ABDULKADIR SALADIN 09

9. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Ran nan dai tura ta kai bango. Yarana sun dawo daga wurin sha, sai suka zo gare ni suka ce wai an yi shawara a gidan giya an shirya duk soja za su watse.
Nan da nan na shiga binciken mafarin wannan bakin al’amari, sai na tarar ashe kune kulle-kulle​n hafsoshina ne Turkawa. Sun ce muddin aka bar Ingilishi suka yi kafi a gwamnatin Masar, lalle mulkin Turkawa a Masar ya kare ke nan. To, an ce in kana gudun sata, ba barawo ajiyar kayanka. Sabo da haka sai na aika aka kira Manjo Muhammed Effendi Farag, na fada masa abin da na ji. Nan da nan sai na ga fuskarsa ta sake, ya yi sanyi. Ya ce zai bincika ya ji mafari. Na kuma kira yarona na ba shi kudi na ce ya kai wa matan nan mai dafa giya, ya gaya mata ta binciko mana sahihin labarin nan a wurin mashaya, bayan sun bugu. Na ce ya gaya mata ta kira kowa da kowa dina, ta ba su giya kyauta, kuma ta samam ma yarona wani dan lungu a gidan ya buya, don ya ji abin da su ke fada. In ta yi haka lalle kuwa zam ba ta lada mai yawa.
Kashegari na sami labarin abin da ya faru a gidan giya. Sai na kira Manjo Muhammed na fada masa sunayen mutum shida, na ce ya kamo su, don su suka shirya wannan makirci. A cikinsu da saje guda, kofur kofur uku, da laskofur biyu. Na tambaye su dalilin shirya wa gwamnati tawaye, amma suka tsaya kai da fata, suka ce su faufau ba su san wannan magana ba. Na ce, “Amma na sani lalle kuna taruwa a boye kuna hasa wuta, a gidan Hadiza mai giya. Kullum ina jin duk abin da ku ke ciki, kyale ku na ke yi don kila kwa iya gane wautarku ku daina. Amma sai kara haukata ku ke. Jiya Hadiza har kiranku dina ta yi musamman ta ba ku giya kyauta, don ku ji dadin tuntsurad da mulkin Masar. Kun shirya, jibi ne za ku yi tawaye. Niyyarku ku bude kofar taska ku kwashi makamai, ku tafi ku yi caffa gun Sultan Abdullahi, masoyin Mahadi. Kai Saje Muhammed, ashe jiya ba ka ce kana da mutum metan wadanda za su bi bayanka ba ? Ka ce mana. Kun ga ashe gardama ba ta da wani amfani, don na san abin da ku ke ciki.”
Da dai suka ji na san asirinsu duka, sai suka amsa laifinsu suka nemi gafara a gare ni. Na ce da su, “Ai maganar yafewa ta fi karfina, sai ku je gaban shari’a, abin da ta yi shi ke nan.” Na gaya wa Manjo Muhammed ya tafi ya shirya majalisar shari'ar soja, ya hallaro duk hafsoshi, amma ya fada musu cewa, sauran masu hannu a wannan laifi kada su tsorata. Ba za a taba su ba. Nan da nan aka shiga bin magana. Masu laifi suka amsa laifinsu. Da azahar sai aka kawo mini irin abin da shari’a ta gani, sai dai ba ta yanke hukunci ba. Sai na ce a koma shari’a ta yanke hukunci. Jimawa kadan sai aka komo mini da takardar shari'a ta hukunta wa masu laifin nan kisa, amma ta rokam musu rangwame gare ni. Ga dara ga dare ya yi. Ni da ke cikin bakin jini, ga ni yau zan tabbatad da kisan soja. Bayan na yi tunani, sai na ga babu hukuncin da zai kashe makircin nan sai kisan. Sabo da haka bisa tilas, na dauki alkalami na sa hannu ga takardar shari'ar, na tabbatad da kisan 'yan tawayen nan.
Nan da nan aka yi begilar dabur, soja duk suka taru a filin kofar sansani. Aka haka kusheyi shida. Aka kawo mutanen nan shida. Ko wanne daga cikinsu babu wanda fuskarsa ta sake, kamar dai za su gidan Hadiza mai giya ne a lokacin, ba lahira za su ba. Aka tasa su a gaba sai bakin kusheyin, ko wanne ya tsaya a bakin gidansa na karshe. Bayan sun yi salla raka’a biyu, sun yi kalmar shahada, aka ba soja oda suka harbe su, nan take suka mutu. Aka ja aka binne. Sai na juya ga sauran soja na ce musu, “To, gani ga wane fa, ya isa tsoron Allah. Duk wanda ya yi laifin ta da hargitsi ko tawaye, don ture mulkin kasa, ga irin abin da zai faru gare shi. Amma ni ba bukatana ba ke nan. So na ke a zauna lafiya bisa kaunar juna da taimakon juna." Da na kare aka ba soja odar abotai, suka juya suka koma sansani.
Bisa gaskiya, lalle ko ni zuciyata ta baci da kashe mutanen nan. Amma babu wani abin da zan yi dabam. Da aka jima sai na yi kiran Manjo Muhammed na tambaye shi, ko ya ga alamar wannan abu ya kada sauran soja, kuma ko sun gane adalcina wajen yafe wa sauran wadanda ke cikin laifin. Ya ce sun kadu. Zuwa can na ce da shi, “Kai Muhammed Effendi, abin da na ke so da kai, shi ne ka tsaya tsakaninka da Allah ka fada mini gaskiya. Na tabbata kai mai kaunata ne, shi ya sa har na ce ka zo mu yi hira mu biyu. To, ina so ka fada mini yaya hafsoshi da soja ke rike da ni a ransu ? Fada mini gaskiya!” Sai ya gyara zama ya ce, “Ko da ya ke suna kukan ka cika matsa musu, amma ba su kinka, don kuwa kana biyansu kudinsu cikin lokaci ba kamar da ba. Kuma suna yaba maka kirki wajen rabon ganima, amma bana da mu ke ta shan kashi, sun fara gundura da yaki.”
Na ce masa, “Amma tilas ne mu yi yaki. Ba neman girma, ko suna, ko samu, ke sa ni fitowa zuwa yaki ba. In don ta ni ne, na fi son in huta.” Manjo Muhammed ya ce, “Hakika na san hakanan, amma wannan hasara ta yi wa mutane yawa. Wani ya rasa dansa, wani ya rasa ubansa, wani kane, wani wa, wani aboki, wani mata. To, im fa wannan ya dore, lalle mutane za su ture su ki yaki.”
Na ce masa, “Lalle ni ma na san haka. Kuma ko da ya ke ban rasa uba, ko da, ko wa, ko mata, ko kane ba, amma na rasa abokai. A kullum ina sai da nawa ran, duk inda yaki ya yi zafi ina wurin. Yadda harsashi ke iya kashe su, haka ya ke iya kashe ni." Sai ya ce, “Su ma hafsoshin da soja sun san haka, amma sai ka gode musu tun da suka yarda suna sai da ransu tare da bako." Na ce, “Lalle kam ni bako ne, Bature kuma, ba na musun haka. Watau abin da su ke ki ke nan, su karbi umumi daga bako ? Na roke ka kada ka boye mini kome.” Sai ya sake gyara zama ya dube ni karr a ido, ya ce, “Gaskiya ka ke so in gaya maka ? To, ba suna kinka don kana bako, ko Bature ba ne, suna kinka don addininka ne!” Ko da ma tadin da na ke so a tabo ke nan, sai na ce masa, “Ashe ? To, ai kuwa duk zamana a Darfur sun san ni Kirista ne, amma ba su nuna mini kiyayya ba." Manjo Muhammed ya ce, “Af, ai jiya ba yau ba ce. Wannan lalatacccn Badongwawali da ke kiran kansa Mahadi, ya riga ya saka tsoronsa a zuciyar mutane. Yanzu dai a wurin sojammu, duk aikin banza ka ke, babu yadda za mu ci nasara a wannan yaki na jihadi, tun da ya zamana kai Kirista ne. Sun ce ko wane yaki ka shugabanta, ka dinga hasara ke nan, har a kai ran da kai ma za a kashe ka, ko a kama ka. Kuma ka san gaskata shirme irin wannan ba wuya ba ne ga sojan da su ke jahilai. Har yanzu ba su gane abin da ke sa mu shan kashi, shi ne Mahadi ya fi mu karfi ba, kuma babu damar mu karo mutane da makamai. Su dai sun tsaya a kan cewa don kai Kirista ne, shi ya sa mu ke rasa sa’a !"
Na ce, “Watau da a ce zan zama Musulmi yanzu, a wurin mutanemmu wannan zai sa musu karfin zuciya ?" Manjo Muhammed ya ce, “Lalle zai sa, kuma za su yarda da kai, tun dai ba su ga kana girmama addinimmu ba. Amma kana iya canja addininka don wannan, tun da ba ka ba da gaskiya da shi ba ?" Na ce masa, “Muhammed Effendi, kai fa ba jahili ba ne. Sai a ture maganar ban gaskiya waje guda. Ko da ita duniya ai haka ta ke, wata rana tilas ka karbi abin da bai yi maka dadi ba, ka kuwa hakura da shi dole. In dai har soja za su yarda su bi ni da zuciya daya, ai shi ke nan. To, amma yanzu wannan al’amari sai ka bar wa cikinka, kada ka fada wa kowa. Ka tafi gida. Mu kwana Iafiya.” Muhammed Effendi Farag ya fita ya bar ni cikin kogin tunani. Zuwa can dai na tsayad da shawara, na yi niyyar gobe da safe ba zan tafi gaban sojammu ba sai ina Musulmi. Na tabbata yin haka zai kawo mini kura bisa kaina, har zai sa wadansu su kini a duniya. Amma dai na yi niyya, mai cewa kome ya je ya ce, ban damu ba. Wannan shi ne zai yi maganin makiya da suka kewaye ni, shi ne kuma zai taimake ni rike wannan lardi, da gwamnatin Masar ta sa alhakinsa a hannuna. Tun ina yaro ni zuciyata ba karfi ta yi wajen addini ba. Na dai tabbata, na gaskata ni Kirista ne, kuma addinin Kirista aka koya mini, amma duk wanda ya ce ga hanyar da ta fi masa wajen samun tsira, sai in ce ya yi ta bi, ba na kinsa don wannan. Kuma ni ban zo yin aikin mishan a Sudan ba, aikin gwamnatin Masar na zo yi.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)