ABDULKADIR SALADIN 05

5. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
....
Ya ce jama’a su bar karbar maganar malamai masu bin son zuciyarsu, su kuma daina jin zancen gwamnati! Ka ji farkon satirum Mahadi ke nan da gurbatar kasar Sudan. Bari mu ji yadda Muhammed Ahmed ya sami yin haka.
TASHIN MAHADI
’Yan watanni kadan da yin caffar Ahmed, sai Shaihil Kuraishi ya rasu. Mutane fa suka danka wa Ahmed shugabancin darikar Sammaniyya. Ya sami mu‘ijiza kwarai wurin masu binsa, kome ya ce musu su aikata a duniyan nan za su aikata, ko da za su rabu da ransu.
A cikin wadanda suka kai caffa gun Muhammed Ahmed, akwai wani da a ke kira Abdullahi bin Muhammad. Shi ya fada mini asirin farkon bunkasar Muhammed Ahmed, da yadda ya nada kansa Mahadi. Wata rana muna zaune, Abdullahi ya ce da ni, “Ya Abdulkadir Saladin”, watau Abdulkadir shi ne sunan da ya sa mini, Saladin kuwa shi ne maimakon sunana, Slatin, “Bari im fada maka farkon saduwata da Muhammad Ahmed. Da na shirya tafiya gare shi, sai na bi tajirai fatake har zuwa Bahrel Gazel. A can na tambayi mutane hanyata ta zuwa inda Mahadi, Muhammed Ahmed ya ke. Sai kowa ya dube ni shekeke ya ce, ‘Me za ka yi a wurinsa ? Ba zai bata bakinsa ya ce maka ko sannu ba. Wane ne kai ?’ Haka na dinga shan wannan wulakanci. Amma wadansu su kan nuna mini hanya. Da haka dai har na kai Mesalamiya, garin da ya ke. Na same shi yana fama da aikin ginin kushewar malaminsa Shaihil Kuraishi. Wallahi, Saladin, ko da na gan shi, duk wuya da wahalar da na sha, sai na manta su. Na zauna a gabansa, na dukad da kaina, ga kafafuna tankwashe. Ni dai ban sami ikon bude bakina in ce masa wani abu ba, mu’ujiza duk ta rufe ni. Sai zuwa can na yi karfin hali, na ta da ido na dube shi, na yi gaisuwa, sa’an nan na fada masa labarina, da abin da ke tafe da ni duka. Na roke shi ya karbi caffata, in zama cikin jama’arsa. Ya yarda, ya miko mini hannu muka yi masafaha na shafa. Na dauki alkawarin bin umuminsa muddin zamana na duniya, ban kuwa karya alkawarin nan ba har ranar da ya bar gidan duniya.
“Shi ke nan na shiga cikin jama’arsa. Ran nan sai ga shi har bukkata. Na tashi na ba shi shimfida, ni kuma na koma waje guda na zauna. Sai ya ce mini, ‘Ya Abdullahi.’ Na ce, ‘Gafarta malam.’ Ya ce, ‘Na zo ne im fada maka wani asirin da ba na iya fada wa kowa cikin jama’ata tukuna. In shaida maka Ubangiji ya sauko mini da wahayi ta hannun ubandakimmu Annabi, ni ne Mahadi!’ Ko kadan ban yi shakkar wannan zance ba, don ni tun ran da na fara ganinsa na yarda har cikin zuciyata, shi ne wanda mu ke sauraro, watau Mahadil Muntazir. Ka ji farkon saduwata da Mahadi ke nan.”
Idan mutum ya dubi farkon Muhammed Ahmed da talaucinsa, da yadda ba a dauke shi a bakin kome ba. Ya ga kuma yadda yanzu ya daukaka haka, ya zama kowa shi ya ke so da gani, sai ya gane gaskiyar maganar mutane da su kan ce, ‘duniya rawar ’yam mata, na gaba ya koma baya.’ Kome na duniya ba ya rasa sanadi. Ashe an nufe shi da shahara ne, shi ya sa suka bata da malaminsa, Muhammad Sherif, ya tafi gabansa da tuba har sau uku, Sherif ya ki yafe masa. Im ba domin batawar da suka yi ba, har abada Muhammed Ahmed ba ya jan batar kansa, balle har ya zama wani abu.
Abdullahi ya zama babban wazirinsa, kuma shi ya fada masa labarin yawancin kabilun Sudan. Shi ya ce masa kabilun jihar Kordofan jarumai ne kwarai, kuma da an kira su jihadi na fi sabilillahi, a guje za su zo. Sabo da haka sai ya shawarci Muhammed Ahmed, ya ce ya kamata ya nuna kansa, ga mutanen Kordofan. Suka shirya suka tashi, ga su nan, ga su nan, sai Dar Gimru, garin su Abdullahi. Nan da nan mutane suka karbe su. Amma ya ce musu lokacin fita jihadi bai yi ba tukuna. Abin yinsu yanzu sai su yi ta zuga sauran jama’a, su zauna bisa shiri har kafin wannan babbar rana ta shahada ta zo.
Daga Dar Gimru suka dunguma sai Lubayya, a can suka sadu da manyan malamai da sarakuna. Ya fada musu niyyarsa, ya ji ra’ayin kowa. Daga nan ne fa ya fara saka tubalin shirin jihadi. Ya gaya wa malaman nan da sarakunan nan cewa a yanzu kada wanda ya daga kansa, don gwamnati tana da karfi kwarai. Ya ce su dai su shiga shirinsu kurum. Daga nan ya yi gaba. A lokacin wannan rangadi, Muhammed Ahmed ya gane halayen da talakawa ke ciki, ya san lalle suna cike da gwamnati, tun dai ba wajen sha’anin haraji ba. Kowa sai kuka ya ke yi, haraji ya yi masa yawa, akwai kuma azaba da cin mutunci wajen karbarsa. Mutanen Sudan sun gaji da mulkin Masar da Turkawa, babu abin da su ke so sai su kakkabe su, amma ba dama. Turawa kuma ’yan kadan da ke aiki a kasar, karkashin gwamnatin Masar, ba dadinsu a ke ji ba. Kai, yadda a ke matsuwa duk mutanen sun matsu, ikon tawaye ne kadai ba su da shi, don ba su da karfi. Gwamna Gordon ya yi babban kuskurc da ya dauki sarauta ya ba wadansu ’yan kasuwa. Wannan ya jawo zargi kwarai da gunaguni, tumbana dai tsakanin sarakunan kasar na gargajiya. Bugu da kari kuma mu Turawa ba son bauta mu ke yi ba. A lokacin nan kuwa arizikin Sudan duk a kan bayi aka gina shi. Shekaru aru aru, bayi su ke ko wace irin hidima, su ke noma, su ke kiwo. Sabo da haka tashi tsayen da mu Turawa muka yi wajen hana kawo bayi daga kasashen Tukururu, watau Bakar Fata, da kuma 'yanta su da mu kan yi in sun kawo kuka gare mu, shi ya kara mana bakin jini.
Muhammed Ahmed ya fahinci dalilan nan duka da ke zukatan mutane, ya kuwa dauke su suka zama makamansa na shirya wa gwamnati tawaye. Ya kuma gane babu wani abin da zai jawo hankulan mutanen kasa duka wajen wannan tawaye sai addini. Yaki da sunan mulki ba zai yiwu ba, sai da sunan addini kurum. Ya kuma sani duk Musulmi suna da sanin cewa ran da addini ya yi rauni, zalunci ya yi yawa, Mahadi zai bayyana don ya tsarkake addini, ya kafa adalci. To, yanzu babu mai shakkar raunin nan na addini da yawaitar zalunci. Sabo da haka, tun da ya ke mutane sun yarda Ahmed na Allah ne, babu wanda zai yi shakka in ya ce shi ne Mahadin da a ke jira. Sabo da haka ya shelata ya ce shi ne Mahadi. Ya zo ya kore bidi’a da zalunci, ya karfafa addini da adalci. Sahihin nufinsa kuwa, shi ne ya kore Misirawa, da Turkawa, da Turawa, wadanda suka taru suka yi gwamnatin Sudan.
Jin haka sarakuna suka rasa sukuni, suka tashi tsaye bisa kashe wannan gagarumar wuta. Babban gwamnan Kahartum a lokacin, Bamisire ne, ana kiransa Abdurra’uf Pasha. Nan da nan ya kira wani wai shi Muhammed Bey Abu Sa’ud, wanda ya san Muhammed Ahmed, ya ce ya tafi Abba maza ya zo masa da Mahadi. Kafin Abu Sa’ud ya zo, mutanen Muhammed Ahmed sun gaya masa kada ya yarda ya tafi Kahartum, don lalle Muhammed Sherif tsohon malaminsa, kuma babban makiyinsa, ya yi masa tarko. Ko da Sa'ud ya zo, Abdullahi ya dauke shi sai wurin Muhammed Ahmed. Sa’ud ya ce surutai na karairai sun watsu, cewa Ahmed yana neman sa mutane su yi wa gwamnati bore. Sabo da haka shugabansa gwamnan Kahartum ya aiko ya je ya fid da kansa daga zargi. Da jin haka Muhammed Ahmed ya yi zumbur ya tashi, ya mara kirjinsa ya daka wa Sa'ud tsawa ya ce, “Kai! In tafi ina ? Bisa ikon Ubangiji ni ne shugaban Sudan dukanta, har abada kuwa ba na zuwa Kahartum don in fadi wata magana a gaban wani mutum !"
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)