Mairo 49

*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*49*

Da gudu Qasin ya shigo part ɗin Momi kai tsaye upstairs ya nufa.
zaune ya tararda ita hawaye na mata zuba, jiki a sanyaye ya zauna "Momi yanzu Abbah ya kirani sai anyi rasuwa k'auye"
Kai ta daga masa "Eh Halilu ne Allah yayi masa cikawa..."
ta karasa maganar,
nan shima Qasin ya kawarda fuskarsa yace "Abbah yace na ɗaukeki muje kamin ya iso inya so sai yaje shida Siraj da Usman"
kai kawai ta iya ɗaga masa ya tashi ya fice.
Part ɗinta ya nufa a gaggauce ya shirya ya fito shida Mansura bayan ta shiga. mota ya shiga ya kira Momi suka kama hanya.

''' *** *** *** '''
Tunda Qasin ya doso unguwar soka soma hangen mutane,
ba karamin mamaki Qasin ya cika dashi ganin motocin Yarima.
yanayin parking ya kalli Momi "Momi ke kika faɗa masa anyi rasuwa ?"
Momi bata bashi amsa ba ta buɗe motar ta fice Mansura ta rufa mata baya.
_"inna illahi wa inna ilaihi raji'um_"
Shine abunda Gwaggo keta furtawa tana dafe da kai hawaye na mata zuba mutane sai hak'uri suke bata Mairo na ganin Momi ta nufe ta gudu tana kuka. rumgumeta Momi tayi suka faɗi zaune ko wanne su na kuka, ganin kukan da suke yasa Mansura ita ta soma kukan mutane dake shigowa suma auka fasa nasu aka sara mai bawa wani haku'uri,
haka gida ya kacame kowa sai yabon halinsa yake.,
guraren la'asar aka ɗauki gawarsa zuwa mak'abarta bayan anyi masa sallah.

Bayan an dawo mutane suka soma yima Gwaggo gaisuwa uffan bata iya cewa ba in banda zubar hawayen da take.
A lokacin su Abbah suka iso shida Siraj da Usman harda Nura. Ba karamin tashi hankalin Abbah yayi ba ganin yadda Gwaggo ta koma nan da nan shima hawayen suka soma masa zuba sai hak'uri yake ba Gwaggo dan yasan tafi kowa jin mutuwar,
"inba wadda ya saniba babu wadda zaice ba nice na haifi Halilu ba bai taɓa min musu ba bai taɓa kin mun biyayyah ba mutum ne da kowa ga yaba da halinsa duk abunda zai ɓata min rai yana gudunsa yana da burika dayawa aranshi na ya kautata min yayi rayuwar jindaɗi ashe Allah bai nufa ba aahe rayuwar yar kankanuwace ba mai tsoyo ba..." cikin kuka Gwaggo take wannan maganar a'na bata hak'uri.
_Gwaggo bata taɓa haihuwa ba hakan yasa lokacin da yayanta ya rasu ta ɗauko Halilu ta rikashi tun yana karami a hannunta ya tashi Mairo ma tunda aka haife aka kawo ata ita itace ta raine ta kasancewar ta tashi babu uba kuma mahaifiyarta gurin haihuwarta ta rasu_

Sai a lokacin Yarima ya shigo cikin gida da sunan gaisuwa har kasan tabarma ya zauna yana gaida Gwaggo "Sannun mu inna Allah ya jikan shi yayi masa rahama yasa ya huta."
duk suka amsa da Amin Abbah ya Kalleshi cike da jindaɗi abunda yayi "Allah yayi maka albarka Yarima ya biya ka"
"Babu komai Abbah ai yima kaine Hajiya ma tana nan zuwa gobe tace nayi muku gaisuwa kamin ta iso"
"Muna amsawa Allah ya kawota lafiya"
nan ya juyo ya kalli Qasin da fuskar da shi kadai zai iya fassara abunda ke rashi "Sannun mu Qasin Allah ya baku hak'uri..."
'Amin' ciki ciki Qasin ya amsa ya ɗauke kansa yana kallon k'ofa nan ya juyo kan Siraj yana yi mashi tashi gaisuwar.
Haka Siraj ya amsa gaisuwar yana jin kamar ya shak'o wuyanshi.
Hannu yasa Aljihu ya ciro kuɗin da zasu kai dubu ɗari biyar ya aje gaban Gwaggo yana faɗin "Ni zan wuce kuma za a shigo da abinci yanzu Allah ya baku hak'uri"
"Amin Yarima Allah yayi maka albarka ya taimake ka akan dukan k'uduri ka na Alheri.. "
Momi ce tayi mashi Addu'a idonta cike da kwallah,
Saida ya haɗe yawu sannan ya kalli Qasin "Ina Maryam ina son nayi mata gaisuwa ?"
haka Qasin yaji maganar kamar izgilanci uffan bai iya ce masa ba Siraj ne kawai ya iya cewa "Ai basai kayi mata ba tunda kayi mana ya wadatar..."
"A'a bari a kira masa ita yana da kyau ita ai yayi mata"
Momi ce ta tashi da sauri ta faɗan haka ta nufi ɗakin da Mairo take.
Daker Momi ta samu ta lallaɓata ta fito. da sauri Yarima ya karasa kusa da ita yana kallon fuskanta ya soma mata gaisuwar "Sannu Maryam Allah ya jikashi kinji Allah ya baki wani ya baki hak'uri..."
Kai kawai ta ɗaga mishi tana kuka, ya ɗan daɗe tsaye sannan yayi musu sallama ya fice.

*FEW HOURS LETTER..........*
Qasin ya tashi ya shiga ɗakin da Mairo take,
Zaune ya tararda ita rakuɓe gefe ɗaya tana shasshekar kuka guri ya samu nesa da ita ya zauna ya kafa mata ido.
Sai a lokacin ya lura da ramar da tayi wani irin tausayin ta ne ya mamaye masa k'ok'on zuciya _she's too young for that yarinyar nan tun tana k'arama ta tashi babu iyaye tayi rayuwar k'auye yanzu kuma mijin da aka aura miki ya rasu kai gaskiya kina cikin halin rayuwa Maryam_ a zuciyarsa yake wannan tunani yana ɗan motsa baki.
Can ya tashi ya k'arasa kusa da ita "Maryam..." a hankali ya kira sunanta.
ɗago kai tayi ta kalleshi da jajayen idonta "Kin ci abinci ?" ya tambaya
Kai ta girgiza masa alamar a'a "Toh miyasa ?" dak'er ta iya buɗe baki tace "Bana iya cine"
"Ai daurewa ake yi Maryam ke bakinsan komai na duniya ɗan hak'uri bane mi kike ao yanzu kici ?"
"Bana son komai bazan iya ciba"
"A'a ai zaki wuni haka ba tun ɗazun baki ci komai ba kuma yanzu ace ki kwanta haka faɗamin mi kike so ?"
Fashe masa tayi da kukan shagwaɓa "Nidai bana son komai kawai ka kyale ni"
"Bazan fa kyale kiba sai kin faɗa min abunda kike so kici ko kuma duk abunda na kawo miki ki ci"
"Qasin miye haka ne tace bata so ba zaka kyale taba"
Kamar daga sama yaji maganar Mansura dake tsaye bakin k'ofa. Juyowa yayi ya kalleta tare da jan tsaki "Mtss wai Mansura mi yake damunki ne ke ko ina sai kin nuna bak'in halinki ?"
"Babu wani bak'in hali sai gaskiya Yarinyar nan dai naga tak'aba take dan haka dole ne ka ɗaga mata k'afa"
Hannu ya ɗaga mata "Mansura yau yau fa akayi mutuwar nan ba jiya ba ko shekaran jiya dan haka kar k'wak'walwar ki ta yayo miki mummunan zato akaina kosan irin abunda kike yi dan ke ba yarinya bace"
Shiru tayi ta tsura masa ido dan tasan halinsa sarai zai iya yimata tatas in halin nashi ya motsa,
Kallon Mairo yayi "Ke mi kike son ki ci ?"
ganin faɗan da yayi ma Mansura kuma fuskarshi a haɗe yasa ta ɗan ji tsoro share hawayenta tayi murya k'asa k'asa tace "Shayi nake so"
kai ya ɗaga mata "Ok bari naje na nemo miki yanzu kinji ?"
ita kan ta ɗaga mishi tana kallon Mansura data wani mugun haɗe fuska,
hak Qasin ya tsara gefenta ya fice.

*©KHADEEJA CANDY*
Post a Comment (0)