♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*Vote me on Wattpad* @khadeeja_Candy
*63*
Asibiti ya nufa da ita bayan an bata gado, ya kira a gidan su ya sanar.
Cikin yan mintuna mahaifiyarta ta iso tare da k'anenta biu, tambayarshi suka rik'ayi yadda abin ya faru bai faÉ—a musu gaskiya sai kawai yace ruwan zafi ne ta É—auko sai ya watsar mata a fuska da jiki.
Sai da ka kira sallar Azahar sannan ya baro asibitin ya nufo gidan Momi, a masallacin dake kusa dasu ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga ciki.
Tun daga yanayin Sallamar shi Momi ta gane akwai abinda yake faruwa bayan sun gaisa ta soma tambayarshi, “Ya akayi yau naga kamar ranka a É“ace?"
Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Momi Maryam ce ta watsama Mansura ruwan zafi"
“Subhanalllahi garin yaya?"
Nan ya kwashe abunda ya faru ya faÉ—a mata.
Baki Momi ta rik'e “Da gaske Maryam ce tayi?"
“Itace Momi kuma ni irin masifar nan ce nake gudu kar wata rana suje suyi abinda yafi haka kuma"
“Ai maganin biri karen baguzawa abinda Maryam tayi Batayi dai-dai ba amman kuma hakan zai sa Mansura ta É—an saurara mata"
Qasin ya gyaÉ—a kai “Ko kuma tace saita rama ba"
“Abinda nake so dakai indan taji sauk'i sai ka tarasu guri É—aya kaja musu kunne"
“Toh Momi zanyi haka In'sha Allahu"
Sai da yaci abinci sannan ya bar gidan.
Mairo na zaune parlor ya shigo da sallama amsa mishi tayi tana kallon cikin idonshi, k'in yarda yayi ya haÉ—a ido da ita tana mishi sannu da zuwa ya amsa ya wuce dakinshi,
Da ido ta bishi har ya shige sannan ta zauna saman kujera tana sauke ajiyar zuciya. Duk sai raji ba daÉ—i. Ta kusan minti 30 a haka sannan ta tashi ta nufi É—akin nashi.
“Assalamu alaikum" a sanyaye tayi sallama shi kuma ya amsa mata yana daga kishingiÉ—e tana dannar wayar shi,
Juyawa tayi zata koma nan ya É—aga kai ya kirata “Maryam"
“Na'am" Juyowa tayi ta k'araso kusa da gadon shi idonta cike da hawaye.
Nan ya unk'ura ya tashi zaune “Mi akay?"
“Ba komai"
“Ba komai kike kuka?"
“Naga kana fushi danine"
“Kan mi zanyi fushi dake ni bana fushi dake amman abinda kikayi ban jidaÉ—i kuma baki kyauta ba"
“Amman ita ta kyauta data fasa min kai ko?"
Cike da shagwaɓa tayi maganar.
Murmushi yayi mata ya janyo ta ya zaunar saman k'afafunshi,
“Toh ramuwace kikayi kenan?"
“A'a nidai bance ba"
“Amman nasan nufi kenan naji yanzu kin rama ai shi kenan ko dan Allah karki sake kinji ku zauna lafiya nine za jindaÉ—i in kika min haka karki sake kulata"
Kai ta É—aga mishi “Bazan sake ba amman sai idan ita bata min ba"
“Ba zata miki ba zanja mata kunne itama"
“Naji tashi muje kaci abinci"
Tashi yayi badan yana jin yunwa ba sai dan yana gudun yace baya ci tace mishi fushi yake da ita.
Zamansu su cigaba dayi na ma'aurata wani abu bi sake shiga tsakanin su,
*** *** *** ***
Mansura kin yarda tayi ta dawo gidan bayan an sallame ta daga asibiti danginta sai masifa suke ita kuma tace sai da ya zaɓa ko ita ko ita ko kuma ya raba musu gurin zama shi kuma yace ba zaiyi ko ɗaya ba Momi tace mishi ya samu musu ido idan ta gaji ita zata nemi dawowa,
*BAYAN WATA UKU*
Rufe yake da ido Mairo na gudu yana binta suna yar link'wa. Saman kujeara ta hau tayi tsaye tana taÉ“a bayan shi juyowa yayi cikin hanzari ya rike yana faÉ—in “Na kama" ita kuma ta fashe da dariya suka faÉ—i k'asa,
Wata razzanann ihu ta saki lokacin da kuiwar hannushi ta daketa a mara by mistake.
Da sauri ya buÉ—e idon yana tambayar ba'asi. kasa magana tayi sai kuka take tana rike ciki, nan ya shiga duba cikin. Jikin da yaganine ya katse mishi hanzari,
da sauri ya É—aga ta amman ta kasa tsaye sai kuka take tana kiran Abban ta saman kujera ya zaunar da ita ya nufi É—aki, riga yasa ya É—auko keys ya dawo parlor a guje ya É—auke ta ya nufi mota da ita.
Asibiti mafi kusa ya nufa da ita yana isa ka wuce da ita Emergency,
Shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake a bakin kofar. Can Momi ta faɗo mishi a rai da sauri ya taɓa aljihu shi da niyar ɗaukar waya yaji babu komai dan ba'a cikin shiri ya fito ba,
juyawa yayi da sauri ya koma gurin da aka tana da dan parking din Motocin Asibitin da na mutane ya shiga tashi motar ya É—auki hanyar gidan Momi.
Hankali a tashi ya shigo yana kiranta.
Da sauri ta fito daga kitchen “Gani nan Qasin lafiya"
“Momi Maryam ce na kai Asibiti yanzu"
“Lafiya miya sameta?"
Kasa faÉ—a mata ainihim abu yayi sai kawai yace “Ruwa suka zuba a kasa shine tana takawa sai ta faÉ—i jini ya dinga mata zuba"
“Inna lillahi wainna ilaihi raji'un wace Asibitin ka kaita?"
"Momi saka hijab É—inki muje a Special Rahama hospital na kaita yanzu suka shiga da ita Emergency"
Kitchen É—in Momi ta koma ta kashe gas ta É—auko Hijab É—inta suka fice.
Gudu ya rik'ayi sosai cikin yan mintuna suka iso Asibitin direct Emergency ya nufa.
Koda ya isa har likitan ya fito daga ciki yana tsaye waje yana magana da wata Nurse. Qasin yace “Yauwa gama likitan daya karÉ“e ta can"
Gurin shi suka nufa ko k'arasawa basu yi kusa dashi ba Momi ta shiga tambayarshi “Likita ya jikin wadda aka kawo?"
Kallon Momi yayi ya É—an murmushi “Kune iyayenta? yanzu nake tambayar wadda ya kawota"
“Mune muka kawota ya jikin nata?" Qasin ya tambaya
“Da sauki bachi take yanzu muje office É—ina akwai maganar da nake sonyi da kai"
Shine a gaba suna biye har ya isa office É—in gurin zama ya nuna musu bayan ya zauna ya É—auko wata takarda yayi rubuce-rubuce ya mika mishi “Wannan maganin za'a siyo mata kuma ina son sanin abinda ya faru da ita har ya janyo zubar jinin nan nata?"
K'arya da yayi ma Momi ita yayi ma likitan yana noce-noce da kai.
Likitan yace “Toh kunci sa'a da cikin bai zube gaba daya ba amman dai yayi zuba dan haka kawanakin haihuwar ta zai karu kamin ta haihu"
Bakin Qasin sake yana kallon likitan dan bai fahimci inda ya dosa ba,
Momi cikin rashin fahimta tace “Dr mi kake nufi ciki ne da ita ko mi?"
“Eh tana da ciki baku sani bane? 3 months amman yanzu ya koma 2 saboda zubar da yayi"
“Dr da gaske?"
“Ya no doubt zaka iya zuwa wani Asibitin ka bincika idan baka yarda ba"
Baki Qasin ya rufe ya lashe ido yana sauke wani nauyayen ajiyar zuciya. Can ya tashi tsaye ya yaba likitan baya ya rumgume hannayenshi yana murmushi,
Momi kuma ta É—aga hannu sama tayi yima Allah godiya. Likitan dai sai kallonsu yake yana murmushi. Momi ce tayi ma likitan godiya shi kuma ya É—auki takardar maganin suka fice.
A hankalin ta fara motsa hannunta har ta buÉ—e idonta,
Qasin ta fara yin karo dashi yana zaune kusa da ita yana murmushin da duk wadda ya gani yasan daga zuciyashi yake. Hannu yakai ha shafa kanta “Babyna kin tashi?“
Kuka ta rik'a k'ok'arin k'ak'arowa “Ina Momi?"
“Tazo ta duba ki sai kuma tace bari taje ta girka miki abinci"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba. Nan yaja yatsanta yana murzawa “Maryam albishirinki?"
Kallonshi tayi “Mi akayi?"
“Mi zaki ban idan na faÉ—a miki?"
Kuka tasa mishi “Nidai kawai ka faÉ—a min"
Ido ya sakar mata yana murmushi har sai da tayi kukan da gaske sannan ya shiga share mata hawaye yana faÉ—in “Likita yace kina É—auke da juna biu kina da ciki"
Tashi tayi zaune “K'arya ne"
Qasin ya É—an sha kunu ya lak'aci kuncinta “Toh wa yake yin k'aryar?"
“Likita mana"
“Toh bari na kirashi kiji daman ai yace idan kika tashi na kirashi"
Bai jira cewarta ba ya tashi ya fice.
Bayan wasu yan mintuna ya shigo tare da likitan suna dariya,
“Sannu ko ya jikin naki yanzu?"
“Da sauki"
Qasin ya zauna kusa da ita “Likita wai har yanzu bata yarda tana da ciki ba"
Dariya yayi “Saboda mi ni har yanzu mamaki kuke bani ace wai bakusan tana É—auke da ciki ba har na tsawon lokaci haka"
“Toh bata wata alama na masu ciki balle na gane tunda bata amai bata rashin lafiya ba wani"
“Eh ai ba duk cikine yake saka amai ba wani sai ciki ya tsofa wani sai yakai tsakiya wani tun yana farkon shiga kai wani ma har ta haihu ita abin yazo mata da sauki ne shiyasa amman ko tofar da yawun nan batayi ne ko kwaÉ—ayi? Kuma baka lura da lokutan period É—inta ba?"
“Bata tofar da yawu gaskiya sai dai kwaÉ—ayi da maganar period kuma ni duk ban É—auka cikin ne ba"
Murmushi likitan yayi ya shiga duba “Akwai wani abin da kike ji yanzu?"
Kai ta girgiza “Babu wai da gaske ciki ne?"
“Ciki ne mana nan da wasu watanin saiki haifo mana baby boy ko girl koma biu ko uku"
Shiru tayi kamar mai tunani ta É—ora hannu saman cikin, nan Dr ya shiga faÉ—a ma Qasin wasu abubuwan daya dace tayi ko kar tayi da kuma wa yanda zata ci, ya dade yana mishi bayani sannan ya fice.
***, *** ***
Kwananta biu Asibitin aka sallame ta bayan likitan yasa ya buÉ—e mata file É—in awo,
Momi k'in yarda tayi su koma gida sai wai abubuwa zasu mata yawa tun shi namiji ne ba zama yake ba k'ara ta É—an kwana biu gurinta sannan.
Qasin ba dan yana so ba sai dan ganin ta nace akan hakan dole tasa ya sai kyali ta dawo gurin Momi da zama, ta kusan wata biu gurin Momi baya aikin komai sai dai taci tasha sai bachi da kuma kallo Momi ta dinga shagwaɓata kamar gareta farau ciki.
Sai da Qasin yayi kamar yanayi sannan Momi ta samu wata yar tsohuwa ta haÉ—a su wai ta rik'a kama mata aiki, da kuma lurarda ita wasu abubuwan da ya kamata ta sani.
AÉ“angaren Mansura tunda labarin ya sameta ta shiga damuwa da nadama kullum cikin kuka take tana dana sanin abinda tayi,
**** **** ****
Wani yanayi Qasin ya sami kanshi wadda bai taɓa mafarkin samun haka ba wai yau gashi shida matarshi suna rainon ciki,
Kula yake da cikin sosai yana Shagwaɓata da tarairaiyarta hakan yasa abu kaɗan sai tasa mishi kuka shi kuma duk yabi ya rikece. Cikinta na wata shida yasa ta shirya shi da ita suka je k'auye gaida Gwaggo,
Aiko kamar ta haÉ—eye Mairo dan murna dan rabonta da ita tun tana Amarya ga kuma cikin da taga jikinta dan Qasin hana Momi yayi ta faÉ—a, aiko murna gurin Gwaggo ba'a magana ta rasa inda zata saka Mairo. Duk inda dangi suke na kusa sai da Gwaggo ta kai ta duk da ita Mairo ba hakan taso ba wai ita kunya take ji,
Kwananta biu can ran na uku Qasin ya zo ya É—auke ta abubuwan su na k'auye Gwaggo ta haÉ—a mata bayan tayi mata tsabar daddawa da miyar kuka, da guro. Da kayayyakin k'walama na k'auye.
*** ***** **** ****
Ganin babu Sarki sai Allah yasa dole Mansura ta nemi dawowa gidanta,
Bai hana taba amman kuma bai bari ta dawo gidan ba dan ganin yake wata fitinar ce zata sake haddasuwa idan ta dawo tunda yasan halinta da kishi kuma Mairo da ciki komai zai iya faru hakan yasa ya ware mata É—aya daga cikin gidajenshi ta tare can duk da ba hakan yaso ba dan wasu ganin suke raba mata kesa yara su tashi ba haÉ—in kai ko kuma su rik'a k'iyayyar junansu,
Wasa-wasa cikinta ya tasarma wata na takwas. Sam Qasin baya yarda tayi wasa da awo dan yasan muhimmancin zuwa awo ga mace mai ciki yana hana faruwar wasu abubuwan yana kuma taimakawa mace ta sami saukin haihuwa.
kullum Qasin cikin zolayar yake wai yan biu zata haifa duk da likita ya tabbatar musu da É—a É—ayane a cikinta,
Itan babu abinda ta tsana irin wannan maganar dan É—an É—aya ma tunanin take yadda zata haifoshi.
*** **** ***** ******
Duk zaune suke k'asan carpet suna kallon Tv. Ita kuma sai faman nishi take tana cin gauta,
Hannu yakai ya shafa cikinta “Wannan cikin Akwaishi da ciye-ciye koda yake daman ance yan biu haka suke"
B'ata fuska tayi “Ka fara ko nace maka nidai bana so"
“Toh ko baki so idan Allah ya nufa sai kin haifa baki ga cikin kullum k'ara girma yake ba?"
“Ai Dr yace É—a É—aya ne"
“Toh likita Allah ne? Abinda Allah yaga dama yake sanar dasu kuma so nawa akayi haka kinga an haifi ba abinda suka ce ba? Kedai kawai kice Allah ya sauke ki lafiya"
“Amin amman nidai É—aya zan haifa"
Murmushi kawai yayi ya cigaba da kallon yana shafa cikinta.
Kwantowa tayi saman jikinshi “Yaya" a hankali ta kira sunan shi
“Na'am K'anwata"
“Ya maganar tafiyarka tana nan?"
“Tana nan amman idan kin barni ba kince bakison naje ba?"
“Toh baza ni ba"
“Toh kayan da naga kasa a boot É—azun fa?"
Murmushi yayi “Wanine ya rok'eni tufafi shine na saka a mota idan zan fita sai na biya na kai mishi"
“Amman kuma ka saka a jakar da kake tafiya da ita?"
“Eh har jakar zan bashi"
“Da gaske?"
“Eh mana ba kince kar naje ba amman fa abubuwa zasu wuce ni da yawa kinga tunda kika zamu cikin nan duk wani abun da zai kaini nesa bana zuwa wannan ma dan naga yana da muhimmanci ne dan kuÉ—i zamu samu ba kaÉ—an ba kuma kinga zamu haÉ—u da wasu turawa ne idan sun mana interview munci sai su saman hannu mu fara wata kwangila a South Africa"
“A'a nidai bana so ka bari har wani lokacin ai duk gun da arzikinka yake sai ka ci"
Kwantar da ita ya ya k'arayi “Ai a zani ba tunda kince bakiso amman dai da kin Amince da yafi"
“A'a ban Amince ba"
“Ok My Queen"
Dariya tayi shima yayi murmushi ya rumgume ta,
Sun daÉ—e parlor sai da yaga ta fara jin bachi sannan ya tashi suka shiga Bedroom.
*WASHE GARI*
Tun da sukayi sallar A'suba suka sake komawa bachi. Mairo bata farka ba sai 9 da rabi. Ta daÉ—e zaune saman gadon sannan ta sauko tana wani abu da jiki kamar wadda ke mata ciyo,
Sai da ta shiga bathroom tayi fitsari sannan ta nufi parlor sanye da doguwar rigar bachi kanta ba É—ankwali,
Murmushi ya rik'a sakar mata har ta k'arasa kusa dashi tana kallon dining room. “Baba Ladi bata k'are haÉ—a breakfast É—in bane?"
“Ta kare mana acici ke nake jira ki tashi muci"
Sai a lokacin ta kalleshi “Good morning"
Ta faÉ—a tana shafa kanshi tana murmushi
Kiss yayi mata a cikin “Morning my babies how was your night?"
Dariya tayi taja mishi kunne. Nan ya tashi tsaye yana faÉ—in “Muje nayi miki brush muci abinci"
Hannunta yaja suka koma É—akin.
*11:5am* Suka gama breakfast cikin dabara Qasin ya zare jiki ya shiga É—akin shi yayi wanka, yana fitowa ya tararda Mairo zaune saman gadonshi tana kallon k'ofar bathroom É—in.
Murmushi ya sakar mata “My babies"
“Ina zaka je?"
Zaunawa yayi kusa da ita yana tsane jikinshi da tawul “Bana faÉ—a miki tun shekaranjiya ba ina da É—aurin Aure?"
“Eh amman ai K'arfe biu kace za'ayi"
“Inason na biya gurin Momi ne kamin lokacin yayi dan kusa da sune"
“Da gaske?"
Fuskarta ya rik'a ya goga mata hancin shi “A'a da k'arya"
Murmushi tayi “Na shirya ka kaini gurin Momi sai ka wuce? Tun da kace zaja biya"
Shiru yayi har na wani lokacin sannan yace “Eh jeki shirya"
Da dariya ta tashi ta fice.
Tare suka tafi gidan Momi yana yin parking yayi saurin riganta shiga parlor, koda ta shiga bata tararda kowa ba kujera ta samu ta zauna taba kiran Momi.
Kitchen Momi ta fito tare da Qasin tana murmushi “Oyoyo Maryam yau gidan mu?"
“Eh Momi ina kwana?"
Zaunawa tayi tana faÉ—in “Wuni dai ko ai sha biu ta wuce yanzu ya gidan?"
“Lafiya kalau ina su Usman?"
“Yana makaranta jiya ko Siraj ya turo mana hoton matar da zai Aura"
Mairo tace “Eh muma ya turo mana Momi kyakkyawa da ita fara"
“Eh yace yana nan zuwa a shirya zuwa gaida iyayenta"
Qasin yace “Wai Momi yar Abuja ce?"
“Eh yace acan take ita da iyayenta"
"amman yayi dacen mata gaskiya" fadar Mairo.
Momi tace "Ai ko ita tayi dacen miji dan É—aya nima ba baya ba"
Duk dariya sukayi Qasin ya shafa kanshi “Nikan bari naje ina son biyawa wani guri"
Momi ta kalleshi “Ok Allah ya tsare"
"Amin"
Da ido Mairo ta bishi har ya fice. Sannan taji ya kira ta,
“Na'am" amsawa tayi ta tashi ta nufi k'ofar, tsaye tayi bakin k'ofar tana faÉ—in “Gani"
Hannu yasa ya janyota ya rufe k'ofar.
“Baki ce Allah ya tsare ba"
“Toh Allah ya tsare duk abinda aka ci ka kawo min"
Dariya yayi “Toh an gama Hajiya ta"
Nan ya matso kusa da ita sosai yasa bakinshi cikin nata ya soma kissing.
Sun daÉ—e haka sannan ya cire bakinshi yana sauke ajiyar zuciya ya É—ora goshinshi saman nata ya lumshe ido,
Can ya É—auke kanshi yana murmushi “Sai na dawo biebes na I LOVE YOU"
“I love you too Allah ya tsare"
Murmushi yayi mata as respond ya nufi gurin motarshi,
Har ya fice hannu take É—aga mishi yaba dago mata. Saida Mai gadin ta rufe gate sannan ta juya ta koma cikin parlor.
shigowanta yasa Momi ta kalleta tana murmushi “Allah ya saukeki lafiya Maryam wannan ciki sai kace yan biu"
“Haka yaya yake cewa shiyasa ko wani aikin kirki bana iyawa" ta faÉ—a tana k'ok'arin zaunawa,
“Ai dole yanzu ma ba dan kar Ladi tace an barta ita ka É—ai ba da sai kiyi zamanki har ya dawo"
“Ai sai ya dawo zamuje"
“A'a yace da maraice yayi na turaki gida kar na bari dare yayi"
Kallon Momi tayi “Momi ba É—aurin Auren zaije ba?"
Murmushi Momi tayi
“Yaje kaduna amman yace kar a faÉ—a miki sai ya tafi"
Nan da nan gashin jikinta ya tashi idonta suka cika da kwallah kan kace kwabo har hawaye sun fara mata zuba,
Momi tace “Toh ai ba dade wa zaiyi ba kwana biu zaiyi ya dawo"
Kuka ta sama Momi sosai “Niko Wallahi ba zan koma ba sai ranar daya dawo ko shekara zaiyi"
“Toh gaki ga guri ai indai zamane ita Ladi anjima sai Nura yaje ya faÉ—a mata taje gida har ki dawo daga nan sai ya biyo miki da kayanki"
Duk da hakan ta daÉ—e tana kuka Sannan ta share hawayen ta cire hijab É—inta,
Momi ta tashi ta É—auko mata fruits.
*** **** *****
Tunda ya tafi kullum cikin kiranta yake kirn safe daban na rana daban na dare ma daban.
Ranar da zai dawo Mairo ta tashi da wani irin matsanaicin ciyon kai da zazzaɓi wuni tayi kwance breakfast ma dak'er tayi bata fito ɗakin ba saida Momi ta kare shirya ma Qasin komai da tasan zai buk'ata dan ya faɗa mata nan zai sauka,
Abinci kusan kala uku Momi ta shirya mishi sannan taje tayi wanka. Mairo ma wankan tayi ta shirya cikin wani les Sky Blue bata yi makeup ba powder kawai ta shafa sai mai a leɓe ta dawo parlor ta zauna. Fuskarta babu walwala,
Zaune tayi a parlor har kusan biyar na yamma. akai-akai take duba wayarta dake saman hannun kujera kamar mai jiran kira gaban sai faÉ—uwa yake, Guraren biyar da rabi ta samu kanta ciki wani yanayi kamar ta fasa kuka. Sai juye-juye take tana sauke ajiyar zuciya.
“Amman yaya ya daÉ—e bai iso ba ko bai taso da wuri bane" a fili ta furta tana kallon k'ofar É—akin Momi,
Wata zuciyar na nuna mata ta kira shi sai kuma taji ba zata iyaba.
Tana haka taji Parking É—in mota da k'arfi ta zabura tana kallon k'ofa bugun gabanta ya k'aru,
Usman ne ya shigo hawaye na mashi zuba, suna haÉ—a ido yayi saurin sadda kanshi yana share hawayen.
Zaro ido Mairo tayi nata idon suka cika da k'wallah “Lafiya Usman miya faru?" ta tambaya muryar ta na rawa.
“Ba komai ina Momi?"
Kasa bashi amsa tayi ta k'ura mishi ido tana son karantar abinda yake É“oye mata,
Fitowar Momi ce tasa ta daga kai tana kallon upstairs. Hawayen da ta gani a fuskar Usman su ta sake gani shinfiÉ—e a fuskar Momi,
Rawa jikinta ya shigayi ta fara wani wahalallen numfashi, kamar haÉ—in baki wayarta tayi ringing.
Da sauri ta kalli wayar tana haÉ—e yawu,
Cikin hanzari Usman ya kai hannu ya É—auke wayar ya kashe.
K'ara zaro ido Mairo tayi hawaye suka shiga mata zuba kamar an koro su, Momi na da fata ta saki wata irin razananniyar kara ta faÉ—i zaune dafe da ciki.
*© KHADEEJA CANDY*