina yarana nake sawa su kula dashi a motar da sukayi accident É—inma harda yaron mu"
Wani irin kyakkyawan murmushi ya shinfiÉ—e fuskar Yarima wadda na tabbatar har a zuciyarsa yake.
tashi yayi tsaye ya k'arasa kusa da mutumin ya dafashi fuskarsa É—auke da annashuwa "Kazo min da albishir mafi daÉ—i kuma goron mai tsokane jeki waje ka jirani amman ka tabbatar mutuwa yayi ba dogon suma ba."


*©KHADEEJA CANDY*


Post a Comment (0)