MALAM INA NEMAN AMSA

TAMBAYA
=========
👇
Assalam alaikum,

Mallam wanine yakamu dason wata wani son har kasa bacci yake akanta kuma tsoron  kar mutane suga wautarsa shi yasa yake boye abin azuciyarsa,  kuma shi sau biyu yaje gidansu hira,
Tambayar shine Mallam irin wannan son babu zargi acikin sa? Kakasa bacci saboda wani ?

AMSA
=====
👇
Babu wani zargi gaskiya. Ae shi SO Halitta ne.
Allah madaukakin sarki a cikin Babban littafinsa da Alqur'ani mai girma, Cikin suratu Ali-imran Allah yace. HAKIKA MUN SANYAWA DAN ADAM SON SHA'AWA DAGA MATA DA 'YAYA DA KAYAN ADO DAGA AZURFA DA ZINARIYA DA DAWAKAI DA DABBOBI DA KUMA KAYAN AMFANIN GONA KO KAYAN MARMARI..
  Anan sai Allah ya fara da maganar So kuma son ma irin na mace.
Lalle akwai jarrabawa akan soyayya. Allah ya kan jarrabi Namiji da son mace ko ya jarrabi mace da tsabagen son namiji, Wanda zataji kamar idan bata ganshi ba ko idan bai ganta ba, zai iya mutuwa a wannan Ranar. So yana sanyawa mace tana yiwa namiji kuka ko Namiji yana yin mace kuka, wallahi Naga wanda yake yiwa mace kuka, kuma na Sanshi. Kuma ina nan yake mata kuka a Gabana.
Wani ya taba gaya min cewar, budurwarsa wadda yake tsabagen sonta, kuma so na hakika, so irin na jarrabawa, sun taba yin magana cewar idan ta Gama wani aiki zatayi masa plashing, sai ya kira ta a waya, gashi kuma yana son zai shiga wanka, Amma a haka yayi ta jira bata kirawo shi ba, har ya yanke shawarar bari kawai ya shiga wanka. Bayan Ya shiga wanka sai ta kira shi. Ae kuwa da yaji arana wayarsa, Wallahi yace min, a haka ya kado da gudu daga Bandaki da kumfar sabulu a jikinsa, har sai da ya dauki wannan wayar sannan ya sami Nutsuwa, sai bayan Ya dauki wayar ne ma ya tabbatar da cewar Ashe wanka yake yi, Sannan ya koma Bandakin yaci gaba da Wankansa.
Wannan kadan kenan fa, wani idan ya gaya Maka nasa zaka sha mamaki, ko idan wata ta gaya Maka nata son zaka sha mamaki.
Kalli Sahabin manzon Allah saw Mugiyra, Wanda soyayyar Barira ta kama shi, haka yake yawo lungu-lungu a garin Madina, yana kuka, yana Nemanta don ya samu ya ganta ko ya sami nutsuwa, harma Manzon Allah saw what rana ya ganshi yana yawon nemanta, ya wuce ta gaban Manzon Allah saw, sai Manzon Allah saw ya nuna shi da hannunsa mai Albarka, yace Da Abdullahi Dan Abbas, KALLI YADDA MUGIYRA YA KOMA. Manzon Allah saw ya  same ta akan ta koma gidan Mijinta. Tace shawara kaka bani ko Umarni? Sai manzon Allah saw yace shawara nake baki, sai tace da umarni ne dole na in koma, tinda wannan daga Allah ne ba yadda Zanyi, amma tinda shawara kaka beni, bazan koma gidansa ba ya Manzon Allah.
Kalli Abdurraahman Dan sayyadina Abubakar, Mahaifinsa ya taba umartarsa da cewar ya saki matarsa, Sabida matarsa din tana da kyau, Wanda wannan ne ma yasa yake neman mantawa da zuwa wajen yaki. Bayan an Rabashi da matarsa, sai da ya hau kan Soron gidansa yana kuka, Akan ayi hakuri a maido masa da matarsa.
Sai dai Imam Ashshafi'iy yana cewa, Idan Allah yaso ya yiwa Bawa ko Baiwarsa Azaba, sai ya jarrabeshi da son wadda bata Sonshi. Ko idan Allah yaso ya yiwa Mace Azaba, sai ya jarrabeta da son wanda baya Sonta.
Abinda ya dace Anan shine, ya zama very control. Wanda idan ya saketa ta gane irin son da yake mata, to fa Lalle zata iya rena shi. Kuma ba yadda xaiyi, tinda yana sonta, domin wannan zai iya kaishi ga halaka, tinda Su mata da yawansu sai a hankali, idan mace bata da cikakken tsoron Allah, sai abinda ka gani.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)