ME AKE FADA A DAREN LAILATUL QADR?

ME AKE FADA A DAREN LAILATUL QADR?

_عنْ عَائِشَةَ رَضِيَ الله عَنْهَا قَالَتْ : قُلْتُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ عَلِمْتُ أَيُّ لَيْلَةٍ لَيْلَةُ الْقَدْرِ مَا أَقُولُ فِيهَا؟ قَالَ : قُولِي : *”اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي“* رواه الخمسة غير أبي داود، وصححه الترمذي والحاكم._

_An kar6o daga Aisha (r.a) ta ce: Na ce ya Manzon Allah! Ka ga ni idan na san daren da lailatul Qadr yake, me zan fadi a cikinta? Sai ya ce: *(( Ki ce: Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa'fu annee))* mutum biyar suka ruwaito shi, banda abu Dawud. Tirmidzy da Hakim sun inganta shi._

_'Yan uwa! Waccan addu'ar ita za mu yawaita yi a cikin Wadannan kwanaki goma har mu dace da lailatul Qadr in shaa Allah. Ma'anar addu'ar shi ne:_

*Ya Allah! Kai ne mai yafewa, Kana son yafiya, Ka yafe min*

_Wannan addu'a ce da sunnah ta koyar. Allah Ya ba mu ikon lizimtar ta._

_Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa'fu annee 👏🏽_

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

_Daga Zauren *🕌Islamic Post WhatsApp.*_
Post a Comment (0)