ABDULKADIR SALADIN 07

7. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Wata rana da muka sadu da Muhammed Guma, yan a cikin wahala a Ondurman ya ce mini, “Ya Saladin, ai da na san haka za ta kawo ni, in rika tafiya babu ko takalmi, ina baran abin da zan ci, da ban aika neman izni ba. Sai in kashe lalataccen shedanin nan. Barinsa ya tsere shi ya jawo mini wannan ukuba.”
GWAMNATl TA KAMA FA'DA DA MAHADI
Wutar Mahadi a kullum sai kara habaka ta ke yi. Mutane sai kara rufo masa su ke, a kullum karfinsa karuwa ya ke yi. Sabo da haka gwamnati ta ga zama kurum ba zai yiwu ba. Nan da nan aka shirya soja dubu hudu, aka danka su a hannun Yusuf Pasha Shellali. Shi shahararren jarumi ne wanda ya kware wajen shirya yaki. Runduna ta dunguma ta nufi yamma dauke da bindigogi, da igwa, da akwatunan harsashi. Ga su nan har suka kai Mesat kusa da Jebel Gedir, inda Mahadi ya ke. Yusuf Pasha, Muhammed Bey, da Abu Sidri, manyan kwamandodin yakin, sun tabbata idonsu idon Mahadi, za su yi kasa-kasa da shi. Me suka rasa? Ga dai makamai irin na zamani, ga gwanayen soja kosassu, wadanda suka san aikinsu. Shi kuwa Mahadi ba shi da kome sai mashi, da kibiya kawai. Kuma mutanensa ba soja ba ne, ba su da ilmin yaki, kuma ba su da koshi. Amma a cikin mayakan gwamnati, akwai wani dan camfi wai shi Abdalla Wad Dafalla. Shi kadai ne ya ce musu kada su saki jikinsu, ba su san irin karfin abokin gaba ba. Da aka tambaye shi dalilin cewa haka, sai ya ce shi dai yana shakkar sa’a a wannan fitowa tasu, don ya fadi daga dokinsa a kofar Lubayya. Wannan ya nuna alamar rashin sa’a ne. ’Yanuwansa suka yi dariya, sun ji zancen camfi!
Suna nan a sansani sun saki zuciyarsu cewa babu wani abin tsoro, suna ta shara barci. Can da asubahin fari, sai ga rundunar Mahadi sun wo kabbara a kansu da masu da asigiri, suka yi ta kisa. Yusuf Pasha da Abu Sidri nan aka tsire su da tsinin mashi. Kafin dai kyiftawa, cikin mutum dubu hudu, wadanda suka rage ba su fi a kidaya ba. Dan camfln nan Abdalla Wad Dafalla shi ne ma kadai ya dan turza, amma kafin wani lokaci, ko shi ma ya tafi lahira. Duk cikin rundunar, wata mace kwarkwarar Abu Sidri, ita ce ma kadai ta nuna jarunta. Ta fito a guje daga tantin mijinta da libarba a hannu, har ta kashe mutum biyu cikin mutanen Mahadi. Kafin ta harba harsashi na uku, an raba kirjinta biyu da mashi, gawarta ta fadi a kan gawar mijinta!
To, malam, ka san yadda al’amari kan zama im bakon abu, wanda ba a zato, ya faru a kasar da jahilci ya yi kauci. Mutane ba su kula da abubuwan da suka kawo abin, sai su ce Allah ne ya kaddaro shi haka. Sabo da haka wurin mutanen Sudan, babu yadda za a ce ’yam mutane kadan, huntaye, masu kibiya da masu kurum, za su iya kashe soja dubu hudu masu igwa da bindiga, im ba domin Allah yana bayan Mahadi ba. Shekara sittin Masar da Turkawa suna mulkin Sudan, suna yin yadda suka ga dama, Ubangiji bai kula da su ba. Amma yanzu da zaluncinsu ya shaddada, ga shi Ubangiji ya kawo mai korarsu. Sabo da haka wanda ma ya yi shakkar cewa Muhammed Ahmed ba shi ne Mahadi ba, kafiri ne.
Nasaran nan da Mahadi ya samu a kan Yusuf Pasha ta saka duk kudancin Kordofan a hannunsa, bayan ganimar kudi, da makamai, da dawakin da ya kwasa ba iyaka. Duk abubuwan nan bai kula da ko daya ba, balle a ce dukiya ya ke nema. Sai ya raba wa sarakunan yakinsa, da mutanensa kurum. Labari fa ya bazu ko ina, yana kara nisa ana kara masa gishiri, ana kumbura shi, har ya zama kamar almara. Talakawa duka suka yi wa gwamnati tawaye, kowa sai wasa mashi da takobi, yana shafa wa kibau dafi, yana jiran kiran Mahadi.
* * *
Mahadi al’amarinsa sai kara haskaka ya ke. Duk inda ya kara da gwamnati ka tarar nasara gare shi ta ke. A lokacin kuma ya sami babban bafade da suka bata da gwamnati, ya goyi bayansa, ana ce da shi Elis Pasha. Mutumin nan shi ya yi ta zuga Mahadi, sai dai ya zo Lubayya ya kama garin. Mahadi kuwa ya shiga wannan zuga, ya daura niyya ya zo ya kewaye garin kaf. Mutane dubbai suka yi wa garin kawanya, ba shiga ba fita. Sai ya rubuta wa gwamnan Lubayya, Muhammed Pasha Sa’id, ya ce ya ba shi zabi, ko dai a zaune wa garinsa haka, har wahala ta sa mutane su bi, ko kuwa ya nemi sulhu. Muhammed Sa'id ya tara sarakunan yakinsa ya karanta musu wannan takarda. Sai sarakunan yakin nan suka shiga zage-zage, wai wannan raini ne, har ma bai kamata a bar wadanda suka kawo takardar da rai ba. Nan da nan aka sa bindiga aka raba manzannin nan da ransu! Ganin haka fa Mahadi ya sami bukatarsa. Ya sa aka yi dabur, sansani ya taru, ya fada musu yadda ya aika da takarda ya ba da sulhu, amma gwamnan Lubayya ya kama jakadunsa ya yanka. Ya shiga yi wa jama'arsa wa’azi, yana ce musu, su daura niyyar jihadi. Kowa ya fadi a wurin jihadi, makoma tasa aljanna! Mutane sun yarda da magana tasa gaskiya ce, sabo da haka duk suka dauri aniya. Ran nan, ran 8 ga Satumba, rundunar Mahadi mai kama da da ta dango, ta dunguma ta nufi gari. Idon mayakan nan ya rufe, romon bakan Mahadi ya huda su. Wurinsu ma, gwanda mutuwa da rayuwa, tun da ya ke in am mutu aljanna za a, ba tsaitsayawa. Ba su da wani makamin da ya wuce takubba da masu, sai fa ban gaskiyar da ke kirjinsu. A kwarin ganuwar gari kuwa ga sojan gwamnati cikin lambatu, ko wanne ya dafe mai ruwa, sai ruwan harsashi su ke zuba wa Mahadawa, suna ta zuba kasa kamar dinya ta nuna. Amma duk da wannan ko kadan ba su ma san ana kashe su ba, sai gaba su ke turawa kurum. Kai, zuwa can dai wuta ta yi wuta, sai Mahadi ya janye mutanensa zuwa gindin wani dutse. Ya san rana ta baci masa.
Kusa da inda Mahadi ya ke, nan Delen ya ke, garin mishan da na ba da labarin na ziyarta, tun farkon labarin nan. Mahadi fa kyanwa ta sami bera. Nan da nan ya sa bawansa ya ce ya debi mutane su tafi Delen, su kamo mishan din nan mazansu da matansu. In sun ki kamo, a zo da kawunansu. Shugabannin mishan din, da Joseph Ohrwalder da Luigi Bonomi suka dan cije da farko, da suka ga abin ba da wasa a ke ba, suka wuce gaba, aka tasa keyarsu sai gaban Mahadi. Aka washe su karkaf, sa'an nan aka matsa musu su musulunta, amma suka ki. Ran nan sai aka tara musu wajen mutum dubu, yara da manya, suka bi bayansu suna musu eho har bakin kasuwa. Su da a zatonsu kasha su za a yi, ni ma haka, amma Mahadi bai kashe su ba. Sai ya ce ya bar su cikin addininsu, amma kamammu ne su. Sai ya danka su a hannun wani kwara wai shi George Stambuli wanda ke tare da Mahadi.
TAURARUWA MAI WUTSIYA
A cikin wannan lokaci na hargitsi da shakka, sai ga wani abin mamaki ya faru, wanda ya taimaki Mahadi kwarai. Ana zaune kurum ran nan, sai ga tauraruwa mai wutsiya fal ta fito. A wurin mutanen Sudan, wannan babbar alama ce ta nuna faduwar gwamnati, kuma lalle Mahadin gaskiya ya zo duniya. Ana cikin wannan zato, sai gwamnati ta turo soja dubu biyu don su taimaka wajen tsare Lubayya. Daga ciki, bayan an gwabza a Bara, dari kadai suka sami komawa gida su kai labari. Igwa dari aka buga don murnar faduwar Bara.
Sojan Lubayya suka dai dage, suka tsare garin wata biyar, har dai aka kai magaryar tukewa. Abinci ya yi wuya a garin, kwai kurum guda daya, ya kai har sule uku. Duk bayan wuyar abinci, ga soja sai mutuwa su ke yi a kullum. Tilas Muhammed Sa’id Pasha ya dauki takarda, ya rubuta wa Mahadi cewa ya bi, ga gari nan ya shigo ya kama. Mahadi ya mai da amsar cewa, yana so ya ga Muhammed Sa'id Pasha da manyan jarumawansa, da manyan gari, su hadu gobe a shirya sulhu. Gari na wayewa. Muhammed Sa’id Pasha ya kira kwamandan soja, Muhammed Bey Skander, da Manjo Nesin Effendi. suka nufi sansanin Mahadi a bayan gari. Suka same shi yana zaune a kan buzun rago, ga jama'a suna kewaye da shi.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)