*_ZAN IYA BADA ZAKKA BA TARE DA NA SANAR CEWA ZAKKA CE BA?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam Tambaya ce daga wata 'yar uwa kamar haka: "Akwai Marayu a karkashi na,kuma dukiyarsu Rana tare dani,ina ririta musu bana son taba ta,musamman asalin dukiyar. Yanzu haka sai iyayena suka nemi na bawa daya daga cikin 'yan uwa rancen kudi don yaja Jari. Yanzu haka an fitar da Zakkah daga kudin marayun,shine nake so na bashi amma ba bashi ba. Sai dai in nace Zakkah ce, to su iyaye na bazasu fahimci dole ne ko an sami hasara dole ne a fitar da zakkah ba,zasu kara tattaro matsaloli suce a bada kudi akansu. Shin ina iya bashi kudin ba tare da nace Zakkah bace, la'akari da matsalolin da fadar Zakkar ce zai jawo min???? Allah ya karawa Malam ilimi da ikhlasi.
*Amsa*
Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa Allah madaukaki ya yi umarni da kiyaye dukiyar maraya, da kuma hana cinta, in ba da gwargwadon bukata ba, ga wanda yake talaka, kamar yadda ayoyin farko-farkon suratunnisa'i suka tabbatar da hakan.
Ba shi daga cikin sharadin zakka, sai an sanar da wanda aka bawa cewa zakka ce, kamar yadda Ibnu Khudamah ya yi bayanin hakan a littafinsa Al-mugni 2\508 da kuma Annawawy a littafinsa Al-majmu'u 6\233, don haka in kika bawa fakiri da niyyar kin fitar da zakka ko da ba ki sanar da s hi ba ta yi.
Saidai malamai sun hana yin dabara wajan bada zakka, kamar ya zama kana so ka yi ma mutum kyauta, amma maimakon ka dauki kudinka ka ba shi sai rowa ta hana ka, sai ka yi dabara ka ba shi zakkar da ka yi niyyar fitarwa.
Duk mutumin da ya bayar da zakka yadda Allah ya yi umarni, tabbas Allah zai mayar masa da ninkin-ba-ninki.
Allah ne mafi sani.
23\2\2016.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.