ABDULKADIR SALADIN 06

6. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
https://bukarmada.blogspot.com/
...
Jin haka sarakuna suka rasa sukuni, suka tashi tsaye bisa kashe wannan gagarumar wuta. Babban gwamnan Kahartum a lokacin, Bamisire ne, ana kiransa Abdurra’uf Pasha. Nan da nan ya kira wani wai shi Muhammed Bey Abu Sa’ud, wanda ya san Muhammed Ahmed, ya ce ya tafi Abba maza ya zo masa da Mahadi. Kafin Abu Sa’ud ya zo, mutanen Muhammed Ahmed sun gaya masa kada ya yarda ya tafi Kahartum, don lalle Muhammed Sherif tsohon malaminsa, kuma babban makiyinsa, ya yi masa tarko. Ko da Sa'ud ya zo, Abdullahi ya dauke shi sai wurin Muhammed Ahmed. Sa’ud ya ce surutai na karairai sun watsu, cewa Ahmed yana neman sa mutane su yi wa gwamnati bore. Sabo da haka shugabansa gwamnan Kahartum ya aiko ya je ya fid da kansa daga zargi. Da jin haka Muhammed Ahmed ya yi zumbur ya tashi, ya mara kirjinsa ya daka wa Sa'ud tsawa ya ce, “Kai! In tafi ina ? Bisa ikon Ubangiji ni ne shugaban Sudan dukanta, har abada kuwa ba na zuwa Kahartum don in fadi wata magana a gaban wani mutum !"
Jikin Sa’ud sai ya dauki kadawa, ya shiga shafar Muhammed Ahmed, yana ba shi magana. Ko da ya sami ’yar kafa sai ya sulale, ya garzaya sai Kahartum. Ya kwashe yadda aka yi ya fada wa Gwamna Abdurra’uf duka.
Muhammed Ahmed fa ya ga babu sauran wata Kumbuya kumbuya kuma. Babu abin da ya rage sai ya tashi tsaye ya shiga jidali da gwamnati, ko kuwa su kama shi. Ya ko sani da kama shi da kisa, duka daya ne. Sabo da haka ya shiga aikawa da takardu ko ina cikin Sudan, fadinta da tsawonta, yana kiran jama’a su daura niyyar shahada. A Kahartum kuma Abdurra’uf Pasha ba kwance ya ke ba. Tun ran da Sa’ud ya komo ya ba shi labarin yadda suka yi da Muhammed Ahmed, shi kuma saiya kira manjojin kamfanin soja biyu, ya ce su je su kamo masa wannan mahaukaci. Don ya kara musu himma, ya ce duk wanda ya kamo Muhammed Ahmed, nan da nan za a kara masa girma. Amma wannan dabara maimakon ta yi amfani, sai ta kawo kishi da barna tsakanin manjojin nan biyu. Abin dai ya kai har da gwabzawa, da zubad da jini.
Labari ya isam ma Muhammed Ahmed, cewa ga sojan gwamnati nan tafe. Sabo da haka shi kuma ya shiga tara nasa baraden. Ya Shiga kunna wutar jaruntaka a zukatansu, har ya ce ya ga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cikin mafarki, ya gaya masa duk wanda ya shiga cikin wannan jihadi, za a ba shi darajar Sidi Abdulkadir Jailani, sarkin waliyai. Musulmi fa in ya ji haka, malam, ina damar tsayawa ? Amma da ya ke an yi latti, irin mutanen da suka zo suka ba da ransu da dukiyarsu kadan ne.
Jirgin ruwan da ke dauke da sojan gwamnati dai ya iso Abba, garin Muhammed Ahmed. Aka sauke soja da almuru, wata kuwa ya shiga duhu. To, da ya ke tun can farko, manjojin kamfunan sojan nan ba shiri su ke da juna ba, ko da suka iso sai wannan ya yi gabas, wannan ya yi yamma. Ba su ko tsaya sun hada shawara ba, su kuwa ba sanin tsibirin suka yi sosai da sosai ba. Suka dai tasam ma inda Muhammed Ahmed ya ke. Shi Muhammed Ahmed kuwa da jin an ce soja sun sauka, ya kwashi mutanen kauyen duk suka shiga sunkuru suka buya, kowa da irin nasa makamin. Wadansu da masu, wadansu kibau, wadansu kulake, wadansu takubba. Suka dai bar kauyen babu kowa, hatta mata da tsofaffi da yara sun kwashe.
Sojan gwamnati fa suka bullo wa garin ta fuska biyu, gabas da yamma. Ko wane Kamfani manjonsu yana kumin ya riga dan'uwansa kama Muhammed Ahmed don ya sami karin girma. Zuwa can sai kamfani guda ya bude wuta. Da daya kamfanin ya ji, sai ya zaci jama'ar Muhammed Ahmed ne, shi kuma ya bude wuta. Suka dinga zuba wa junansu harsashi, ba su sani ba, ashe kansu su ke ta kisa. Zuwa can da suka kusa hallaka juna, sai Muhammed Ahmed ya raba jama’arsa biyu, rabi suka yi kabbara suka fada wa ’yan sauran sojan kamfanin gabas, rabi kuma suka fada wa na yamma. Suka same su suka yi musu kaca-kaca. Suka yar da bindigogin, kowa ya kama gabansa. ’Yan kadan suka kai wurin jirgi da kyar. Asuba na yi, jirgi ya juya sai Kahartum.
Wannan nasara da Muhammed Ahmed ya samu a kan sojan gwamnati ya fito da shi fili, ya kuwa firgita gwamnati kwarai. Wadanda ba su yarda da shi ba suka yarda, masu shakka suka daina, abokan gabansa suka shiga tsoro. Amma duk da haka ya sani gwamnati za ta yi babban shiri ta auka kansa. Abdullahi ya shawarce shi, ya ce ya kamata ya nisanta kansa daga Kahartum.
To, don kada a ce gudu ya yi, sai ya sa aka yi shela ya ce wai ya sami wahayi an ce ya koma Dutsen Masa, a kudancin Kordofan, don a can ne za a rika aiko masa da aikin da zai yi daga sama. Kuma an umurce shi cikin wahayi ya nada halifansa. Na farkonsu shi ne Abdullahi, na biyu Ali Wad Helu.
Da suka kare shiri, suka tashi. Ko ina suka ratsa sai sun kwashi mutane. Kasa dai ta faso zuwa gare shi. Labarai irin na karya suka watsu, cewa ga Mahadi ya bayyana, yana iya yin kaza da kaza da kaza. Jahilai fa suka yarda, suka tashi har iyalansu suka bi shi, su sun sami ubandaki! Wata rana ya sauka yana hutawa da 'yam mutane kadan, ayari kuwa na gaba. Bai sani ba ashe yana kusa da kamfanin sojan gwamnati ne mutum sittin, masu karbar haraji. Babbansu ana ce da shi Muhammed Guma, ya yi shawarar fada masa, amma bai sami iznin haka ba daga manyansa. Sabo da haka sai ya yi maza ya aika Lubayya neman izni. Kafin amsa ta zo, Mahadi ya tarad da ayarinsa, sun dunguma. Ba don neman iznin nan ba, da an yi ta ta kare a ran nan.
Wata rana da muka sadu da Muhammed Guma, yan a cikin wahala a Ondurman ya ce mini, “Ya Saladin, ai da na san haka za ta kawo ni, in rika tafiya babu ko takalmi, ina baran abin da zan ci, da ban aika neman izni ba. Sai in kashe lalataccen shedanin nan. Barinsa ya tsere shi ya jawo mini wannan ukuba.”
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)