ABDULKADIR SALADIN 08

8. ABDULKADIR SALADIN​
Na Alhaji Nuhu Bamalli
http://bukarmada.blogspot.com/
....
Gariwayewa. Muhammed Sa’id Pasha ya kira kwamandan soja, Muhammed Bey Skander, da Manjo Nesin Effendi. suka nufi sansanin Mahadi a bayan gari. Suka same shi yana zaune a kan buzun rago, ga jama'a suna kewaye da shi.
Ya karbe su da murna da fara’a, amma ya ce ba su kyauta masa ba, da suka kashe manzanninsa da ya aiko. Ya ce wannan ba kome, ya yafe musu.
Ashe Mahadi ya shirya manyan mabiyansa a boye, ya ce su yi maza su je su gaje gidajen manyan sojojin gwamnatin nan, su kwashe dukiyarsu karkaf. Da zuwan mutanen suka shiga waso. Suka bincike gidan Muhammcd Sa’id Pasha babu ko anini. Aka sa Ahmed Wad Sulaiman, watau ma’ajin daular Mahadi, aka ce ya tambaye shi in yana da kudi ya bayar a zuba a baitulmali. Muhammed Sa'id Pasha ya ce shi ko taro ba shi da shi. Nan kuwa kowa ya sani tajirin gaske ne. Sabo da haka Mahadi ya ce a matsa wa yaransa da tambaya, sai sun nuna inda ya boye. Can da matsi ya yi matsi, sai wata kuyanga tasa ta nuna wani katon ginshiki a dakinsa, ta ce a fasa, kudi na nan. Nan da nan aka rabo aka rada wa Mahadi, ba tare da sanin Muhammed Sa’id Pasha ba. Mai nema a duhu, balle ya samu da rana! Da ma Mahadi bukatarsa ya nuna karama ne, to, ga hanya ta budu.
Sabo da haka sai ya kira Muhammed Sa’id Pasha ya ce, “In kana da kudi fito da su.” Muhammed Sa'id Pasha ya yi tsalle waje guda ya ce Allah ya kashe shi, ba shi da wuri. Mahadi ya ce, “Kai dai fadi gaskiya.” Muhammed Sa’id Pasha ya ce ba shi da wuri. Mahadi ya ce, “Lalle kuwa ashe gaskiya ne da aka ce kudi su ne asalin bakin ciki duka. Ga shi yanzu ka rantse a kan karya, bayan kuwa kana da kudi. To, zan nuna maka ni Mahadi ne, ina ganin gaibin da idon mutum kurum ba ya gani. An nuna mini akwai dukiya tana nan dankare, ka binne a gidanka. Ina Ahmed Wad Sulaimanu, ku tafi gidan mutumin wofin nan, ku sare ginshikin shigifarsa kudi na nan ku kwaso." Aka tasa keyar Muhammed Sa’id Pasha sai gidansa, ko da aka bugi ginshikin da diga, sai ga akwatin karfe na kudi ya fado bif. A bude sai ga kudi ja zir, har £7,000. Mahadi ya ce, “Muhammed Sa'id ka yi karya, amma na yafe maka. Ahmed, tafi da kudin nan ka zuba a baitulmali a raba wa fakirai da gajiyayyu. Kai kuwa Sa’id, tafi ka ba ni wuri. ‘Di ma biyenfa ma’ana.’ Watau ‘Ba ka cikin irin jama’armu.’ Ta haka aka kwace wa Muhammed Sa’id Pasha kudinsa, daga baya ma har aka kashe shi.
Ni na sani, tun da mutanemmu suka ga tauraruwa mai wutsiya, suka kuma ga irin sa’ar da Mahadi ke yi, lalle samun gwamnati ta yi nasara, sai an yi da gaske. Ko a cikin sojammu akwai mutane dubbai da suka ba da gaskiya, cewa Mahadi na Allah ne, kuma karfin Zati yana tare da shi. Amma duk da haka ni ban nuna alamar karaya ba, kuma a kullum ina feshin cewa wannan Mahadi, dan tarzoma ne kurum, mai son mulkin duniya, su bar gaskata shi.
Ran nan da yamma, muna zaune a sansani, sai ga labari wai ga wani nan an hango shi ya nufo sansanin da farar tuta, ya ce daga Mahadi ya ke yana neman sulhu. Da ya ke ba na so ya shiga sansani ya ga yadda mutane da yawa ke da rauni don kada ya koma ya ba da labari, sai na tare shi a kofa. Ko da na karbi takardar, sai na ga daga wurin Moddibo ne, wanda ke iko da kasar da muka sauka a ciki. Modibbo ya firgita kwarai, don cewa ya yi, ya kamata in nemi ysulhu da Mahadi. Ban zarge shi ba, don shi ba soja ba ne, yaki bakon abu ne gare shi. Ya ce a takardarsa, ga Mahadi nan ya yad da mashi a kofar Lubayya, ya kuwa tabbata garin zai shiga hannunsa nan da nan. Ya ce in na yarda na tafi inda shi Modibbo ya ke, lalle zai kai ni gun Mahadi, ba tare da tashin hankali ba. Da na kare karantawa, sai na juya gun dan sakon na ce masa da karfi, ya koma ya fada wa Modibbo, cewa Ubangiji ne ya nufe mu da shan wuya, amma wuya ba mutuwa ba ce. Mun sani muna cikin yankin kasarsa ne, amma im ba ya sommu da yaki ne, tilas ya zuba ido kurum, don ba za mu fasa ba. In kuwa ya bi Mahadi ne, don ya shiga aljanna, to, ya zo nan gobe mu gamu. Da ma muna shirin tashi, amma sabo da shi mun fasa, muna jiransa. Manzo dai yana tsaye, sai cewa to kurum ya ke, duk ya kosa ya bar sansanin.
Kashegari sai muka sami labari, Modibbo yana kusa, tare da runduna mai yawa. Amma bai taba mu ba.
Mu kuma da jin haka muka tashi muka ci gaba, muka nufi Dara.
Duk cikin wannan gwabzawa da a ke ta famar yi, Allah bai nufe ni da rasa raina ba, sai dai na sha azabu iri iri. Da farko dai, harsashi ya cire mini yatsar hannu gudu, ya karya mini kashin cinya, an kuma sare ni da takobi a gwiwar dama. Amma duk wannan ba su hana ni ci gaba da yakin ba.
Muna cikin haka, sai wani shaidan ya haddasa kiyayya tsakanina da hafsoshin da ke karkashina. Labaran karya suka dinga zuwa, wai gwamnatin Masar ta sallame ni daga aiki, rashin hanya ne kurum ya sa takardar korata ba ta iso gare ni ba. Jin haka fa ’yanuba suka ce bismilla. Suka shiga zuga soja bisa kin karbar umurnina kwarai da gaske. A da, in na gitta kara babu mai ketarewa, amma yanzu in na ba da oda, sai juya baya a ke, wadansu har su yi mini eho. Ni kuwa ko kadan hankalina bai tashi ba, don na san aikin ’yanuba ne. Na rike wani karin magana na Larabawa da su kan ce, “Rakumi bai kula da haushin kare ba."
Ran nan ina zaune ina rubuta odojin da zam ba hafsoshina, sai ga wani mutumin Dara, wai shi Abdurrahman Wad Sherif, ya zo yana haki. Na ce masa ko lafiya ? Ya ce, “Ai babu lafiya, domin Lubayya ta mika wa Mahadi wuya, ya ci garin !“ Wannan labari lalle ya dagula mini rai ainun. Ya ce yana tsaye lokacin da kwamanda mai tsare da Lubayya ya fito, da farar tutarsa a gaba, ya nemi sulhu gun Mahadi.
Da ya kare, sai na tara manyan mayaka da ke cikin rundunata, watau Darho da Sulaiman Basyuni, na fada musu wannan mummunan labari. Na sani barin kashi a cikin ba ya maganin yunwa. Boye wannan labari aiki banza ne, don kuwa lalle zai iso kunnen mutanemmu. Na tabbata wannan labari zai yi dadi ga wadanda kc kin gwamnati a boye. Bayan ’yan kwanaki kadan fa labarin faduwar Lubayya ya watsu a kasar Sudan duka, masoyan Mahadi sai kyarma da ruba su ke yi. Ko wane gari dattijai sai taruwa su ke suna kulla shawara, da haka dai shawara ta zauna, cewa duk kasar sun goyi bayan Mahadi, za su yi wa gwamnati tawaye.
Da ya ke ni kadai ne Bature ma’aikacin gwamnati a cikin wannan bakuwar kasa, kuma a tsakiyar munafukai na ke, masu kulle-kulle​, sai na ga ba abin da ya kamata in yi, sai in nemi sanin abin da a ke ciki ta ko wace hanya. Wani lokaci da kudi na kan nemi labari a boye, wani lokacin da toshiyar baki, ta kyautar abubuwa. Da taimakon yarona da na zaba, da wadansu karuwai masu dafa giya, na sami ’yan labarai da suka taimake ni. A gidan giyan nan, da gidan karuwai, nan a ke samun labarin da ba ya samuwa ta wata hanya. Mashayi in ya bugu, babu abin da ba ya fada, acikin sokana, har sai a ciri gaskiya daga bakinsa. Yarana sun gaya mini, cewa ko da ya ke mashayan nan ba su kula da Mahadi ba, don galibinsu daga arna ne sai ’yan iskan Musulmi, amma akwai abu guda wanda duk sojan da ke tare da ni suka gaskata. Sun ce ko da ya ke suna sona, amma dai sun tabbata ba wani abu ke sa mu shan kashi haka wurin yaki ba, sai domin ni Kirista ne. Ka ji aikin magabta! Na tabbata wannan makircin Turkawa ne da Misirawa, don dai sojana su ki ni.
Ran nan dai tura ta kai bango. Yarana sun dawo daga wurin sha, sai suka zo gare ni suka ce wai an yi shawara a gidan giya an shirya duk soja za su watse.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)