Mairo 60

♡... MAIRO ...♡*

*BY*

     *_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*Vote me on Wattpad* @khadeeja_Candy

*60*

Daga Momi har Qasin tashi sukayi Suna kallonshi. nan Mairo ta shiga k'ok'arin kwace hannunta. Iya k'arfinshi yasa ya rik'e hannun gam. Ko motsin kirki ta gagara yi.
   Cikin wani irin zafin nama Qasin ya k'araso kusa dashi ya É—aga hannu zai mareshi. Da sauri Yarima yasa É—ayan hannunshi ya rik'e mashi hannu yana mishi wani kallo.
   “Kayi kaÉ—an kasa wulakantaccen hannunka a fuska ta"
  Damk'e hannu Qasin yayi da k'arfi kamar mai dambe ya kai mishi naushi dai-dai k'ahon zuciya.
  Zaro ido Momi tayi ta É—ora hannu aka “Qasin mi kake k'ok'arin aikatawa haka?"
  Baiyi wata-wata ba ya sake aika mishi wani bugun.
Ba shiri ya saki hannun Mairo ya faÉ—i durk'ushe dafe da zuciyar. Ture Qasin Momi tayi idonta cike da k'wallah “Wai baka da hankali ne Qasin so kake ka kashe shi fice ka bar parlor nan"
   Hannu Mairo ya fisga sukabar parlor tare.
         
Part É—in shi ya nuf har lokacin yana rik'e da hannunta.
    Bai sake ta ba sai da ya sata cikin É—akin shi sannan ya jefar da ita saman kujera ya zaro belt É—in shi ya hau dukanta.
     Mairo bata san zafin duka ba sai yau tunda Gwaggo bata taÉ“a sa mata hannu ba kuma bata bari kowa yasa mata.
   Ihu ta dinga yi tana kuka baji ba gani tun tana iya É—aga murya har muryata ta dakushe.
  Saida yayi mata dakan da shi kanshi ya gamsu ta daku sannan ya jefar da belt É—in yana faÉ—in “Daga yau duk kika kuskura kika sake bari wani namiji ya rik'a miki hannu sai na karya ki"
Yana kaiwa nan ya juya ya fice.

      Saida yayi kusan minti 30 da fita sannan ta samu ta rarrafa ta fito.
    Tana kawowa parlor Momi ta zube k'asa ta rushe da sabon kuka. Da sauri Momi ta k'arasa ta rik'o “Inna lillahi wainna ilaihi raji'un dukanki yayi Maryam?"
   Kai ta É—aga mata tana wani irin kuka. Dak'er Momi ta lallaÉ“ata tayi shiru sannan taja hannunta tana matsifa suka shiga É—akinta.
   Sai da Momi ta shiga ta haÉ—a mata ruwan É—umi sannan ta shigar da ita bathroom É—in ta gasa mata jiki. Bayan ta k'are ta sake haÉ—a mata wasu ruwan wankan ta fito.
     Mairo wanka take tana kuka har tayi ta gama. Koda ta fito ta tararda doguwar rigar atamfa aje saman gado. D'auka tayi ta saka ta hau tsakiyar gadon ta kwanta tana sauraren ciyonkai da ya kawo mata ziyara.

***
    Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shigo side É—in Momi k'asa-k'asa ta amsa mishi sallamar da yayi muryarta na É—auke da damuwa.
Kusa da ita ya zauna tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya,
    “Momi kiyi hak'uri Zuciyata ce ta rufe shiyasa"
Kallonshi Momi tayi “Amman kuma dan zuciyarka ta rufe saika aikata abinda in badan Allah ya gyara ba da zai iya kaimu ga dana sani? Daker Yarima yabar parlor, saboda mugun Bugun da kayi mishi duk kuma haka bai maka ba sai da kasa Maryam gaba ka dinga dukanta kamar an aiko ka"
      “Momi Yarima dai ko kashe shi nayi inada hujja tunda shi ya kawo kanshi har cikin gidan nan ya kuma É—aukar min mata ya fita da ita Maryam kuma inba duka nayi mata ba ba zata samu  natsuwa ba"
    Kai Momi ta girgiza “Ko kaÉ—an Qasin duka baya gyara sai dai ya É“ata faÉ—a ya kamata kayi mata ba duka ba bazan yarda ba,
   Ba kuma zansa muku ido ba kai ka daketa matar ka ta daketa ba jaka bace dan haka karka sake sa mata hannu"
    Bak'ar ledar dake gefen hannun shi ya mik'a mata yana faÉ—in “Naji Momi ayi hak'uri bazan sake ba ga wannan maganin a bata tasha"
  Saida Momi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta k'arÉ“i ledar tana faÉ—in “Ka turo min Mansura zanyi magana da ita"
    “Bata nan Momi nima koda na dawo ban tararda itaba daman da zan fita naga tana haÉ—a kayan ta"
    “Fushi tayi kenan akan wani dalili?"
  KafaÉ—unsa ya É—aga “Oho mata nidai bazan je bikonta yanzun ba tunda bani nace taje ba kuma ba wani abin akayi mata ba"
     TaÉ“e baki Momi tayi “Toh Allah ya kyauta"
Saida ya amsa da “Amin" sannan ya tashi ya nufi dining.
   Momi kuma ta nufi É—akinta.

        Zaune Momi ta tararda Mairo tana cin kankanar dake gabanta da É—ai-É—ai. Ruwan goran dake gabanta Momi ta É—auka ta k'ara zubawa a kofi sannan ta kankare maganin ta mik'a mata.
   “K'arÉ“i kisha jikinki zai É—anyi sauki kamin gobe"
   Ba musu ta karÉ“a ta sha. ta cigaba da cin kankanar.
   A hankali Momi ta shafa kanta “Maryam dan Allah ki rik'a jin magana kinji in nace kiyi abu ki rik'ayi ki É—inga karatun ta natsu
Kinga har makaranta nayi maganar zan saki amman sai naga natsuwarki tukuna"
   Da sauri ta kalli Momi “Na daina Momi ina son makarantan ina ne? Bazan sake ba"
   Murmushi Momi tayi “Toh sai dai naga natsuwarki tukuna dan karatu natsuwa yake so balle ba subject É—aya za'ayi muku ba kinga za'a koya Miki yadda zaki iya saka tufafi, da tafiya, da iya magana, da dafa abinci, da zaman gidan Aure, da rubuta da karantawa,
   Har sana o'i duk ciki za'a koya muku kuma kuÉ—i da yawa ake kashe dan haka nafi son sai kin natsu dan bana son kuÉ—ina suje a banza"
    Shiru Mairo tayi kamar mai tunani.
   Momi ta cigaba
       “Makarantar ba nisa nan ne gurin Abdullahi Fodio Road sunan makarantar gyara da kanki nima a radio naji ta na É—auki number malamar na kirata mukayi magana kuma Fitar da nayi É—azun gurin gaisuwa ma saida na biya naga makarantar,
  Dan Allah ki natsu kinji ki daina duk wani abu da kikasan baya da kyau"
   Kai kawai ta É—aga mata taja fillo ta kwanta Momi taja zane ta rufe mata jiki tana faÉ—in “Ina tafar dai kinyi sallar I'sha ko?"
  Nan ma kai ta É—aga tasa hannu a baki.

Washe gari Mairo a É—aki tayi breakfast su Momi ne kawai sukayi a dining room.
   Nan na Momi take tabartawa Qasin maganar makarantar. Bai yi unk'urin hana taba duk da wani É“angare na zuciyarshi baya so fatan alheri kawai yayi mata ya tashi ya fice.

    Wasan É“oya Mairo ta dinga yi da Qasin sam bata yarda ya ganta duk gun da tasan zai iya ganin ta daina zama.
Sai da Momi tayi mta faÉ—a sannan gaisuwa ta dinga shiga tsakanin su kuma daga gaisuwar bata wuce ba data gaisheshi ya amsa zata tashi ta bashi guri,
    Hakan kuma sai ya soma damuwar Qasin ganin bata sakewa dashi.

   Saida Momi ta tabbatar da taji sauki sosai sannan ta É—auke ta da kanta ta kaita makaranta akayi mata komai da ake buk'ata. Daman suna da school bus ga mai buk'ata. KuÉ—in bus É—in Momi ta biya wadda za'a rik'a zuwa É—aukarta kullum da k'arfe 10am a dawo da ita 5pm.
     Maida hankali tayi sosai gurin karatun gashi Momi kullum cikin jaddadamata take kar tasa tayi hasarar kuÉ—inta
    Wata irin natsuwa ce ta sauko mata tunda ta fara zuwa makarantar kwata-kwata ta cire wasa gefe ta aje ta tattara hankalinta gurin É—aya ta kama karantunta
   
       A makarantar darussa aka dingayi musu kala-kala tun Mairo na ganin abinda kamar lalata tarbiyane yana bata haushi har ta daina sannu-sannu abin ya fara shiga ranta.

*****
      Ranar wata Jumma'a da misalin karfe goma sha É—aya na dare Qasin ya shigo parlor Momi.
    Mairo na ganin shi tayi saurin tashi daman ita ka É—ai ce parlor ta gaishe shi bayan ya amsa ta aje remote É—in dae hannunta ta juya da niyar tafiya.
   Da sauri ya riko hannunta “Ina zaki Maryam?"
   Ba tare data juyo ba ta amsa mishi “D'aki kwantawa zanyi"
     “Baki tashi yin bachi ba sai da kika ganin wai miyasa kike wahalar da nine Maryam bayan kuma kin kore min mata"
   Sai a lokacin ta kalleshi “Nikan ban korar maka mata ba ita dai taga dama tayi tafiyar ta"
   “Amman dai ai saboda ke ta tafi ko?"
  “Amman kuma ni bance ta tafi ba ganin damarta ne"
    Wani dogon numfashi yaja “Fine tunda kin iya jayayya"
   B'ata fuska ta É—anyi “Ni ba jayayya nake ba ai jayayya ba kyau kawai ina faÉ—an gaskiya ne"
    TaÉ“e baki yayi yaja hannunta. Saida suka kai bakin k'ofa sannan ta fisge hannun ganin zai fita da ita “Ina zamu?"
   “Part É—ina mana"
“Na maka mi?"
“In mukaje zaki gani"
Yana sake rik'a hanunta ta fisge.
  D'aure fuska yayi “Kinsan bana son musu ko ba dai canye ki zanyi ba ba kuma dukanki zanyi"
  Shiru tayi ta É—anyi k'asa da kanta.
Bai bari ta tsaya tunani ba ya sake jan hanunnata a karo na uku suka nufi Part É—in.
   
       Sama  gadon shi ya zaunar da ita.
Ita kuma gaban sai faÉ—uwa yake bedside drawer ya buÉ—e ya É—auko wani dan karamin box Red color ya ya kalleta yace “Rumtse idonki"
   “Kamin mi?"
“Ai dai bazan cutar dake ba ko Please close your eyes"
   Rumtse idon tayi gam tana haÉ—iyar yawu.
Wani daddaÉ—an K'anshi ne ya daki hancinta hakan yasa ta buÉ—e idon a hankali.
    Arba tayi da wata kyakkyawar sark'ar gold “Yaya kamar zinari na wanene?"
  Ta tambaya idonta a zare zuciyar na bugawa da sauri.
   “Gold ne ba kama bace kuma ke na siya ma ko baki so"
   Da sauri tasa hannu biu ta karÉ“a ta kuma durkusa k'asa “Inaso yaya na gode sosai Allah ya bika Jazakallahu khar"
   Murmushi yayi ya É—an tsosa bakinshi “Ur welcome dear" Ya tado da ita yasa bakinshi cikin nata.
   Batayi k'ok'arin hana shiba har saida ya gaji dan kanshi ya zare bakin daga nata.
Tashi tayi da sauri “Bari naje na nuna ma Momi"
  Kunkurumta ya rik'e “A'a Momi yanzu ai tayi bachi kuma kinsan bata son a tashe ta"
    Kai ta É—aga mishi tana murmushi mai fitar da sauti har cikin zuciyar ta take jindaÉ—in.
    Laptop É—in shi ya janyo “Zauna na nuna miki wani abu" kusa dashi ta zauna tana ciki da jindaÉ—i.
    Kunna laptop É—in yayi ya shiga nuna mata wasu pictures É—in da bata san lokacin ya É—auke suba.
       Dariya ta dingayi ganin wasu bachi ma take “Lahhh Yaya yaushe ka É—auka?”
   “Kina bachi na É—auka ba kece kike tsayawa kallo a parlor ba"
     Murmushi tayi ta k'asa da kanta kamar wace taji kunya.
    Nan ya shiga nuna mata nashi hotunan da yayi a k'asashe waje. Ganin ta fara jin bachi yasa ya janyota ya kwantar da ita saman jikinshi.
    Aiko nan da nan bachi ya buget. Qasin kamar mai jira ya rufe laptop É—in, bai ko bari bachi nata ya nina sosai ba, ya kwantar da ita kan gadon ya rabata da rigar jikinta ya shiga shafa ta yana aika mata kiss ta ko'ina.
   Wasa yayi da ita sosai sai da yaji ya gamsu sannan ya tashi a wahale ya shiga bathroom. Wanka yayi ya fito ya saka kayan bachi sannan ya nufo ta ya mayar mata da rigar,
   Itakan sai bachi take abinda bata masan yayi ba. É—aukar ta yayi kamar baby tare da sark'ar ya kawota part É—in Momi ya kwantar saman doguwar kujera ya aje mata sak'ar aje.
      Ya daÉ—e tsaye yana kallonta sannan manna mata kiss a goshi, ya kashe wutar parlor tare da Tv yaja mata k'ofa.

***
   Asubar farin Momi ta tashi ta daman haka take mata kullum saboda zuwa makaranta tunda har Asabar da Lahadi zuwa suke basu da ranar hutu.
    Cikin magagin bachi ta motsa tana faÉ—in “Yaya duk sunyi kyau"
   Momi ta jijjigata da k'arfi “Ke tashi kiyi wanka kiyi sallah wane yaya kuma?"
    Muk'a ta shiga k'ok'arin yi sannan ta tashi, sark'ar dake gefenta ta faÉ—o. Bata kula ba ta wuce É—aki tana murza ido da mamakin ganinta parlor Momi ita da bachi ya É—auke a part É—in Qasin.
   D'aukar sak'ar Momi tayi ta rufa mata baya bayan ta k'are mata kallo,  Sai da tayi sallah ta shirya sannan Momi ta tambayeta ina ta samo sark'a.
   Dariya tayi “Ashe da gaske ne ni na É—auka duk mafarki nake Yaya ya bani jiya da dare"
    Momi tayi murmushi “Aiko ya kyauta tunda daman bakida sak'ar zinari kuma ya siya miki mai tsada ina fatar dai kin mashi godiya dan godiya tana É—aya daga cikin abin da take saka Namiji jindaÉ—i idan yayi miki kyauta koda kusa kyautar bata kai ta kawo ba"
        Kular abincinta ta É—auka tana faÉ—in “Nayi mishi Momi bari naje ga motar makarantar mu can ta iso"
    “Toh Allah ya tsare ya kiyaye"
    “Amin Momi sai na dawo"
    Kai Momi ta daga mata tana murmushi, iya natsuwa yanzu kan tasan Mairo ta samu saidai wayou ne ba tada tabbaci ko tayi amman da tasan ko minene dai sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daÉ—e ba'aje ba.

'''**'''
   
Bayan Sallar Azahar Qasin ya shigo part É—in Momi, sun É—an daÉ—e suna fira anan ne take mashi zance sark'ar daya ba Maryam tana godiya.
     Dariya yayi “Haba Momi dan naba Maryam sark'a sai kuma kimin godiya?"
    “Eh mana ai idan kayima Maryam abu kamar ni kayima tunda Maryam yata ce"
     “Amman dai Momi bata ce miki wani abuba ko?"
   “Kamar na mi kasan ai yanzu ta rage yawan zubar nan wani abun kace tace ne?"
  Kai ya girgiza “A'a"

     “Wai Qasin ya maganar tarewarku ne?" Yana unk'urin tashi tayi mishi maganar hakan yasa ya koma ya zauna yana faÉ—in “Momi toh ai ke nake jira"
    Momi tace “Jiya Abbah ka yayi maganar daya kirani a waya har nake ce mishi akwai kayan da ba'ahada ba yace zai turo kuÉ—i ayi komai,
   K'auye ma ance tambaya kawai suke Gwaggo ku sai fama  matsifa take"
     “Nima dai Momi shi nagani yanzu dai babu wani abinda ake jira"
   “Idan ya turo kuÉ—in zan siya mata duk abunda ake bukata sai asa ranar tarewar taku"
   Murmushi yayi “Hakan yayi Momi Allah ya taimaka"
   “Amin amman dai kasan dole ne kaje bikon Mansura ko da baka tare daga kai sai ita ba ka kyale ta can"
   “Momi ai Mansura bata gari"
   “Bata gari kuma?" Momi ta tambaya.
   “Eh wai taje raka yayarta a indiya duba lafiya"
   “Da gaske?"
“Allah kuwa nima a bakin Sadiq naji kinsan yana Auren k'anwarta kuma dana kira wayar yak'i shiga"
   “Amman da izinin waye taje kai kasan da tafiyar ne?"
  “A'a sai bayan ma taje ne nake ji"
  Momi ta rik'e baki “Amman dai gaskiya daga ita har iyayenta basa da tunani Allah ya kyauta"
    “Amin ai sai ta gane kuskurenta bari naje nayi sallah naji kiran La'asar"
   Maganar yake yana kallon agogon hannun shi, Momi tace “Nima ai bari na tashi naje nayi sallar"
   Tashi yayi ya fice, ya bar Momi tana mamakin hali irin na Mansura.

'''** ** ** **'''
Da murmushi Momi ta sauko downstairs tana kallon kujerar da Yarima yake zaune,
   “Masha Allah Yarima har an iso?"
   Ba tare daya kalleta yace “Eh miyasa kike nema na?"
   Ruwa Momi ta É—auko mishi da cup ta dire mishi sannan ta zauna a É—ayan kujerar tana faÉ—in “Ya gida ya kowa da kowa"
    Ya daÉ—e yana kallon zoben hannun shi sannan ya amsa mata “Lafiya kalau"
   Momi tayi gyaran murya cikin fuskar manya ta soma magana “Wata alfarma nake nema a gurinka Yarima"
   Sai a lokacin ya kalleta “Allah yasa zan iya"
    “Zaka iya dan bata gagareka ba kuma kana da ikon aiwatarda ita"
    Shiru yayi yana murza yatsunshi, yasan Momi da wayo kuma gashi she's look so serious akan ko minene.
    Sai da ya busar da iskar bakinshi ya É—ora k'afarshi É—aya saman É—aya sannan ya kalleta kamar mai karantar abu a fukarta.


*© KHADEEJA CANDY*
Post a Comment (0)