DAGA INA SAHU YAKE FARAWA?

*_DAGA INA SAHU YAKE FARAWA???_* 

                          *Tambaya*
Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma aiki, mal don Allah innada tambaya mal sahun sallah kan ta dama za'a fara ne ko ta hagu.?

                            *Amsa*
Wa'alaikum assalamu To dan'uwa sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman ma'ana a sanya liman a tsakiya, saboda fadin Annabi S.A.W "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 116. Sannam da fadin Anas R.A lokacin da yake bada labarin ziyarar da Annabi S.A.W ya kai gidansu: "Sai muka tsaya ni da marayan a bayansa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 694, daga nan kuma sai a cigaba da cika shi ta bangaren dama.

Haka nan ake so sahu na biyu shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi zuwa dama, saboda fadin Bara'u dan Azib R.A "Mun kasance idan muka  yi sahu a bayan Annabi S.A.W mu kan so mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da fuskarsa" Muslim a hadisi mai lamba ta: 709.

Allah ne mafi sani

21\2\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)