ABDULKADIR SALADIN 16

16. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Da na gama karantawa, Halifa ya ce, “Me aka ce ?" Ni kuwa sai na ce, “Wannan takarda Gordon ne ya rubuta ta da hannunsa, amma da faransanci ya rubuta, ni kuwa ba na jin faransanci. Nan da nan fa hankalin Halifa ya tashi, ya ce, “Me ka ce ? Ban gane nufinka ba." Na ce, “Abin da na ke nufi, shi ne akwai kalmomin da ban gane nufinsu ba, don kamar zaurance su ke, wanda a kan yi sabo da rufe asirin yaki. Im ba mutumin da ya koye su ba, gane su ba shi yiwuwa." Halifa ya ce, “Ashe ba a ambaci sunayen mutane a ciki ba, da kuma yawan soja ?" Na ce, “Duk wanda ya ce an ambaci suna da yawan soja, bai yi karya ba, amma wannan kurum ai bai cikasa ma'anar takardar ba. Amma kila wanda ya fada maka sunayen nan zai iya gaya maka sauran abin da ke rubuce.” Kila Halifa ya gane da gangan na ki fada masa, shi ya sa ya yi fushi, ohol Ni dai ban ankara ba sai naga ya fizge takardar daga hannuna.
Ganin wannan fushi da ya yi, na kuma san lalle karshen fushin ba alheri, sai nan da nan na shiga ba shi magana. Na ce, “Sai ka yafe ni, ya Halifa. In da ina iya karantawa, ai da babu abin da zai fi mini dadi da haka. To, iyawa ne ban yi ba, amma kila magatakardunka za su fi ni fahimtar rubutun zaurance.” Halifa ya ce, “Ko ka san abin da takarda ta ce, ko ba ka sani ba, duka uwasu daya. Gordon dai faduwa zai yi, Kahartum kuwa za ta shiga hannummu dole.” Sai ya mike ya yi waje, suka bar ni ni kadai cikin duhu.
A cikin Kahartum, Gordon yana ta rarrashin Turawan da ke garin da ’yan ciniki, bisa su fita su nemi hanyar tsira. Ko ina sai kukan yunwa su ke yi. A kullum ko wane Bature, mai gida, za a ba shi biskit dari shi da iyalinsa, amma duk wannan bai isa ba. Kullum idon Gordon na kan Kogin Nil ko ya hangi jirgi mai zuwa da sojan Ingilishi, da aka yi masa alkawari daga Masar, amma a banza. Ko labarinsu babu, ga ko Mahadi da mutum dubu bisa dubu a kofar gari, ga barikin Omdurman an ci shi, an kwashe duk makaman da ke ciki. Ga shi ba shi da mataimaka wadanda za su tsare garin, balle ma su kori rundunar Mahadi! Haka aka zauna kwanaki, ba a fada wa Kahartum ba, ba a kuwa koma baya ba. ’Yan sojan da ke hannun Gordon suka yi iyakar kokarinsu, suka tsare duk mashiga. Amma fa duk wannan kafin ranar motsawar Mahadi ta zo ne. Ana nan ranar ta zo. Ranar masifa, ranar shan wuya, ranar da ba zan mance da ita ba har in koma kushewa!
Ran Lahadi, 25 ga Janairu, 1885, watau kwana goma da faduwar Omdurman, ran nan Mahadi da Halifa suka shiga jirgin ruwa, suka bi tsawon Nil zuwa inda ’yan yakinsa na gabas da gari ke tare. Kowa ya sani gobe tun da asalatu za a fada wa Kahartum. Shi ya sa Mahadi ya je don ya kara wa mutanensa karfi a zuciya. Ya yi musu wa’azi, ya ce su daura niyyar shahada, ya yi wa wadanda za su fadi a fagen fama alkawari da gidan aljanna, wadanda suka rayu kuwa da lada kamar yashin Nil.
Duk abin nan Gordon bai sani ba. Ni kuwa a wannan dare ba na iya kwatanta irin halin da zuciyata ke ciki. Yadda na ga rana, haka na ga daren nan, na kasa barci har aka kira asuba. Barci ya fara surata ke nan, sai karar igwa ta farkad da ni. Na ce lalle abin da a ke gudun ya zo ke nan. Bayan jimawa kadan ban sake ji ba, sai ’yan bindigogi ke fafarniya kurum. Na yi ta waswasi a zuciya, na ce yanzu iyakar kokarin sojan Kahartum ke nan ? Bindigogi su yi ’yar hargowa ta minti kadan, sai kuma a ji shiru ?
Jim kadan sai ga masu gadina sun komo a guje suna haki. Na ce, “Me ya faru ?” Suka ce, “Ai Kahartum tana hannun Mahadi.” Na kada kai, na yi mamaki. Zuwa can sai na ji hargowar mutane wajen tantin Halifa da na Mahadi. Na ga an yi cincirindo a wurin, mutane sai tsalle su ke, suna kada bindiga, da masu, da takubba a kansu, suna ihun murna. Sai na yi rarrafe, na fito daga tantina don in leka, in ga ko mene ne. Kafin in kai wurin sai ga mutum uku sun keto taron nan sun nufo tantina, duk ido kuma ya biyo su. Da suka zo kuwa, sai na ga ashe sojan Mahadi ne, Bakar Fata, su uku. Daga cikinsu wani wai shi Shatta yana dauke da wani abu cikin wani kyalle. Suka iso suka tsaya a gabana tsiwa-tsiwa. Shatta ya kwance kunshin ya ce mini, “Kai Abdulkadir, dubi nan.” Ko da na duba, sai ga kan Janar Gordon!
Nan da nan idona ya rufe, ina ganin sama da kasa kamar sun gamu. Ga jini na zirara daga cikin kan. Idon nan nasa ga su sun kusa rufewa kamar wanda barci ya kusa daukarsa. Ga bakin nan a rufe, gashin kansa da dan sajensa duk sun rikide sun zama fari. Ni dai sai kallo na ke kurum, ban iya ce kome ba. Na ga aikin rashin imani.
Cikin haka Shatta ya kara fama zuciyata ya ce, “Wannan ba kan kawunka ne, kafirin nan ba ?” Na ce, “To, in kansa ne fa ? Me ke nan kuka yi? Ai ya nuna jaruntakarsa tun da ya fadi a fagen fama. Shi ya ji dadi da ya mutu ya huta da zilla.”
Shatta ya yi dariya, hahaha, ya ce, “Watau har yabon kafiri ka ke yi ? Sai ka yi da-na-sani.” Suka juya suka tafi. Ni kuma na koma cikin tantina. Ina tunani ina cewa a zuciyata, “Kahartum ta fadi? Gordon ya mutu ?” Na ji dai kamar mafarki na ke yi.
YADDA GORDON YA MUTU
Da dare, ana gobe wannan bakar kaddara za ta faru, Gordon ya sa aka yi shela a Kahartum aka fada wa mutane su kwana bisa kan shiri. Don ya kara musu karfi, ya sa aka yi ta wasan wuta, ana harba albarushin takarda mai launi iri iri. Aka kare, ’yan badujala suka yi ta kida suna busa. Zuwa can su ma suka yi shiru, gari ya yi tsit, kowa ya shiga daki ya kwanta. Can sai Mahadawa suka yunkuro yuu kamar fara. Sun san duk inda soja su ke, sun kuma san wuri mai karfi, da mara karfi. Sai rabinsu suka zaga suka hudo wa garin ta fuskar Farin Nil, don a nan wajen ganuwa ta fi rushewa. Rabi kuwa suka tari sojan gwamnati gadan gadan. Da soja masu tsare da Farin Nil suka yi dan fufuf fufuf da bindiga, suka ga abin ya fi kariinsu, sai suka tsere.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)