*♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*Vote me on Wattpad* @khadeeja_Candy
*_Wannan shafin naku ne members of KHADEEJA CANDY NOVELS. Love You All_*😘
*64*
Da sauri Momi ta kamata wani irin rik'o Mairo tayi ma Momi da k'arfi tana wasu zafafan hawaye “Momi ya rasu ko? Yaya ya rasu?"
“Ba rasuwa yayi accident ya samu a hanyar shi ta dawowa"
Usman ne ya bata amsa dan Momi in banda kuka babu abinda take.
Kai ta girgiza “A'a nasani É“oye min ne kuke ya rasu na shiga uku na bani na lalace"
Bakinta Momi ta tushe tana girgiza mata kai,
Sun dade a haka kowane su sai kuka yake Usman ne yayi k'arfin halin yace “Momi kuka bayayi addu'a zakiyi bari naje Asibitin na gani"
Momi na k'ok'arin tashi Mairo ta rigata “Zan bika Usman"
“A'a Maryam ki zauna gida har na dawo" Momi ce take maganar cikin kuka,
“A'a Momi dan Allah ki barni naje koda gawarshi ce na gani babu wani abinda zaku É“oye min na riga naji komai dan Allah Momi karki hana ni"
Shiru Momi tayi kamar mai tunani sannan ta nufi upstairs ta É—auko hijab É—inta dana Mairo ta fito. Momi da kanta tasa mata hijab É—in sannan ta sama kanta suka fice.
Suna isa Asibitin suka nufi gurin da wata Nurse ta nuna musu, tsaye sukayi bakin k'ofar cirko-cirko kowanne fuskarsa da hawaye in banda Usman da yake k'ok'arin danne kuka,
Likitoci uku ne akan shi suna aiki bashi taimakon gaggawa. Sunyi awa uku a É—akin suna abu É—aya dak'er suka sami numfashinshi ya tsaya dai-dai yadda ake buk'ata, sannan suka cigaba da duba sassan jikinshi, Ko a hakan ma sun daÉ—e sannan suka fito.
Da sauri Momi ta tare su “Dr yana da rai yuwa?"
Ido Dr ya sakar mata sannan ya kalli Usman ya sake kallonta ba tare da yayi magana ba. Momi cikin kuka tace “Dr ka faÉ—a mana kawai ni uwar shi ce wannan k'anen shine wacan kuma matarshi ka faÉ—a mana kawai"
Ajiyar zuciya ya sauke yace “Mama ki kwantar da hankalinki bai mutu ba ya daiji mummunan rauni ne babu kariya aciki amman dai awazonshi sun samu matsala wadda ya haddasa murdewar jiyojinshi"
Kuka Mairo tasa “Dr kawai kace mana ya mutu"
Nan ya kalleta “Bai mutu ba nan da wasu awanin zai farka har magana zaku iya yi dashi amman ba zai iya tashi ba ko cin abinci ya haÉ—e har sai an mishi aiki"
Usman ya faÉ—i zaune dafe da kai yana “Inna lillahi wainna ilaihi raji'un"
Momi ma durkuashewa tayi tana kuka, Mairo kan hawayen tsaya mata sukayi k'ofar É—akin kawai take kallo,
_ni kuma na kasa ganewa shin farincikin ance yana raye ne ya hana mata kuka ko kuwa dan ance ya samu matsala ne bakin cikin ya hanata kuka_.?
A hankalin ta jingina jikinta jikin ginar dake bayanta ta sulale k'asa zaune ta rafka tagumi,
Daker Usman ya lallaɓa Momi ta tashi daga inda take ta zauna saman kujera,
Nan ya zauna kusa da ita yana bata hak'uri.
Kiran sallar I'sha ice tasa kowanne su ya tuna da bai yi magariba. Da sauri Usman ya tashi “Momi bari naje nayi Sallah"
Kiran shi tayi ya juyo tace ya bata wayarshi ba musu ya mik'a mata ya fice,
Wata number tasa ana É—auka ta fda mata wasu abubuwa da za'a dauko mata. Bayan ta ashe wayar ta kalli Mairo tace “Zaki wani abu?"
Kallonta kawai Mairo tayi ta kauda kai ba tare data bata amsa ba,
Zirga-zirga yan'uwan da abokin arziki da suke kusa suka rik'ayi Asibitin duk da likita bai ba kowa damar shiga ba, sai dai su yima Momi da Mairo sannu su tafi.
Guraren 3 da rabi likitan ya sake shiga É—akin bayan wasu yan mintuna ya fito ya kora Usman dake zaune saman kujera a hankali dan a zaton shi su Momi sunyi bachi ganin duk sun zaburo yasa ya É—aga musu hannu “No kuyi zamanku shi kawai nake buk'atar yazo"
Da sauri Usman ya tashi ya nufe shi. Shi kuma ya k'arasa buÉ—e mishi kofar suka shiga tare.
Maida k'ofar Dr yayi ya rufe sannan ya kalli Usman yace “Ya farka baya buk'atar hayaniya shiyasa na kiraka kai ka É—ai dan nasan su zasu iya sa mishi kuka har wani abu ya faru"
Usman ya rike shi “Da gaske Dr"
“Gashi can zaka iya zuwa ka ganshi sai dai ba zai iya magana ba sai nan da awa biu"
Cikin sauri ya k'arasa gaban dagon yana kallon Qasin shima shi yake kallo kowanne idonshi cike da hawaye.
A hankalin Usman ya kira sunanshi cikin muryar kuka “Yaya" nan Dr ya tari numfashi shi “Na fada maka baya son hayaniya ciyinshi zai iya karuwa idan ka tada mishi hankali dn haka ina son ka zauna dashi ne kawai har lokacin da zaiyi magana kar kuma ka barsu su shiga har sai na bada izini"
Kai kawai Usman ya É—aga mushi yaja kujera ya zauna,
Shi kuma Dr ya juya ya fice.
Momi na ganin ya fito ta tareshi “Dr ko ya mutu ne?"
Murmushi ya É—anyi “A'a bai mutu ba É—anki fa shida wata matsala idan ba wannan matsalar dana faÉ—a miki ba"
“Toh yanzu Dr babu wani abu da zaku iyaye ku shawo kan wannan matsalar?"
"Za'a iya mana za'a iya yi mishi aiki sai dai aikin da hatsari sosai kuma Dr É—aya ne ya k'ware sosai akan wannan matsalar duk Nijeriya shine Dr Siraj kuma yanzu an mayar da shi Abuja da aiki sai idan transfer za'ayi muku kuje can Abuja ko kuma na ku fitar dashi waje gaba É—aya gun da k'wararrun suka da yawa dan a ganina fitar dashi wajen yafi"
Rufe baki Momi tayi hawaye suka zubo mata, hak'uri Dr ya bata sannan yasa kai ya fice.
***
Sai da awa biyu ta cika cif sannan Qasin ya lumshe ido ya haÉ—eye yawu har lokacin Usman kallonshi yake yana hawaye,
A wahale ya soma magana “Ina Momi"
B'ari jikin Usman ya shigayi cikin rawar murya ya bashi amsa, “Tana waje Yaya ya jikin naka?"
“Maryam tayi kuka ko?"
“A'a batayi ba"
“Karkamin karya Usman"
“Tayi yaya ita da Momi duk sunyi"
Har lokacin idonshi a rufe yake yana maganar duk da turo k'ofar da Momi tayi ta shigo baisa ya buÉ—e ido ba sai hawaye kawai suke mashi zuba,
Cikin muryar kuka Momi ta kira sunan shi “Qasin... "
Ya dade kamin yayi magana “Momi kibar kukan nan bana son kina kukan nan koda na mutu"
“Bazan iya ba Qasin bazan iya juye ganin halin da kake ciki ba banyi kuka ba kaima kanka ai kukan kake"
A hankalin ya buÉ—e ido ya kalleta “Momi ina kukane saboda ni kadai nasan abinda nake ji sannan ina tunanin yadda rayuwarku zata kasan idan bani"
Cikin kuka Momi tace “Ba zaka mutu ka bar muba Qasin kada Allah ya nuna min san wannan ranar ina raye"
“Ina Mansura ina Maryam?"
“Mansura tana can kwance tun da labarin ya sameta ta faÉ—i ana mata k'arin ruwa Maryam kuma tana nan waje zaune"
Usman ne ya bashi amsa
Ya É—an daÉ—e kamin yace “Kira min ita" da sauri Momi ta juya sai da Usman yayi kamar ya dakatar da ita akan abinda Dr yace sai kuma yaji ba zai iya ba,
Da sauri-sauri gudu-gudu Mairo ta shigo É—akin ta k'araso kusa da gadon shi “Sannu Yaya sannu" Abinda ta ringa furtawa kenan tana wani yawo da ido kamar firgitacciya.
Cikinta ya k'urawa ido sannan ya kalleta ya sakar mata murmushin k'arfin hali tare da kiran sunanta “Maryam"
Da sauri ta amsa "Na'am Yaya Allah ya baka sauki tashi kafaɗarka" Hannu takai tana taɓa shi,
“Amin amman dan Allah kubar kukan bana son kuna min kuka koda na mutu"
Kai ta girgiza “A'a bazaka mutu ba Yaya baza mutu ba idan ka mutu nima mutuwar zanyi"
“Ba zaki mutu ba nine dai zan mutu ke zaki rayune keda abinda kika haifa cikin jindaÉ—i"
"Taya kake tunanin zamu yi rayuwar jindaÉ—i nida abinda na haifa idan baka raye kunci ne kawai zai mamaye mu dan Allah ka dai na wannan maganar bazaka mutu ba"
“Mutuwa wajibi ce Maryam dole ne sai mun mutu shiyasa ake son a rik'a tuna ta a kowane lokaci"
Rushewa Mairo tayi da kuka mai k'arfi ta rike gadon da yake kwance. Hakan ya haddasa shigowar likitocin da sauri.
FaÉ—a sosai É—ayan likitan yayi ma Usman sannan duk suka sawo su waje,
Kuka sosai Mairo keyi wadda har saida ya haddasa mata ciyo a kasan mararta,
***
Ana sauke Sallar A'suba Siraj ya diro cikin Asibitin, Momi na ganin shi ta tsaye da sauri tana kallon shi har ya iso. Fuskarshi cike da tashin hankali yace “Momi ya jikin nashi?"
“Yana ciki bazan ce maka ba sauki ba tunda yana magana amman yana cikin mawuyacin hali"
Kai Siraj ya É—aga wadda hakan yasa ya hango Mairo dake kwance saman carpet dafe da ciki idonshi cike daf da hawaye,
Da sauri ya share hawayen ya kara matsowa kusa da Momi ta yadda Mairo bazataji Abinda yake faÉ—a ba yace “Momi mi yasa kika sanar da ita miyasa kuka zo da ita har a Asibiti ba a sanar da mace mai ciki irin wannan tashin hankali"
"Nima ba a son raina ta sani ba" Haka kawai Momi tace mishi ta cigaba da kukanta.
Hannayenshi yasa aljihu ya sake ajiyar zuciya sannan ya nufi k'ofar É—akin,
Tsaye yayi yana kallonshi bayan ya maida k'ofar ya rufe kamin ya k'arasa kusa dashi ya kira sunanshi "Yaya ya jikin naka?"
Daker ya masa mishi “Alhamdulillahi Siraj ka iso?"
“Eh mi kake ji yanzu?"
Bai bashi amsa ba sai kawai yace “Siraj Please ka kula da Momi sosai da kuma Abinda Mairo zata haifa nasan zasu iya shiga wani hali idan ba kowa kusa dasu musamman Momi"
Kallon rashin fahimta Siraj yayi mishi “Mi kake magana akai ne
?"
“Siraj bana jin zan tashi daga ciyon nan inajin ajalina yana kusa dani"
“Waya baka tabbacin ba zaka tashi ba?"
“Babu nine naji a jikina"
"Zafin ciyone kuma In'sha Allahu zaka warka"
“Nidai inason ka kula da Momi Siraj karka barta ta shiga damuwa"
Siraj zai sake yin magana yaji an turo k'ofar É—akin, hakan yasa shi juyawa yana kallon Mansura da wata mata ke rike da ita, daga jiya zuwa yau kawai tayi wata irin rama idonta yayi bak'i kamar ba ita ba,
Har kusa da gadon matar ta kawota, ita kuma ta fashe da kuka tana kallon Qasin “Ina ni Allah ya É—orawa wannan ba kai ba ina son ka Qasin sosai"
Cikin sanyin murya yace “Na sani Mansura shiyasa naso nayi rayuwa ta jindaÉ—i tare da ke naso naga jininki"
Durkushewa tayi gaban gadon tana kuka “Hakika na cutar dakai Qasin duk wani hakki da yake akaina naka banayi kana son haihuwa amman na dinga shan magani akan kar ka É“ata min rai ka kyale ni har mahaifa ta lalace ta yadda bazan iya haihuwar ba yanzu"
“Ba amfanin yin wannan maganar a yanzu ni dai Abinda nake so dake shine kada ki cutar da abinda Maryam zata haifa dan Allah"
“Duk abinda Maryam zata gaifa Qasin jininka ne bazan taÉ“a cutar dashi ba zan nuna mishi so kamar É—an ciki na zamu bashi kyakkyawar tarbiya ba zamu sake faÉ—a nida Maryam ba zamu zauna a gida É—aya zan rike kamar k'anwata nayi maka alkawari"
“Ba tashi zanyi ba Mansura dan haka babu anfanin yin wannan maganar kawai dai inason ki kula da abinda Maryam zata haifa kamar naki"
Kai ta girgiza tana wani irin hawaye “Bazan iya rayuwa ba kai ba Qasin ka sani"
“Na sani amman daga yanzu zaki soma"
Cikin kuka mai k'arfi tace “A'a Qasin ba zaka mutu ka barni ba ba zamu rabu da juna ba"
Nan Siraj ya kalli matar ake rike da ita itama tana kukan yace “Fitar da ita waje Please yana cikin zafin ciyo yanzu"
Ba musu ta kamata tana kukan suka fice.
Tashi shima yayi ya fice yan nashi hawaye,
Jinginawa yayibjikin k'ofar yana kallon Mairo dake kwance dafe da ciki bayan ya fito,
Can ya k'arasa kusa da ita yana kllonta rabon daya sata a idonshi tun ba'a ɗaura mata Aure da Qasin ba dan duk zuwan da yake yi sai dai yace yana gaisheta amman bai taɓa yarda sun haɗu ba koda sau ɗaya,
Tana kallonshi ta fashe da kuka “Siraj Yaya" Abinda ya furta kenan tana rike da mararta. Nan ya kalli Momi yace “Ko nakuda take ne?"
“A'a ba watan haihuwar ta bane cikinta wata takwas ne"
Nurses Siraj ya kwalama kira cikin hanzari suka iso ya nuna musu ita,
Bayan sun É—auke ta yaje ya kira wata Dr mace dan ta kula da ita.
Baifi minti biyar zuwa shida da barin gurin ba Yarima ya iso, kana ganin shi shima zakasan hankalinshi a tashe yake. Kallo kawai yayi ma su Momi a atsayin gaisuwa dan yadda ya gansu cirko-cirko bai iya yi musu magana ba sai kawai ya tura k'ofar É—akin ya shiga,
“Sannu friend Allah ya baka lafiya" Abinda yake faÉ—a kenan yana k'ok'arin k'arasawa kusa dashi.
“Yarima..." A hankalin Qasin ya kira suna shi. Amsawa yayi tare da jan kujera ya zauna “Na'am ya jikin naka?"
“Wata alfarma nake rik'o a gareka"
“Alfarma kuma Qasin kamar ta me?"
Ya dade kamin yace “Nasan ka tsaneni Yarima amman ina rokonka dan Allah kada k'iyayyar da kake min ta shafi Maryam ko abinda zata haifa Please"
Murmushi Yarima yayi idonshi cike da hawaye yace “I hate you no more Qasin banyi maka tsanar da har zai iyasa na cutar da iyalinka ba kuma duk wannan ma abaya ne na maka alkawari babu abunda zai sake shiga tsakanin mu"
“Yes babu kan tunda zan mutu zan tafiyata na bar duniyar"
Kafadarshi Yarima ya dafa “Zaka tashi Qasin zamu sake zama abokai kamar lokacin da muna k'anana"
“Bazan tashi ba Yarima i feel it" Idonshi cike da hawaye yayi maganar,
Hannu Yarima yasa ya toshe bakinshi ya lumshe ido. Suna haka Siraj ya shigo wata Nurse na bayanshi rike da akwatin magani,
Tun daga bakin kofa yace ma Yarima “Ka tashi ka fice yana cikin zafin ciyo yanzu baya buk'atar kowa kusa dashi"
Sai da ya buÉ—e ido ya sake kallon Qasin sannan ya tashi ya fice.
Sirinji Siraj ya É—auka ya shiga É—ura mishi allura, yana faÉ—in “Ya kamata ka samu bachi yanzu"
“Karka min alurar nan Siraj"
“Dole ne ayi maka ita Yaya kana buk'atar hutu"
“Baka tsoron idan kayi min wannan alurar nayi ta bachin da bazan farka ba"
Tsayawa Siraj yayi cak. Sannan ya lankwashe alurar har ta sokar mishi hannu, da sauri Nurse É—in ta aje abinda ke hannunta ta rik'e hannun shi tana faÉ—in “Calm down Dr"
Bai kulata ba ya shiga faÉ—a da Qasin idonshi cike da kwallah “Irin wa yannan kalaman naka ne suka haddasa matar nakuda ba lokacin haihuwar taba wadda hakan kan iya haddasa mutuwar abinda zata haifa ko kuma ita kanta, miyasa kake irin haka ne Yaya?"
“Siraj ba ko wane bawa bane idan zai mutu yake samun irin damar dana samu ta aiwatarda wasu abubuwan da halshen bakina ba"
Gufanawa Siraj yayi gaban gadon kamar mai rokon gafara yana kuka “Dan Allah kabar irin wannan maganar Yaya i don't want to lose you"
“Of course you haka to" A wahale yake maganar,
“Taya kake tunanin É—an'uwanka zai rayu idan ba kai a kusa dashi?"
“Ka dawo da aikinka a nan Siraj dan idan ka cigaba da zama Abuja abin zai yima Momi yawa"
Gefen rigarshi Siraj yasa ya share hawayenshi ya tashi ya fice.
*** *** ***
Two hours Mairo tayi tana nak'uda cikin ikon Allah Allah ya kawo mata sauki ta santalo kyakkyawan É—anta,
Nan wasu Nurses suka hau gyara ta ita kuma Dr ta shiga cigaba da yi mata abubuwan da akeyi ma macce bayan cire É—a.
Saida suka gyara shi tsaf sannan wata Nurse ɗin ta fita karɓa kayan jariri,
Bayan sun saka mishi kayan suka naÉ—eshi cikin tawul suka fito dashi suka mik'ama Momi dake kuka tare da dariya.
Mansura ce ta riga kowa karɓar shi ta manna mishi kiss a goshi sannan ta nufi hanyar da zata kai gurin da ɗakin Qasin yake,
A hankalin ta tura k'ofar É—akin ta shiga Momi na bayanta kowanne fuskarsa da hawaye. Kusa da gadon ta tsaya tana nuna mishi jaririn “Maryam ta sauka Qasin mun samu É—a"
Yana kallon yaron ya lumshe ido hawaye suka gangaro mishi suka shiga cikin kunnen shi sai numfashinshi ya fara rawa.
*© KHADEEJA CANDY*