TAMBAYA TA 379

*Tambaya ta (379)*
:
_Mutum ne yace yasaki Mace tunkafin ya aureta, Shin daga lokacin da ya aureta nantake tasaku kenan kokuma bata sakuba??_
:
*_Amsa_*
:
_*Mālamai sunyi Saɓani* dangane da wannan Mas'ala ta hukuncin Mutum yace yasaki Mace tunma kafin ya aureta, ansamu ra'ayoyi da maganganun *Mālamai* akan haka:_
:
_*→(1)-Ƙauli na farko shine,* Mazhabin *Mālikiyya da Hanafiyya* suntafi akan cewa  idan har Mutum ya ayyana wata Mace sananniya kamar misali yace indai na auri *Hafsat* to na saketa, kokuma ya ayyana wata *Ƙabila* kamar misali yace indai na auri 'yar *Ƙabila-Kaza* ko *'Yar-Gari-Kaza*  to na saketa, kokuma ya ayyana wani zamani sananne kamar yace daga nan zuwa *shekaru-2* indai nayi auri Mace to na saketa, *Mālamai* sukace shikenan daga lokacin da'aka ɗaura musu aure  nantake *Matarsa* tazama sakakkiya, amma idan Mutum cewa yayi duk Matar da na aura na saketa, amma batare da ya ayyana wata Mace sananniya ba, ko wata *Ƙabila,* ko wani *Gari,* ko wani *Zamani* sananne, kawai yabar abinne asake ba *Ƙaidi,* to anan sai *Mazhabin-Mālikiyya* sukace duk lokacin da yayi aure to Matarsa tananan bata sakuba, saidai *Mazhabin-Hanafiyya* sun *Sāɓāwa Mālikiyya* anan, domin su cewa sukayi aikoda bai ayyana wata Mace sananniya ba ko wata *Ƙabila,* to daga lokacin dayayi aure kawai Matarsa ta saku,_
:
_*→(2)-Ƙauli na biyu kuma shine,* Mazhabin *Shāfi'iyya da Hanābila* suntafi akan cewa *Kwata-Kwata* Matarsa bata sakuba koda kuwa ya ayyana wata Mace sananniya, ko *Ƙabila,* ko *Gari,* ko *Zamani,* sukace Matarsa tananan bata sakuba, daga cikin *Dalilansu sunkafa Hujja* da wannan Hadisi na *Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* da yake cewa:_
:
*"لا طلاق إلا فيما تملك، ولا عتق إلا فيما تملك، ولا بيع إلا فيما تملك،"*
*_MA'ANA:_*
*_(Baka da ikon kayi) saki sai akan abinda (matarda) ka mallakaba, (baka da ikon) ka 'yanta bawa sai wanda ka mallaka, babu cinikayya sai  akan abinda (hajar da) ka mallaka,_*
:
_Danhaka *Mālamai* sukace da *Ire-Iren* waɗannan *Nassosinne* mafi yawa daga cikin *Sahabbai da Tābi'ai* suka fahimci cewa ashe idan Mutum yace yasaki Mace tunkafin ya aureta to koda ya aureta bata sakuba, domin ya saketane alokacin da bashi da iko akanta domin bai mallaketaba, hakanan antambayi_
_*Abdullahi-Ɗan-Abbas* cewa Mutum ne yace duk Matar da ya aura to ya saketa, sai_
_*Abdullahi-Ɗan-Abbas* yace babu saki, saboda faɗin *Aʟʟαн(ﷻ)* da yake cewa:_
:
*"يا أيها الذين آمنوا إذا نكحتم المؤمنات ثم طلقتموهن………"*
*_MA'ANA:_*
*_Ya waɗanda kukayi imani, idan kuka auri muminai mata sannan sai kuka sakesu………_*
:
_*Muhallish-Shāhid* acikin ayar shine, saida *Aʟʟαн(ﷻ)* yafara ambatar yin aure sannan ya ambaci yin saki, kuma aka sanya lafazin *Summa* atsakaninsu, wanda hakan kenuna cewa ashe dole sai in anfara yin aurene sannan za'a iyayin saki, *ko shakka babu cewa* maganar datafi inganci kuma mafi yawan *Sahabbai da Tābi'ai dakuma Mālamai* suka tafi akanta shine ba'ayin saki kafin aure, danhaka koda Mutum yafurta cewa dukkan Matar da ya aura ya saketa, to maganarsa bata dawani amfani,_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_
:
*"فتح القدير" (4/113)*

*"المغني لإبن قدامة" (9/416)*
:
*"شرح الخرشي على مختصر خليل" (4/50)*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)