*Tambaya ta (378)*
:
_Shin wai idan *Jinin-Al-ada* ya ɗaukewa Mace kafin ketowar *Al-fijr,* dolene sai tayi *Sallar Magriba* da *Isha'i*?_
:
_*Amsa:*_
:
_Dangane da abinda Mālamai sukace akan wannan *Mas'ala* shine, idan mai *Jinin-Al-ada* tayi tsarki kafin *faɗuwar rānā* kokuma tayi tsarki kafin *ketowar alfijr* to wajibine akanta tayi *Sallolin Magriba da Ishā'i* kokuma *Azahar da La'asar*, saboda tsarki ya zomata acikin lokutan waɗannan Salloli, sannan kuma zata haɗesune alokaci ɗaya ta Sallacesu wato zatayi jam'insune, saidai idan lokacinne yaƙure tayadda bazai yiwu ta sallacesu gaba ɗayaba, to shikenan sai tasallaci taƙarshen kawai, kuma wannan itace fatawar da wani sashe na *Sahabban Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* suke bayarwa, sannan kuma mafi yawa daga cikin *Mālamai* suma akan haka sukatafi, saidai wasu daga cikin *Mālamai* sukace ā'ā iyakar *Sallar* da tasamu tsarki acikin lokacintane kaɗai zata *Sallata:*_
:
_Amma idan tsarki yazowa Mace bayan *Sallar Asubahi* ko *Sallar Azahar* kokuma bayan *Sallar Magriba* to kawai zata Sallaci waɗannan *Salloline* ɗaiɗaikunsu tunda dama ba'ayin jam'i atsakaninsu,_
:
_Saidai *Mālamai sunyi Saɓani* gameda cewa idan *Jinin-Al-ada* yazowa Mace alokacin *Sallah* kuma batariga tayi wannan *Sallarba* Shin idan tayi tsarki dolene sai tarama wannan *Sallar* kokuma ā'ā bazata ramaba? Mazhabin *Shāfi'iyya* dakuma *Hanābila* suntafine cewa dole sai tarama, amma Mazhabin *Mālikiyya* da *Hanafiyya* sukace a'a bazata ramaba tunda bawai sakaci tayiba na *ƙin yin Sallar* akan lokacinta, danhaka sukace bazata ramaba, agaskiya *Mālaman* da suka tafi akan *Ƙaulin* cewa bazata ramaba *Alal-Haƙiƙa* maganarsu tafi Dalilai dakuma Hujjoji masu *Ƙarfi,*_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"المجموع للنووي"(2/562)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (1/238)*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
*_→AMSAWA←_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi