HANYOYIN DA ZA'A BI A KARYA SIHIRI A ƘARƘASHIN KOYARWAR ADDININ MUSULUNCI DA SUNNAH


*HANYOYIN DA ZA'ABI DOMIN KARYA SIHIRI AKARKASHIN KOYAR WA TA ADDININ MUSULUNCI DA SUNNA TA ANNABI* 

Sihiri raba kauna, ko na raba mata da miji (Tafreeq),
Sihiril junun (hauka),
Sihiri na hana Aure mace, ko namiji.
Sihiri wanda yake haukatarwa (Junun) ko gamo.
Ko sihiril mahabba (Soyayya) wanda mata suke yi ma mazaje domin sukara sansu, ko su sosu. 

Ko sihir na maita, irin wanda ake cewa ai mayene yakamata, ko yakama shi.

Da Kuma shafar jinnu kowanne irin shafar jinnu ne, da yanayoyin dasuke haifarwa daban daban ga al'umma.

Da dai sauran kalolin Sihiri mabam bamta, da Kuma Yana yoyi daban daban. 
Duba littafin "Assarimul Battar na Wahid Abdus-Salam Bali" babin da ke magana akan Sihiri da karkasuwan sa.

Dafarko, akwai Ganyen Magarya (Assidir), za'a kwankwatsa shi ajikin duwasu guda biyu, sai a sanya su ackin ruwa mai tsafta a karanta ayoyin Ruqya baki daya... Sai ayi wanka da ruwan a inda babu najasa, kamar bayi ko inda ake fitsari.. 

Hanya ta gaba; Za'a samu ruwa mai tsafta, sai a yanka albasa acikinsa, asanya kawwa da gishiri, sai akaranta ayoyin Ruqya acikinsa.. Sai akamfaci ruwan da hannu, akuma tauna albasan dake cikin ruwan, sau uku. Haka za'a cigaba da aikata wa

Hanya ta gaba; za'a sami Tazargaje da Gishiri, sai asanya su acikin ruwa, akaranta ayoyin Ruqya acikinsa, za ayi wanka da shi, kuma za'a dibi daidai yanda zai isa mutum sha, sai asha bayan anyi wankan. Amma kada ayi a bayi ko inda akwai najasa.

Wadannan Hanyoyi sukan yi ta'asiri ne cikin yardar Allah, idan yaso
Kuma Ya amince.
Amma babu abinda yake bada kariya, da Kuma
karya Sihiri, face yawaita azkar, da yawaita
adu'ah. Wannan shine abinda yake bada kariya,
da Kuma saurin lalata Sihiri, domin ita adu'ah, kamar Takobi ne mai kaifi wanda take yanke ko sare abu kai tsaye.
Don haka kowanne nau'in Sihiri, da
Kuma nau'ikan ciwuka masu wuyar sha'ani to
yakamata murika hadawa da
adu'ah, musamman samun ruwan zam zam
Ko ruwan Sama (Manzon Allah S.A.W, yace acikin wani hadisi nashi; "Ruwan zamzam yana aiki da duk niyyan daka sha domin sa". Shikuma ruwan Sama, Allah Ta'ala yana cewa acikin littafinsa Mai Tsarki; " Muna Saukar daga sama ruwa mai tsarki." Duk abida Allah yasaukar mai tsarki daga gare shi, to yana tsarkake dukkan cuta ko datti akoma ina ne.
Asshafi yabamu ikon dace wa. 
والله تعالى أعلم.
Dan uwanku a Musulunci
Ahmad Muhammad Nata'ala
(Abu Fu'ad)
CEO: Daru As'habun- Nabiy Islamic chemist Kaduna
08069823502, 08075049989, 08083335561.

1 Comments

Post a Comment