MALAM MECECE MAFITA?

TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum mallam barka dawarhaka  mal ina da tambaya jiya ne muki hira da friend dita taki tambayata nace sai na tambaya nema tayi aure ba awuce wata uku ba suka rabu da mujin yana abuja da aiki ita kuma tana kano yariki mata gidan haya nashikara daya toh awata uku suka rabu ranan ya kushi kayansa yatafi ankirasa domin sulhu yakixo wa wajin iyayinta takushi kayanta tazo gida sai kawayinta suka bata shawara da tajita sami dilalin daya nemu gidan nasu yamayar mata da sauran kudi hayan nasu takar ba tayi anfani dasu tunda tana da hakki akansa har idda takari sai tabi shawaransu tayi hakan aka samu wane yakama gidan aka mayar mata dasauran kudin tayi amfani da su amma batafa dawa mujin nataba kuma bai zo yabukace sauran kudin ba shikara 2 kenan da faruwar al amarin shine taki tambayan hallacin  yin hakan.

AMSA
======
👇
Wannan shine matsalar mu mata da mu da iyayenmu mata kenan, Bama zurfafa binciken wanda yazo neman yarmu da Aure. Indai yana da abin duniya ko idan yace yana aiki a Abuja, sai a dauka wai wani mutum ne daban, sai a dauki auren yarinya karama a bashi, ya tafi da ita yana fara mata Azaba, bayan kuma ita kanta Abuja suna ta tara, wani ma a kauyen Abuja yake ba a cikin Abuja ba, amma sai Kaji yace shi a Abuja yake, ita kuma yarinya sai ta kama Rawar jiki wai za'a kaita Abuja FCT.
Maganar kudin da ta karba kuma, idan muka kalli hakkin da take dashi na sallama, Wanda idan an saki mace ake bata, tinda Allah yace WAMATTI'U HUNNA. Wato muyi musu kyauta, mawadaci ya bayarda da yawa, talaka kuma ya bayar da daidai karfinsa. Kamar yadda Allah ya fadi, idan muka kalli wannan Sai muce taci halak.
Duk da ma bansan Adadin kudin da kika karba ba.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)