27. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Akwai bambanci kwarai tsakanin ja-gabana na farko, su Hamid da Belal, da ja-gabana na yanzu, su Ibrahim Ali da Yakub Hassan. Na farkon, mutanen kirkin gaske ne, amintattu, masu niyyar taimakona. Amma wadannan ko kadan ba haka su ke ba. Suka dinga gunaguni a kan hanya, har suna zagin mai gidansu, Ahmed, da ya hada ni da su. Ran nan, ran wata Alhamis, muna cikin tafiya sai suka ja akalar rakumansu suka tsaya cik, suka ce su baya za su juya daga nan Na ce musu ina dalili ? Ashe ba an tsadance da su ne su kai ni wurin Sheihu Hamid Fadai a kasar Masar ba ? Suka ce lalle haka ne, amma suna jin tsoro, kasadar ta yi yawa. Suka ce in wannan labari ya kai kunnen Halifa, ba su kansu ba, ba ma ’yanuwansu ba, kabilarsu dungum kila kasuwa za a kai su a tsire, ko a sare kawunansu. Sabo da haka ba za su yi gaba ba.
Na ce, “To, yanzu yaya za ku yi da ni, ina bako ban san kasa ba, ban san kowa ba ?" Suka ce za su kawo mini mutumin da zai ketare da ni kan iyaka zuwa Kasar Masar.
Suka ce in jira su, suka shiga wani dan kauye, suka bar ni cikin fargaba da mamaki. Da aka jima kadan suka komo tare da wani wai shi Hamid Garbosh. Kakkarfa ne, ko da ya ke shekarunsa sun fara zurfi, don ya ba hamsin baya. Muka shiga maganar ijarar da zam biya shi don ya ketare da ni iyaka. Ya fito fili ya fada mini gaskiya, ba noke noke, ya ce, “Abdulkadir." Na ce, “Na’am.” Ya ce, “Ka san kome ana yin sa don riba ne. Na yarda im fisshe ka kasar Halifa, in kai ka Assuan a Kasar Masar, amma nawa za ka biya ni ? Ka tuna fa da kafa zan tafi, kuma daji za mu yanka, ba turba sosai ba. Ka tuna kuma da halakar da na jawo wa kaina in an gane ni ne na yi maka ja-gaba." Na ce, “Gaskiyarka. To, ran da muka isa Assuan, zam ba ka dala dari da ashirin. Zan kuma yi maka kyauta gwargwadon yadda ka nuna kokarinka a hanya.”
Ya ce, “Na yarda. Na kuma gaskata cewa za ka biya ni. Zan kai ka gun ’yanuwanka ta hanyar da ba wanda ya san ta. Allah da Annabinsa su ne shaiduna ba zan cuce ka ba."
Ya koma gida ya shiryo ya moko muka yanki daji. Da Ibrahim Ali da Yakub Hassan kuwa na sallame su suka juya gida. Muka dinga tafiya dare da rana ba ya da zango, sai ko in za mu gasa gari mu yi wata irin gurasa da shi Hamid Garbosh ya iya. Mu hau wannan dutse mu gangare, mu fada wannan karkara mu ketare, haka dai, daga mu sai Allah a cikin hamada. Ran nan sai muka kai dutsen Etbai, watau mun shiga Kasar Masar ke nan. Na hau tsororuwar dutsen na hanga gaba. Watan Maris yana da kwana 16, da dan hantsi kadan muka iso Kogil Nil, ga Birnin Assuan a bakinsa.
Mai karatu, na bar maka sani, don alkalami ba ya iya bayyana zurfin farin cikina. Yau Allah cikin rahamarsa, ya kare wahalata, da bakin cikina. Yau Ubangiji ya fid da ni daga cikin duhun zalunci, ya kawo ni cikin hasken adalci. Yau na tashi a baran Halifa Abdullahi! Babu sauran im fadi kasa in gai da wani, babu sauran in dafa masa kuturi in ya hau doki, babu sauran cin sudin abincinsa, babu sauran zama a bakin kofar fada, kowa ya yi gaisuwa in ce, “A Gaishe Ka!” Na daga kaina sama, na yi wa Sarkin Sarauta godiya da ya kwato ni daga hannun Halifa Abdullahi.
Da shigarmu garin, na nufi unguwar Turawa. Kowa ya fito a guje, maza da mata, suka rungume ni suna min barka da samun kai. Na sadu da Turawa da Misirawa, ma’aikatan Sarkin Masar. A cikin Turawan nan har da wani gwanin zana taswira wai shi Bimbashi Watson. Ya ce kafin in yi aski in share gemuna, ko in sake tufafi, yana so ya zana taswirata cikin halin da na isa Assuan. Na ce na yarda, nan da nan ya zana. Turawan nan kowa ya bude mini dakin tara tufafinsa, ya ce in zo in sa wanda na ga dama, ya ba ni. Kowa sai ja na ya ke, “Zo mu sha ti, zo mu ci abinci.” Kai, na gode wannan zumunci da nuna kauna da suka yi mini. A ran nan kamannuna suka sake, sabon jini ya fara zuwa mini.
Ja-gabana Hamid Garbosh kuma na biya shi hakkinsa, dala dari da ashirin. Na kuma yi masa dashin wadansu kudi dabam, da tufafi, da bindiga. Har wa yau kuma don a nuna masa an gode masa sabo da kawo ni nan lafiya, sai Gwamnan Assuan, Kanar Hunter Pasha, ya kawo kyautar £10 ya ba shi. Muka yi kyakkyawar sallama, yana godiya ina godiya, muka rabu. Kafin gobe labari ya isa har Alkahira. Na yi ta samun wayoyin murna da barka da arziki daga wurin su Manjo Lewis Bey, da Baron Heidler Von Egeregg, wakilin Austria a Masar, su Manjo Wingate Bey da sauransu.
Na yi sa’a a lokacin nan jirgin ruwa mai daukar mel zai tashi zuwa Alkahira. Sabo da haka aka shirya mini tafiya a cikinsa. Kulliyar Turawan da ke Assuan suka yi mini rakiya har bakin jirgi, muna tafe badujala na tashi, ram, ram, ram! Wannan liyafa ta yi mini dadi a zuciya gaya, na ko gode wa wadanda suka yi mini ita.
Na isa Alkahira ran Talata, 19 ga Maris. Ko da ya ke da sassafe jirgimmu ya dangana, amma duk da haka na sami Baron Heidler Von Egeregg da ma’aikatansa duka sun taru a tasha don taryena. Ina saukowa daga jirgi suka rufe ni, suna yi mini barka. Masu jaridu kuma suka shiga yi mini tambayoyi, masu hoto suka shiga dauka. Daga nan muka shiga mota sai ofishin wakilin Austria. A ran nan kuma na sami wayar murna daga ’yanuwana da abokaina daga Austria a Turai. Bayan ’yan kwanaki na sami ganin mai girma Sarkin Masar, na yi gaisuwa, na kuma shaida masa duk irin abubuwan da suka faru gare ni a takaice, da irin halin da Sudan ke ciki. Ya yi mini barka, ya kuma koma da ni cikin aikina, aka kara mini girma, na zama Pasha.
In na dubi matsayin da na zauna shekara goma sha biyu ina barantaka a hannun Halifa, na kuma dubi irin halin da na ke ciki yanzu, sai in ji kamar mafarki na ke yi. Bauta shekara goma sha biyu ba wasa ba ce! A ciki har da watanni takwas ina daure cikin sarka.
Yanzu na sami ’yancin kaina, na zama mutum a cikin mutane. Babu abin da ke cike da zuciyata sai murna da godiya ga Madaukakin Sarki. Rokona daya ne yanzu gare shi, yadda ya kubutad da ni, ya kubutad da wadanda ke tsare a hannun wannan mugu Halifa Abdullahi.
Amin.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com
http://bukarmada.wordpress.com
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada