*_MASLAHA_*
1. Manyan malaman Sunna sukan diba maslaha kafin aikata wani aiki ko fitarda wani hukunci.
2. Hukunce hukuncen da ake fitarwa daga Al-Qur'ani da Hadisan Manzon Allah, akan diba yanayi da maslaha kafin a zartar dasu.
3. Da yawa daga cikin malaman Alhussunah wadanda su ake la'akari dasu a matsayin shuwagabannin tafiyar Salafiyya na da, dana yanzu sukan aikata ayukkan da suke ganin ba daidai bane ko su kame daga wasu ayukka da suke ganin dai dai ne domin duba maslaha da yanayi. Ga misali: a) Ibn Taymiyya R. yayi biyyaya ga Mamluks [shuwagabannin zamaninsa da suka shahara da zalunci da Bidi'ah] kuma ya umarci jama'a suyi musu biyayya kuma su hada kai dasu domin yakin Tatar [mongols]. Bayan angama yaki da Tatar, Mamluks suka rufe Ibn Taymiyya sau biyu a gidan kurkuku saboda yace Allah yana sama kuma yayi fatawa da Hadisi akan mas'alar saki, su kuma a wurinsu ba'a fatawa da Hadisi saidai abi mazhaba. b) Sheikh Nasirudden Albani ya tashi tsaye domin National Anthem a Saudi Arabia, bayan yana ganin ba'a tsayuwa ga kowa da natsuwa sai ga Allah. Dalibinsa da ya ruwaito wannan kissar, Sheikh Abdullah Murad yace ina ganin kyama a fuskar sheikh lokacin daya tashi. c) Sheikh Muhammad Ibn Salih al- Uthaimin yayi wa'azi a Saudi Arabia a gaban Sarki Fahad anayi masa tafi [clapping] (video yana a YouTube), amma baiyi inkari ba a lokacin dukda yana ganin tafi baya kamata. Wadannan malaman duk sun aikata wadanna ayukkan ne domin duba maslaha da yanayin da ake ciki.
4. Annabi S.A.W da yafi wadannan malaman duk yabar gumaka 360 a cikin ka'aba yana dawafi a Umratul Qadah bai afka musu ba sai a fathu Makkah lokacin da ba wanda ya isa yace miyasa. Bayan haka Annabi S.A.W ya gayawa Nana Aisha cewa ba a daidai aka gina ka'abah ba kuma badon [maganar] mutane ba da ya rushe ka'abah ya sake gina ta a daidai. Haka kuma ya gayawa Sayyidina Umar cewa ya bar kisan munafukai ne domin kada mutane suce yana kisan Sahabban sa [ ba don munafukan basu cancanta a kashesu ba].
Duk wadannan abubuwan Annabi S.A.W yayi su ne domin Maslaha.
5. Ana amfani da hankali ne a duba maslaha kafin a fitar da hukunce- hukunce daga Ayoyin al-Qur'ani da Hadissan Manzon Allah S.A.W., don haka idan mutum ya hardace al-Qurani da Hadisai sai ya haukace, hukunci bazai hau kansa ba ballantana a karbi hukunci daga gareshi, domin da hankali ake amfani wajen ciro hukunce hukunce.
6. A kasashen da ake da karancin karatu da karancin tattalin arziki, anfi samun rikici da sunan addini. Wani mutum baizai tara jama'a yayi wata ibada data sabawa jama'ar gari ba da sunan cewa shi yayi karatu ya gano daidai a kasashe irin Saudi Arabia ko Malesia ba, saidai a Afghanistan ko Somalia ko wani yanki na arewacin Nigeria.
7. Duk wani aiki da karshen hukuncin da malamai zasu bashi shine suce Halas ne bai kamata a aikatashi ba inda zai jawo ayiwa Sunna mummunar fahimta ko a dauki Ahlus-Sunna a matsayin
8. yan tawaye ba.
9. Saka Ikhlasi a gaba da rashin neman shuhra da yin karatu ga malamai, yana taimakawa wajen biyan maslaha da yin daidai.
10. Allah ya bamu Ikhlasi yasa muyi sabodashi ya tabbatar damu akan kitabu wassunah akan fahimtar magabata nagari.
Rubutawar: ✍
*_Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula {Hafizahullah}._*