26. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
NA TSERE
Karfe goma na dare na yi, sai Halifa ya shiga gida, duk aka rurrufe kofofi. Nan da nan na tashi na dauki farda, watau dardumar salla, da farwa, watau bargon ulu, maganin sanyi, na saba a kafada, na sulale ta masallaci sai kan titi. Na sa fuska arewa, ga ni nan, ga ni nan har bayan gari inda muka shirya da Muhammed. Da zuwa sai na ji dan tari, ohom, ashe shi ne ya gan ni. Na ja na tsaya cif, zatona wani ne. Sai ya kawo mini jaki na hau muka nufi wani kango can a gafen gari. Muna isa sai ga mutum ya jawo rakumi. Muhammad ya ce mini, “Ga ja-gabanka. Sunansa Zeki Belal. Zai kai ka inda rakuman da za su dauke ka su ke a cikin hamada. Hau maza maza. Allah ya fisshe ka lafiya. Sai wata rana.”
Belel ya dora ni kan rakumi, shi kuma ya dare, muka duka. Ga mu nan har sha dayan dare, sa’an nan muka iso inda rakuma su ke. Belal ya hau guda, ni kuma na hau guda. Hamid Ibn Hussein shi kuma ya hau guda. Tafiya ta mika har gari ya waye. Muna tafe muna tadi, Hamid ya ce, “Kana zaton yaushe za su fara nemanka?” Na ce, “Bayan sallar safe.” Ya ce, “Wus, in haka ne kuwa sai mu cira kafa. In dai ba wani abu ya faru ga rakuman nan ba, kafin lokacin ai mun tsere, da ikon Allah!”
Muka ci gaba. Don tsoro, im mun taba ’yar tafiya kadan sai in waiga. Ni har yanzu jikina bai ba ni ba. Muna cikin tafiya bayan wayewar gari sai Belal ya ce, “Ku tsaya, ku tsaya. Kwantad da rakuma, kwantar da sauri!” Muka kwantad da rakuma, na ce masa ko lafiya ? Ya ce, “Na hango rakuma can nesa, da dawaki biyu, na kuwa tabbata sun hango mu.”
Tir, malam, ai ba ka ji zuciyata a lokacin ba! Na ce, “Amma in har sun gam mu, ai gwamma mu yi gaba. Kwantad da rakuma zai sa su zaci wani abu.” Hamid ya ce, “Gaskiyarka.” Na dura harsashi cikin bindigata muka duka. Can sai muka hango daya daga cikinsu ya dare bisa doki, ya nufo mu a sukwane.
Na ce da Hamid, “Yi maza ka tarbi mutumin can, ni kuwa za mu yi gaba a hankali da ni da Belal. Tsaishe shi, ka ba shi amsar tambayoyin da ya ke da su, kada ka bari ya matso ni. In ya ki, ba shi ’yan kudi ya juya.”
Muka yi gaba, ina boye fuskata da rawani don kada ya ga farar fatata, ya gane ni bako ne. Muna tafiya, muna satar kallonsu, sai muka ga Hamid ya durkusad da rakuminsa. Ni kuwa zuciyata ta dauki daka. Bayan kamar minti ashirin, muka ga Hamid ya mike, suka yi ban hannu da mutumin ya juya, shi kuma ya cim mana. Yana zuwa ya ce mini, “Abdulkadir, gode wa Allah da ka tsira. Ai wannan mutumin, wani dagaci ne, abokina! sunansa Mukhal, za shi Dongola. Da saduwarmu sai ya ce ina zan tafi da farin Bamisire. Kai, wannan da kaifin gani ya ke, na yi mamakin yadda ya hango farar fatarka daga can nesa haka.” Na ce da Hamid, “To, wace amsa ka ba shi ?” Ya ce, “Na fada masa gaskiya, na ce ba Bamisire ba ne, Banasare ne. Amma na roke shi Allah da Annabi ya rufe bakinsa, na kuma kara toshe masa bakin da dala ashirin. Ka san mu Larabawa makwadaita ne. Ya kuwa rantse zai kame bakinsa in ya gamu da masu bimmu. Sabo da haka yanzu sai mu hanzarta, don mun bata lokaci."
Rana tana faduwa muna ketare duwatsun Hobegi, muka sauka muka ba rakumammu hutu kamar sa'a. Da muka nemi ci gaba, sai rakuman nan suka kasa motsawa, don gajiya. Muka kara dakatawa kamar rabin sa'a sa'an nan da kyar suka mike. Ko da muka hau, sai takawa su ke yi kyuya-kyuya, duk kuwa ba wani abu ba ne gajiya ce. A zuciyata na ce tir, ba sha’ani. Im fa rakuman nan suka kasa mana a nan, ai al’amari ya baci ke nan. Muka dai lallaba su hakanan har gindin wani dutse. Daga wurin zuwa inda sababbin rakuma ke jirammu tafiyar kwana biyu ce. Muka sauka. Ja-gabana suka ce sai a bar rakuma a nan su kwana biyu karfinsu ya komo musu. Ni kuwa suka ce bai kamata in tsaya a kan turba ba, sai suka kai ni wani dutse kamar mil ashirin daga arewa da hanya suka boye ni. Na shiga kogon dutse, Hamid ya ce, “Zauna nan babu abin da zai same ka. Nan kasarmu ce, tun muna yara muka san lungu lungu cikin duwatsun nan. Ni zan koma im ba rakuma ruwa, Belal zai kawo maka ruwan sha. Zam boye rakuman don kada ungulai su nuna inda su ke. Zauna kurum har mu dawo.” Suka tafi suka bar ni.
Bay an an dade, can wajen yamma, Belal ya komo da da salkarsa cike da ruwa. Ya ce, “Dandana ruwan kasarmu ka ji." Na karba na sha, na sha, har na koshi. Na ce yadda ruwan nan ke da dadi, Allah ya sa zuciyarmu ta yi dadi hakanan. Belal ya amsa ya ce, “Malalsh, kullu shai’in bi iradatallahi,” watau, “Ba kome, duk abu yana faruwa da yardar Ubangiji ne.” Kashegari Hamid ya komo daga wurin boye rakuma. Muka yi shawara, Belel zai tafi wurin da sababbin rakuma su ke ya zo da su, mu kuwa mu jira shi a nan har ran da ya komo. Ya tafi, bayan kwana uku sai ga shi ya komo. Ya ce ya zo da rakuma biyu da mutum biyu ja-gaba. Muka shirya, muka hau, muka mika. Ran nan muna cikin tafiya sai Hamid ya ce, “Abdulkadir, yanzu fa mun kusa rabuwa, don mun kawo inda za mu bar ka, wadansu su ci da kai gaba. Tabawa kadan nan sai Kogin Nil. Ka san a nan alkawarimmu ya tsaya. Sabo da haka sai ka tsaya nan kai, mu kuwa za mu isa bakin kogi mu dauko abokan tafiyarka. ”
Suka bar ni ni kadai, na shiga sakar zuci. Ko da ya ke tsoro na cike da ni, amma zuciya ba ta daina yawo zuwa gidammu a Turai, tana nuna mini fuskokin ’yanuwa da masoya da na kosa in gan su ba. Na kwanta rigingine ina tuna yadda zuciyar Halifa ta ke yanzu game da ni. Ni kam na tabbata na tsere wa wannan mugun ke nan har abada.
Can wajen almuru, sai ga su Hamid da mutane biyu. Muka gaisa suka ce mini, “Abokinka Ahmed Wad Abdalla shi ya ce mu zo mu kai ka bakin kogi. Shi da kansa zai ketare da kai. In ka haye za ka sami masu rakuman da za su kai ka zangon gaba. Sai ku yi sallama da abokanka su Hamid don nasu aikin ya kare !"
Muka yi sallama da su Hamid. Lalle kuwa abokaina ne wadanda ba zam mance da su ba, ba zam fasa gode musu ba har abada, ko da ya ke aikin lada suka yi. Muka rabu cikin begen juna da kyakkyawar addu’a. Sababbin ja gaba. sunansu Muhammed da Is’haku. Na tambaye su ko su ne za su kai ni zangon gaba, suka ce ba su ba ne. Masu kai ni suna can gaba. Muka nufi kogi. Na tsaya nesa, su kuwa suka dangana. Can sai suka dawo tare da Ahmed.
Ahmed yana ganina, ya rungume ni don murna. Ya ce, “Marhaban, marhaban da Saladin. Na ji dadi da ganinka yau a kasarmu. Ni ne abokinka Ahmed Ibn Abdalla, kuma ka tabbata ka tsira, da yardar Allah.” Lalle na san Ahmed tun ina gwamna. Ya kawo mini gurasa da madara na ci na sha, sa’an nan ya ja ni sai bakin kogi, amma nesa da mashigi. Aka kawo kwalekwale muka shiga muka haye. Sai na ga sun nutsad da jirgin, ashe wai duk bad da sau ne.
Wajen tsakar dare, sai ga rakuma uku. Ahmed ya hada ni da ja-gabana biyu, Ibrahim Ali da Yakub Hassan. Muka yi sallama da Ahmed muka tashi.
Akwai bambanci kwarai tsakanin ja-gabana na farko, su Hamid da Belal, da ja-gabana na yanzu, su Ibrahim Ali da Yakub Hassan. Na farkon, mutanen kirkin gaske ne, amintattu, masu niyyar taimakona. Amma wadannan ko kadan ba haka su ke ba. Suka dinga gunaguni a kan hanya, har suna zagin mai gidansu, Ahmed, da ya hada ni da su. Ran nan, ran wata Alhamis, muna cikin tafiya sai suka ja akalar rakumansu suka tsaya cik, suka ce su baya za su juya daga nan Na ce musu ina dalili ? Ashe ba an tsadance da su ne su kai ni wurin Sheihu Hamid Fadai a kasar Masar ba ? Suka ce lalle haka ne, amma suna jin tsoro, kasadar ta yi yawa. Suka ce in wannan labari ya kai kunnen Halifa, ba su kansu ba, ba ma ’yanuwansu ba, kabilarsu dungum kila kasuwa za a kai su a tsire, ko a sare kawunansu. Sabo da haka ba za su yi gaba ba.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com
http://bukarmada.wordpress.com
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada