TUN KAFIN AURE💐1
Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka'a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya...daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta....wane dan kut....maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni...wunin uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da hawaye.
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon bango. Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu je kayi wanka kawai tace masa. Ba musu ya hau sama tana bayansa yana tangadi amma yana iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi bai zamu musu komai ba sai silar watsewar tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata. Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa da gwiwa... Alhaji kenan ta fada tana shimfida abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani. Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka. Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa 'yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina dake sokonci kin manta mun taba hirar dake lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa. Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo. Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu adaidaita sahu suka tafi gida.
Batul Mamman💖