Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Muhammed Effendi Farag ya fita ya bar ni cikin kogin tunani. Zuwa can dai na tsayad da shawara, na yi niyyar gobe da safe ba zan tafi gaban sojammu ba sai ina Musulmi. Na tabbata yin haka zai kawo mini kura bisa kaina, har zai sa wadansu su kini a duniya. Amma dai na yi niyya, mai cewa kome ya je ya ce, ban damu ba. Wannan shi ne zai yi maganin makiya da suka kewaye ni, shi ne kuma zai taimake ni rike wannan lardi, da gwamnatin Masar ta sa alhakinsa a hannuna. Tun ina yaro ni zuciyata ba karfi ta yi wajen addini ba. Na dai tabbata, na gaskata ni Kirista ne, kuma addinin Kirista aka koya mini, amma duk wanda ya ce ga hanyar da ta fi masa wajen samun tsira, sai in ce ya yi ta bi, ba na kinsa don wannan. Kuma ni ban zo yin aikin mishan a Sudan ba, aikin gwamnatin Masar na zo yi.
Kashegari da safe sai na ce duk soja su taru. Sai na aika a kira mini Ahmed Beshir, alkalin gari, da kuma babban tajirin garin, Muhammed Ahmed. Da suka zo, na ce su biyo ni, sai filin farati. Na ba soja oda, suka yi famsikwaya. Na hau doki na shiga tsakiyarsu na ce, “Soja, na sani lalle mun yi ta shan wuya da bakar wahala. Kun yi yaki, kun daure, kun nuna jaruntaka. Na tabbata kuwa jaruntakan nan taku ba karewa ta yi ba. Muna yakin nan don shugabammu ne, mai girma sarkin Masar, mai mulki da kasan nan. Na tsotsi zaki tare da ku, na tsotsi daci tare da ku. Duk inda wuya ta ke, nan na kan kutsa kai, ban taba nokewa ba. Ko da ya ke ni ne shugabanku nan, amma da ranku da nawa duka daya ne. To, na ji an ce har yanzu kuna dubana a bako, kuma Kirista. Amma wannan ba haka ba ne. Ba bako ba ne ni, ba kuma Kirista ba ne. Ni Musulmi ne kamarku.” Ina kare wannan magana, sai na yi kalmar shahada. Jin haka fa sojan nan kulliyarsu sai ihu, suna murna. Hafsoshi kuma sai zuwa su ke suna ba ni hannu, suna mubaya’a. Da hargowar ta natsa, na ce da soja a kullum za mu yi salla tare da su. Daga nan na ba da odar furje’am, na sallame su, suka juya suka shiga sansani.
Da na koma gida na kira hafsoshina. A nan suka tabbatar mini da ban-gaskiyarsu, da muka kare ci da sha muka yi sallama. Na sa aka sayo hurtuman shanu ashirin na ce a yanka wa sauran soja. Ran nan suka yini, suka kwana, suna shagali. Wannan dabara babu abin da ya fi ta fita. Nan da nan mutanen nan suka sake ra’ayinsu, kiyayya, da shakka, da zargi, duk suka fita daga zukatansu. Ni kuma hankalina ya kwanta, ko da ya ke abokin gabammu kullum sai kara karfi ya ke yi.
Yanzu mutum daya ne kadai ya sha mini kai, shine Zogal Bey. Ga shi dai babba ne cikin aikin gwamnati, ga shi da arziki, da alheri, kuma ga shi yana bayan Mahadi ne a boye. Kyauta tasa ta sa ko am fadi laifinsa mutane ba su yarda. Sabo da haka na rasa yadda zan yi in raba shi da Mahadi. Ba ni kuma da iko in taba shi, sai in ta da zaune tsaye. Ran nan sai na yi niyyar lalle zan kira shi in nuna masa mun san kunikunin da ya ke yi, kuma im fada masa ya rabu da Mahadi, in ya ki wata rana zai yi kuka.
Na sa aka kira shi, muka kebe mu biyu. Bayan mun gaisa sai na ce da shi, “Zogal, ka ga mu biyu ne a nan, daga ni sai kai, sai ko Mahaliccimmu Ubangiji da ya ke ganimmu. Tun zuwana kasan nan mu ke tare da kai. Ba ni da mutumin da ya fi ka. Mun ci tare, mun sha tare, mun kwana tare, mun yi aiki tare. Na sani ni ke gaba da kai, amma ban taba nuna maka iko ko fifiko ba. Sabo da haka ina so zan tambaye ka abu biyu yanzu, ka ji tsoron Allah ka fada mini gaskiya.” Zogal ya ce, “Babban gwamna, tun da ya ke kana shugabana ne, akwai wani abin da zan boye maka ?" Sai na ce masa, “'Danuwanka Mahadi yanzu ya ci Kordofan, ya ci Lubayya. Jama’a duka sun rufu a bayansa. Wannan sa’a da ya samu har ta sa ka bar bin gwamnati kana binsa a boye. Ka manta da duk alherin da gwamnati ta yi maka ne ? Ka manta da darajar da mai girma sarkin Masar ya ba ka, da karin girma cikin aikinka ? Ka san duk wanda ya sami daraja da girma irin taka, ana tsammaninsa da bauta wa gwamnatinsa tsakani da Allah."
Zan ci gaba sai Zogal ya ce, “Gaskiyarka Saladin, na tabbata Mahadi danuwana ne. Kuma na yarda zumuntan nan da ke tsakanimmu ta karkatad da zuciyata zuwa gare shi. Amma a ko yaushe ina aikina bisa gaskiya, ba kuwa zan saki wannan babbar amana ba." Ni kuma na ci gaba, na ce, “Na sani ka yi aikinka daidai, amma na ji an ce ka hada kai da Mahadi. Me ya sa ka boye mini wannan?“ Zogal ya ce, “Lalle ba zan ce ba mu da labarin juna tsakanina da danuwana ba, amma babu takarda tsakanimmu, sai dai sakon baki kurum na gaisuwa, daga fatake masu zuwa daga Kordofan. Na riga na yi rantsuwa ba zan fadi irin sakon da su ke fada mini ba, kuma ba zan fadi sunayen masu kawo sakon ba. Dalili ke nan da na boye maka wannan magana. Abu guda kurum zan iya fada maka, ko ka yarda ko ka ki, shi ne labarin abin da kasar Kordofan ke ciki kurum suke ba ni. Mahadi bai taba kokarin janye ni zuwa gare shi ba.”
Jin haka sai na yi farat na katse hanzarinsa na ce, “Tsaya, Zogal! Ba na so ka buda mini irin asirin da ke tsakaninku da danuwanka. Amma ka sami labarin irin gawurtaccen shirin da gwamnati ke yi don kwato Kordofan ?" Ya ce, “Na ji.” Na ce, “Lalle za a kwato kasar daga hannun Mahadi, kuma kai ga amana zam ba ka, ko kana iya dauka ?", Ya ce, “Ba sai na ji irinta ba ?“ Na ce, “Kai Zogal, na gan ka mutum ne mai hattara da hikima. Kuma ka sani ina da ikon da zan yi kaca kaca da kai. Amma na ga wannan hanya ba za ta yi wani amfani ba. Ba na so in wulakanta mutum irinka, wanda ya yi shekaru yana bauta wa gwamnatin kasarsu da gaskiya. Yanzu abin da zan yi, shi ne zan sallame ka daga aikin yaki, amma ina so ka tafi Kordofan ka gano mini halin da Mahadi ke ciki. Na sani tawaye in na addini ne, jan mutane ke gare shi da farko, sai dai im mai hankali ya yi tunani ba ya tura kansa ciki. Yanzu zam ba ka takarda wadda ni ke so ka san yadda ka yi ta sadu da gwamnati a Kahartum cikin sirri, ba tare da sanin kowa ba. Da ya ke gwamnati ba za ta aika da rundunarta Kordofan ba, sai watan gobe, ina so ka yi kokari ka hana Mahadi aikawa da soja Durfur, ka kuma hana shi aikawa ana shela ana sa mutane su yi tawaye. In gwanmati ta yi nasara za ka ji dadi. In kuma Mahadi ne ya ci nasara, wannan sanin abin da zai faru sai Ubangiji. Amma don in gaskata biyayyarka, zan rike iyalinka duka a nan, in ka je ka yi magudi kanka ka cuta. Za su zauna cikin jin dadi, ba yunwa ba kishirwa har ka dawo.”
Zogal ya ce, “Na ji, na karba, ko da ya ke ba da son raina ba. Amma tun da ya ke yin wannan shi ne zai tabbatad da amanata ga gwamnati, na yarda zan tafi.”
Sai na aika aka kira mini Farag Effendi, da Wad Asi, da alkali, na fada musu yadda muka yi da Zogal. Suka ce har yanzu ba su gaskata shi ba sai ya rantse tukuna. Aka kawo Alkur’an ya je ya yi alwala, ya rantse. Bayan kwana uku shiri ya gamu, na ba shi ’yan rakiya ya tashi, ni kuma na koma Dara.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada